Alternative Espaces Citoyens Niger

Articles les plus récents


Articles les plus récents


Talaka kai ma da laifinka!!!

jeudi 9 mars 2006 par Arimi Abba
Yan iya magana na cewa “waiwaye adon tafiya“ yau idan muka waiwaya muka dubi irin kazamin halin da kasar Nijar ta tsinci kanta a ciki, na kangin talauci, jahilci, cin hanci da rashawa, handamar dukiyar kasa, tare da rashin hukumta masu laifuffuka, da dai sauran makamantan haka. Tsakanin gwamnati da talakawa, waye ya cancanci a dorawa alhakin faruwar hakan ga kasar ta Nijar.? > suite


“Karen da ya sha kwai a kansa takan kare”

jeudi 9 mars 2006 par Arimi Abba
Yau ako ina cikin duniya, in ana maganar kasashe da gwamnatocin da su ka yi kaurin suna wajen cin hanci da karbar rashawa tare da rashin nuna adalci a shara’a kasashensu, to kasar Nijar na daga cikin jerin su, sabanin lokutan baya da kasar ta zama yardadda kamila mai kula da hakkokin talakawanta daidai gwargwado, sai gashi yau ta zama abin gudu da kyama a tsakankanin kawayenta, saboda cin hanci da rashawa tare da nuna rashin adalci da su ka yi kakagida a cikinta. > suite


A

vendredi 23 décembre 2005
Abdiquer : Kasawa : Yin murabus, fasawa, zarumi ya kasa gaban abokin hamayyarshi Abnégation : Bada kai : Kuzari. Shugaban jamhuriya yana gayyatar yan kasa da su bada kansu ga ayyukan ginin kasa. Faire preuve d’abnégation : nuna kuzari : bada kai cikin tafiyar da wasu ayyuka, bada (...) > suite


Al’ummar Yamai ku da wadataccen ruwan sha, watakila sai badi warhaka

vendredi 23 décembre 2005
Ruwa su ne rayuwa ! Alhaji Baba Ba’abba, magatakardan gwamnatin jahar Yobe a tarrayar Najeriya, kuma tsohon magatakarda mai zartarwa na hukumar ABN da ke kulla da raya kogin Nijar, ya jadadda cewa, dan adam na iya rayuwa har tsawon kwana 40 ba tare da ya ci kallaci ba, amma ba zai iya rayuwa kwana 40 ba tare da ya sha ruwa ba, wannan magana nuna mana muhimmancin ruwa ga rayuwar dan adam a duniya. > suite


Rashin hadin kan kungiyoyin kwadago abin farin ciki ne ga gwamnati !

vendredi 23 décembre 2005
Daya ga watan mayu 1886, 1 ga watan mayu 2005 shekaru 119 kenan cur da aka yi wa ma’aikatan kwadago dake zanga zangar neman hakkin su kisan gilla a birnin Chikago na kasar Amuruka. Kamar sauran ma’aikatan kwadago na kasashen duniya nan ma a kasar Nijar ma’aikatan sun gudanar shagulgullan tunawa da wanan bakar rana ta alhini da takaici. > suite


Kiran kungiyoyin farar

Kira, daga kungiyoyin kwadago, da masu zaman kansu, da na Mata da Matasa, tare da na mazauna karkar da su ka halarci babban zaman taron al’ummar Nijar

vendredi 23 décembre 2005
Kamar sauran kasashen Afrika, kasar Nijar ta rungumi tsarin mulkin Democradiya tare da samar da jam’iyun siyasa barkatai ne, a 1991, a lokacin da ta gudanar da babban zaman taron kasa mai cikakken iko.Wannan cigaba da aka samu ya haifar da kafa jam’iyun siyasa da dama tare da shirya babbab zabe, da kuma samar da kundin tsarin mulki da ya tabbatar da yancin dan adam da na Democradiya, kana an samu kafuwar kungiyoyin fararen hula da dama, tare da sakin mara ga kafofin yada labarai.Duk kuwa wannan muhimmin cigaba da aka samu ta fuskar siyasa, ya faru ne sanadiyar sadaukar da kan da al’ummar Nijar maza da mata su ka yi ne, tare da kaucewa dak wani yanayi da zai sa a koma gidan jiya ,ma’ana inda aka fito. > suite


Tsadar Haya a birnin Yamai

vendredi 23 décembre 2005
Tsadar hayar gidaje a birnin Yamai da kuma sauran manyan birane na kasar Nijar, ta zama daya daga cikin abubuwan da ke ci wa ma’aikatan bariki da sauran jama’a musamman masu dan karamin karfi tuwo a kwarya,inda a cikin yan shekarun baya-bayan nan matsalar ke cigaba da yin kamari. > suite


Malamai magoya bayan kungiyar SNEN a Damagaram, sun gudanar da azumi da adu’o’i domin neman sakayyar Ubangiji akan gwamnati

vendredi 23 décembre 2005
Bayan sun sha yin yajin aiki sau da dama kamar yadda uwar kungiyar su ta bukace su, domin ganin cewa gwamnati ta shafe masu hawaye, a halin yanzu malaman makaranta magoya bayan kungiyar SNEN a birnin Damagaram sun canza salon gwagwarmaya domin kwato hakkokin su da suka ce gwamnati tayi rib da ciki akan su yau shekaru da dama kenan. A ranar Alhamis da ta gabata, daruruwan malamai ne magoya bayan kungiyar ta SNEN suka fito akn titunan birnin na Damagaram inda suka yi wata zanga-zangar lumana, domin ko wata kila hukumomi za su saurare su a wannan karo har ma su shafe masu da hawayen na su. > suite


Ana wata ga wata, bayan karin kudin harajin TVA, shi ma kampanin SEEN yayi kari ga kudin ruwan sha

vendredi 23 décembre 2005
Kaungiyoyin kare hakkin dan Adam da kuma na ma’aikatan kwadago a kasar Nijar, sun kudiri aniyar cigaba da gwagwarmaya har sai lokacin da shugaban kasar Tanja Mamadu, ya soke dokar nan mai kara kudin haraji akan kayayakin abunci, ruwan sha da kuma makamashin lantarki . > suite


Bakin tika tika bakin tik !!!

vendredi 23 décembre 2005
Daga Karshe dai an cimma daidaito tsakanin gwamnati da kungiyar nan mai fafukar yaki da tsadar rayuwa a kasar Nijar. > suite

Accueil du site | Contact | Plan du site | Espace privé | Statistiques | visites : 45639

Suivre la vie du site ha    ?

Site réalisé avec SPIP 1.9.2c + ALTERNATIVES

Creative Commons License