Alternative Espaces Citoyens Niger

Articles les plus récents


Articles les plus récents


Ra’ayoyin jam’iyyun siyasa

mercredi 21 décembre 2005
Isufu Tambura Mataimakin magatakarda mai kula da sadarwa na MNSD - Nassara Mata da matasa su ne ginshikin jam’iyyar siyasarmu. Tun kafa wannan jam’iyya mata ba a barsu baya ba. A cikin kungiyoyin jam’iyyar nan akwai sashi da ake kira tsari na mata Nasara "Amazones" da (...) > suite


Matsaloli da amfanin

mercredi 21 décembre 2005
Shekaru biyar (5) bayan da aka yi watsi da zabubbukan kananen hukumomi na shekarar 1999, tabbatar da sassauta iko ya zama sabon abu a mahawarorin kasar Nijar. Bayan tattaunawa da jayayya da dama, yan siyasa sun tsaida yin zaben kananan hukumomi a watan mayu 2004. Yan watanni gabanin zaben, ya cancanta yawancin yan kasa su samu cikakken fahintar ainahin mahimmancin wannan tsari da ya danganta da kuzarin al’umma wanda amfani ne na kansu da kansu. > suite


Raya karkara a Jahar Maradi

mercredi 21 décembre 2005
Yankuna da dama ne a nan kasar Nijar ke cin moriyar ayukan raya kasa da kuma cigaban jama’a wadanda kungiyoyin bayarda agaji na kasa da kasa da kuma projet ke gudanarwa kowace shekara ta Allah.Mafi yawa daga cikin irin ayukan da wadannan kungiyoyi ke gudanarwa, mazauna yankunan karkara ne suka fi amfana dasu, ayukan da suka hada da bunkasa ilimi, samarda ruwan sha da kuma bunkasa ayukan noma . > suite


Takardar aihuwar kungiyar

mercredi 21 décembre 2005
kungiyoyin gari da makamantansu, masu tahiyar da ayukka a cikin sassa da dama na bunkasa, ko da yake an san da zamansu, mahi yawancinsu ba su da takardar aihuwa kan gaskiya. Gwamnati na yarda da su a sabilin yarjejeniyar hulda da ke akwai tare da masu hannu da shuni. -ar sa in sa da ke hada su da gwamnati ba ta huce kara takarya ba. Kuma tana da alaka da tattalin daji, kamar a misali kasuwar itace. > suite


Zabe daban-daban

mardi 20 décembre 2005
Bayan an san aikin da ya rataya ga kungiyar da za a sabuntawa, ire-iren mambobi da nauyin da ya rataya ga kowane makami, wannan shafi zai yi zance bisa duk yadda ya kamata a yi zabe don ba mahalarta damar daukar wanda ya kamata kuma a makamin da ya dace da shi cikin haske da yarda. > suite


Sanin kungiyoyi

mardi 20 décembre 2005
Sanin Kowa ne, lokacin zabe, abu lokaci ne mai mahimmanci ga duk kungiyoyi. A wannan damar ce yan kungiya ke zaben cikin walwala wakillansu da yan kungiya ke zaben wakillansu cikin walwala wadan da za su gudanar da ayukkan kungiyar. > suite


Hira da Rayyanatu Lutu

mardi 20 décembre 2005
Rayyanatu Lutu : Ni dai suna na Rayyanatu Lutu , na yi karatuna ne ta fannin zana taswirar gidaje a wata makaranta ta koyon gine-gine dake birnin Lome na kasar Togo, bayan na kare na dawo gida Nijar inda na buda ma’aikata mai kula da zana taswirar gine-gine. Ra’ayi : Mine ne ya (...) > suite


"Groupement Naney"

kungiya daya mai gwagwarmayar kare yancin mata a kasar Nijar

mardi 20 décembre 2005
Ranar 13 ga watan Mayu rana ce mai matukar muhimmanci ga matan kasar Nijar, domin kuwa ita ce ranar da aka kebe masu domin murna da kuma nuna irin bajintar da suke da ita ta fannin gina kasa da kuma kyautata rayuwar al’umma. Ita dai wannan rana ta samo tushe ne tun cikin shekarar 1991 lokacin da matan Nijar suka shirya wata zanga-zangar limana domin neman gwamnati ta kyautata rayuwarsu da kuma basu damar taka rawa a cikin sha’anin hukuma kamar dai sauran yan uwansu maza. Daga wannan lokaci kawo yanzu, kungiyoyin mata da dama ne aka kafa a kasar , wadanda kuma suke gwagwarmyar kare hakkoki da kuma taimakawa matan . > suite


Sassauta iko :

buda ma mata wasu hanyoyi

mardi 20 décembre 2005
Da yake lokacin zaben kananan hukumomi yana kusantowa, la’akari da rashin kulawa da mata ya fara yaduwa da bayana ga kawunan yan kasa. Bayannai da dama sai hitowa suke da cewa masu daukan matakkai su kula da taimaka ma mata a harakokin siyasar karkara. Saboda haka wannan kungiya mai suna demokarasi 2000 ta tattauna da Malama Fumakwai Nana Aishatu tsohuwar minista. > suite


Bukin zagayowar ranar mata ta duniya a kasar Nijar

mardi 20 décembre 2005
Kamar dai ranar takwas ga watan Maris na kowace skekara, ko a bana mata a sassa daban daban na duniya sun gudanar da shagulgula a ranar ta takwas ga watan na Maris domin murnar zagayowar wannan rana da majalisar dinkin duniya ta kebe masu. A shekarar bana dai kamar sauran shekaru, kungiyoyin mata a kasashen duniya daban daban sun yi amfani da wannan rana, domin yin bitar irin matsaloli ko kuma cigaban da suka sama a cikin rayuwar su. > suite

Accueil du site | Contact | Plan du site | Espace privé | Statistiques | visites : 45639

Suivre la vie du site ha    ?

Site réalisé avec SPIP 1.9.2c + ALTERNATIVES

Creative Commons License