Alternative Espaces Citoyens Niger

Articles les plus récents


Articles les plus récents


Harshe da al’adu...

HARSHE DA AL’ADU...
jeudi 22 décembre 2005
Ko wa ya bar gida, gida ya barshi. Shi ne yanayin da mu ka tsinci kan mu ciki a halin yanzu. A yau kasar Nijar na da shekaru 45 da samun yancin kai daga turawan mulkin mallakar kasar Faransa. Shekaru 45 ba kwana 45 ba ne,amma kusan gidan jiya noman Goje. kasar Nijar dai kasa ce mai kumshi da (...) > suite


Muhimmin Jawabin da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana game da Hakkokin Yan-adam a shekarar 1948

jeudi 22 décembre 2005
Gabatarwa Ganin cewa yanci da adalci da zaman lafiya ba za su girku a duniya ba, sai in an amince da cewa: dukkan yan-adam suna da mutunci, kuma suna da hakkoki na kowa daidai da na kowa, wadanda ba za a iya kwace musu ba, Ganin cewa ba abin da ya sa aka aikata abubuwa irin na lokacin (...) > suite


A garin Inates na jahar Tillaberi, an rufe kare da sanho

jeudi 22 décembre 2005
Bauta wata kalma ce da bahaushe ke amfani da ita domin bayyana rayuwar wani mutun ko mutanen da suka kasance ba tare da sun mallaki ikon kansu ba. Tarihi ya nuna cewa bautarda jama’a abu ne wanda ya samu tushe tun shekaru aru-aru a cikin kasashen duniya da dama, wadanda suka hada har da kasar Nijar. > suite


Matsalar ruwa

"Rabon mu da ganin ruwan pompo tun a sallar layyar da ta gabata"

mercredi 21 décembre 2005
Matsalar nan ta karancin ruwan sha da al’ummar Damagaram ke fama da ita yau shekaru aru-aru sai cigaba da kamari ta ke. Zancen da ake yanzu haka, mazauna wannan birni na shan bakar wahala kafin su kai ga samun ruwan sha ba wai na wanka ko wanki ba. Wannan matsala dai ta mamaye illahirin birnin, domin kuwa ba wata unguwa da abin bai shafa ba. > suite


Rabon unguwanni tsakanin sabbin kananen hukumomi na birnin Damagaram

An yanka ta tashi, rabon unguwanni tsakanin sabbin kananen hukumomi na birnin Damagaram

mercredi 21 décembre 2005
Har yanzu da dama daga cikin mazauna birnin Damagaram basu tantance ko a karkashin wace karamar hukuma suke ba daga cikin kananen hukumomi guda biyar da ake da su a wannan birnin, wanda aka karkasa shi karkashin sabon tsarin fasalta yankuna na kasar Nijar. Sakamakon rashin sanarda al’ummun wandansu unguwanni ko a karkashin wace da’ira suke cikin wadannan da’irori guda biyar, yasa aka kusa baiwa hamatta iska tsakanin magajin gari da’ira ta daya da kuma takwaran sa na da’ira ta biyu, lokacin wani zaman taro da aka shirya domin warware wannan matsala da aka jima ana neman shayo kanta. > suite


Zaben mashawarta a Garin Damagaram

mercredi 21 décembre 2005
A ranar 24 ga watan Janairun da ya gabata ne, aka gudanar da zaben shugaba da mataimaka na majalisar zartarwa ta mashawartan birnin Damagaram na jahar Zander.Shi dai wannan zabe wanda ya gudana karkashin jagoranci gwamnan jahar Abba Malam Bukar. Yan takara uku ne suka nemi shugabancin majalisar, wato Laminu Suleman, Abubakar Egin da kuma Malam Abdu Bukari, duk- kannin su daga jam’iyar CDS-RAHMA. > suite


Ba girin-girin ba dai tayi mai inji kura da ta yi tsintuwar ganga...

Ba girin-girin ba dai tayi mai inji kura da ta yi tsintuwar ganga...

mercredi 21 décembre 2005
Shugaban kasar Nijar Tanja Mamadu ya bayyanawa ilahirin yan jarida da kuma sauran ma’aikatan kafofin watsa labarai na kasar cewa, a shirye yake domin taimaka masu su gudanar da ayukansu cikin tsanaki da kuma samarmasu da hanyoyin inganta ayukan nasu . > suite


Kananan hukumomi

A daidai lokacin da al’umma ke jiran gashin da suke ya gasu suci, a wannan lokaci ne wasu ke kokarin kashe wutar

mercredi 21 décembre 2005
Anya tsarin karkasa yankunan kasa da Nijar ta rungma na iya warware matsalolin da kasar ke fuskanta a halin yanzu kuwa ? ganin har yanzu talakawan kasar basu gani a kasa ba, duk da cewa shirin na nufin baiwa talakawa yancin tafiyar da lamurransu da kansu. Wannan ya sa jaridar Ra’ayi yin hira da wani dan kasa har ila yau dan siyasa, shugaban jam’iyar ORDN TARMAMUWA Maman Sani Adamu, domin jin ainahin abinda yasa gwamnatin Nijar rungumar wannan tsari ? > suite


Ra’ayin addinin

Shuwagabannin addinin suna bada bayaninsu

mercredi 21 décembre 2005
Da wasa ko da gaske, ana daukar musulumci tamkar addini ne da ke tauye mata, ya kuma hana su je gaban jama’a. Don tantance gaskiyar zargin da kuma kawo haske game da matsayin mata a addini, mun tattauna da wasu shugabanin kungiyoyin addinin musulumci na kasa. A ganinsu addinin Muhammadu (...) > suite


Ra’ayin Hukuma

«Dan kasa zai kasancewa a tsakiyar rayuwar kananen hukumomi»

mercredi 21 décembre 2005
Sannu ba ta hana zuwa, kasar Nijar ta kusanto karshen tsarin sassauta iko da tsarin zaben kananan hukumomi ranar 29 ga watan mayu 2004. Zancen jefa kuri’a yana ga karfafa dangance da tsarin kalkasa hukumomi da aka yi. Bugu da kari ana jaddada bukatar shigar mata a cikin harakokin cigaban (...) > suite

Accueil du site | Contact | Plan du site | Espace privé | Statistiques | visites : 45639

Suivre la vie du site ha    ?

Site réalisé avec SPIP 1.9.2c + ALTERNATIVES

Creative Commons License