Alternative Espaces Citoyens Niger

Articles les plus récents


Articles les plus récents


Shin wai Nijar ce tafi duk sauran kasashen duniya tsadar Man Petur ?

vendredi 23 décembre 2005
A ranar Lahadi 1 ga watan mayu ne al’ummar Nijar suka wayi gari da karin farashin kudin man petur da ba a taba ganin irinsa ba a tarihin kasar, wanda yasa lita daya na man ya kai dala 106 sabanin dala 98 da yake tunda farko, al’amarin da ke nuna karin ya kai na dala 8. Wannan tashin gwabran zabo da farashin man ya yi, ya kara jefa al’umma cikin maywuyacin halin matsi da wahalar da suke fuskanta tunda farko. > suite


A garin bakin tone-tonen sa zakara ya tono wukar yankansa, domin kuwa dan Nijar ya zabo yan majalisar dokoki daidai da shi !!!

vendredi 23 décembre 2005
A daidai lokacin da al’ummar Nijar ke fama da kangin talauci, fatara, kai har ma da karamcin abinci sai gashi kwatsam sabuwar majalisar dakoki kasar ta amince da wadansu sababbin hanyoyin karbar haraji ga talakawa kota halin kaka wanda gwamnati ta gabatar mata. > suite


Kimanin kudi SEFA miliyon dubu har sau dubu ne ake biyar kasar Nijar bashi

vendredi 23 décembre 2005
Kungiyar nan mai yaki da karbar bashi da ruwa anan Nijar wato RNDD a takaice, tana shirye-shiryen gudanar da wani rangadi a sassa da dama na kasar nan domin fadakarda jama’a manufofin wannan kungiya da kuma ayukan da ta gudanar daga lokacin da aka kafa ta yau fiye da shekaru biyu da suka wuce kawo yanzu. Shugaban kungiyar ne Malam Ibrahim Yakuba ya bayyana haka lokacin da yake hira da jaridar Ra’yi anan birnin Yamai, inda yace tuni kungiyar tasu ta tsara jerin sunayen garuruwa da kuma wuraren da suke da mahimmanci ta fannin tattalin arziki ga kasar nan, wadanda ya ce tawagar ta su zata ziyarta a matsayin mataki na farko domin kara matso da jama’a zuwa ga fahimtar ayukan da wannan kungiyar ta ke yi. > suite


Shekaru uku kenan da ake fama da karamcin ruwan sha a birnin Maradi

vendredi 23 décembre 2005
Shekaru uku zuwa hudu kenan da al’umma mazauna birnin Maradi ke fama da wata mummunar matsala ta karamcin ruwan sha, matsalar da a kowace rana sai kara munana take ba tare da daukar wani mataki ba na shayo kanta a cikin gaggawa, kamar yadda jama’a ke fatan ganin hakan ta wakkana a matsayin wani yunkuri na samarwa talakawa rayuwa ingantacciya. > suite


Gwamnati ta ci ribar milyon 100 da wasu yakai a game da sabon harajin TVA da ya fara aiki

vendredi 23 décembre 2005
A ranar Juma’a 6 ga watan Mayu, majalisar dokokin kasar Nijar ta jefa kura’ar amincewa da sabuwar ayar dokar nan, mai kwaskwarima kan karin harajin TVA ga wasu kayayyakin masarufi dangin rayuwar al’umma. Majalisar dokokin ta amince da sabuwar ayar doka ne, kamar yadda aka (...) > suite


Hira da sakataren hulda da jama’a na hadadiyar kungiyar ma’aikata ta CDTN game da zagayowar ranar ma’aikata ta duniya.

vendredi 23 décembre 2005
Kamar dai sauran kungiyoyin ma’aikata na kasashen duniya, hadaddiyar kungiyar ma’aikatan kwadago ta kasar Nijar mai suna CDTN ta yi amfani da ranar daya ga watan Mayu domin gudanarda shaglgula da dama na murnar zagayowar wannan rana mai matukar muhimmanci ga ma’aikata. Bisa ga al’ada kuwa, kowace kungiya ta kan yi amfani da wannan ranar domin isarwa hukumomi da kuma masu kamfanonin da suke wa aiki jeri koke-kokensu, domin sanin irin matsalolin da suka fi damuwar ma’aikata a wannan kasa ta Nijar, jaridar Ra’ayi ta tattauna da sakataren hulda da jama’a na kungiyar ta CDTN wato Malam Ibro Ayuba, inda kuma ya soma da karba mana kamar haka. > suite


Karin harajin TVA ya haifar da rikici tsakanin masu gidajen bredi da dillalansa a birnin yamai

vendredi 23 décembre 2005
A ranar assabar 26 ga watan fabrairun da ya gabata ne, jami’an yan sanda suka yi awon gaba da mutane 18 mambobin kungiyar masu saida shayi da bredi ta kasa da ke cigaba da yajin aiki karo na 2 na tsawon kwanaki 3 a jere, bayanda yan sandan suka ce an samesu da laifin cin zarafin wasu (...) > suite


Yaki da tsadar rayuwa

Idan rana ta fito tafin hannu ba ya iya kareta

vendredi 23 décembre 2005
Sama da mutane dubu hamsin ne suka halarci taron gangamin da kungiyoyin nan masu yaki da tsadar rayuwa a kasar Nijar suka shirya, a ranar Talata 15 ga watan Maris 2005 a harabar majalisar dokoki da ke birnin Yamai, Mahalarta taron suka yi tir da Allah waddai da manufofin shugaban kasa Tanja (...) > suite


Ko Karin harajin kudin TVA zai iya haddasa karuwar marayu a kasar Nijar ?

vendredi 23 décembre 2005
A ranar alhamis10 ga watan Fabrairu ne hadin guiwar kungiyoyin farar hula da ke kokowa da duk wata siga da ke haddasa tsadar rayuwa ga al’umma a kasar Nijar, suka gudanar da wani zaman taron mahawara a gidan matasa da al’adu na Gyado Sekou dake nan birnin Yamai. Mahalarta taron (...) > suite


Dan Ibro a birnin Yamai

vendredi 23 décembre 2005
Ni suna na Rabilu Musa Dan Lasan, wanda aka fi sani da Dan Ibro .An haife ni ne a garin Dan Lasan na karamar hukumar mulkin Warawa dake jahar Kano tarayyar Najeriya, shekaru na ba su wuce 31 ba, a yanzu ina zaune a garin Wudil dake cikin jahar Kano, ina da mata guda biyu da yaya na 8. > suite

Accueil du site | Contact | Plan du site | Espace privé | Statistiques | visites : 45639

Suivre la vie du site ha    ?

Site réalisé avec SPIP 1.9.2c + ALTERNATIVES

Creative Commons License