Alternative Espaces Citoyens Niger

YAKI DA TSADAR RAYUWA : INA AKA KWANA ?

mardi 18 avril 2006 par Mamane Sani Adamou

Ranar 15 ga watan Maris na 2005 ta kasance mai matukar mahimmanci cikin tarihin gwagwarmayar kungiyoyin farar fula na jamhuriyar Nijar. Hakika, tun zanga-zangar da ta biyo kisan gillar dalibai na jami’ar Yamai a shekarar 1990, ba a taba samun yunkurin al’umma da ya yi tasiri da karbuwa ga ma’abuta ci-gaba da masu begen dimokaradiyya ba. Sai dai abin mamaki shi ne bayan shekara guda da kammala gwagwarmaya, kwalliya bata biya kudin sabulu ba. Ma’ana ganin yanda rayuwar al’ummar Nijar ke ci-gaba da dagulewa yayin da magabata ke cin karensu ba babbaka suna awon gaba da dukiyar kasa. Ayar tambaya a nan shi ne :Menene ya haddasa wannan rashin nasarar ? Akwai mafita kuwa?

Yanayin musamman

Yana da mahimmanci a bicinki halin da yan Nijar suke ciki domin fahimtar makasudin zanga-zangogin da suka wakana. Shekarar da ta gabata, idan ana tune, Nijar ta yi kaurin suna a fannoni da dama na rayuwa. A fuskar tattalin arziki furucin habakar dukiyar kasa da gwamnati ke yi bai tabbata gaskiya ba. Sheharu biyar na ayyana shirin tada komadar tattalin arziki (PAS) ko mu ce shirin <> sun ragargaza ginshikkan cimin kasa. Duk da gudunmawar magodan kudi daga kasashe masu hannu da shuni, gwamnatin Tanja Mamadou ba ta taka rawar gani ba. Akasin haka kididdigar da hukumar tarayyar turai ta zartar ta bayana cewa mahukuntan Nijar sun kashe kudin tarayyar Turai ba bisa ka’ida ba. Kazalika larwai da tawagar hukumar bada lamani da bankin duniya suka gudanar ya gano cewar gwamnati na tabargaza ainun da dukiyar kasa. Musamman kudin da suka shigo baitulmalin kasa a matsayin raguwar bashin da ake bin kasashe masu nauyin bashi ba a fasalta amfani da su ba. Saboda haka babu zancensu cikin kasafin kudi. Wannan lamari ba baki ne kawai suka yi la’akari da shi ba. A’a. Jaridu masu zaman kansu sun sha kalubalantar almubazzaranci, cin rashawa da rashin iya tanadin dukiyar kasa da magabata ke aikatawa.

Babu mamakin ganin yadda halin rayuwar al’umma yake ci-baya. Tsarin koyarwa sai tabarbarewa ya ke cikin makarantun boko inda dalibai kan yi zaman kashe wando na shekara da shekaru basu wadatu da karatu da rubutu ba sakamakon rashin tallafi daga gwamnati. Kazalika shiga asibitoci ya zama sai mai hali. Rahoton shekara shekara na hukumar majalisar dinkin duniya mai kula da rayuwar al’umma (PNUD) ta karfafa wannan hasashe inda ta sa Nijar a lambar karshe cikin jerin kasashe dangane da kokarin kyautata rayuwa. A gefe guda kuma kungiyar Transparency International mai yaki da cin hanci a duniya ta saka Nijar a sahun gaba na kasashe masu karbar rashawa. Duk wadannan su ne ummal aba’isan gwagwarmaya da kungiyoyin kwadago da kare hakkin bil’adama suka yi har tsawon shekaru biyar.

A fannin siyasa kuwa shekaru biyar na mulkin Tanja sun kasance zagon kasa ne ga tsarin dimokaradiyya da aka shimfida da kyar da zufan goshi. Ga alama komai yana tafiya daidai saboda an shimfida dukkan gabobin hukuma da kundin tsarin mulki ya tsaida. Majalisar dokoki, kotun tsarin mulki, kotun koli, gwamnati da sauransu duk sun cike gurabbansu amma ba su kare talaka daga bala’in yunwa da fatara ba. Bugu da kari ba su taimaka wajen fitar da kasa daga cikin kangi ba. Yanci da walwala na masu galihu ne kawai. A shekarar 2003 kadai kotun tsarin mulki ta yi watsi da kudurori na majalisar ministoci fiye da goma saboda sun kaucewa dokokin kasa. Wannan yanayi shine dalilin tashe-tashen hankula da hasumi da suka wanzu tsakanin gwamnatin Hama Amadu da kungiyoyin farar hula da jam’iyyun siyasa bangaren adawa kenan.

Yunkurin kungiyoyin farar fula

Lokacin da mahakuntan jamhuriya ta biyar suka fitar da sabuwar doka mai shinfida haraji na TVA ba su yi tsammanin za su fuskanci matsala ba. Wannan zato na da alaka ne da nasarar da suka yi shekarun baya wajen murkushe duk wani bore na soja ko barazana ta kungiyoyin kwadago da sauran kungiyoyin kare hakkin bil adama. Ko kadan basu yi la’akari da kokarin fadakarwa da wayewar kan al’umma dangane da matsalolin da kasa take ciki da kungiyoyi kishin dimokaradiyya daban daban ke ayyanawa kusan tsawon shekaru biyar. A cikin wannan kokari kafofin watsa labarai masu zaman kansu sun taka rawar gani sosai musamman wajen shirya mahawarori.

Hakika magabata ba su fahimci cewar tura ta kai bango ba. Saboda haka basu damu da kafa hadin gwiwar kungiyoyin gwagwarmaya da tsadar rayuwa tun watan janairu ba. Kamar yadda gwamnati ba ta farga da bayanan da jami’an wannan hadin gwiwa suke yi cikin masalatai, unguwanni da kasuwa ba. Gwamnati na dauka cewa kiran wadannan kungiyoyi ba zai samu karbuwa ga al’ummar da ta basu cikkaken rinjaye a zabukka da aka kammala yan makwannin da suka gabata ba. Bugu da kari gwamnati na dauka cewa ai wadannan matakai umarnin kungiyar kawancen tattalin arziki na kasashen Afirka ta yamma (UEMOA) ne. Kenan ba laifin hakumar Nijar ba ne. Duk wannan bai hana kungiyoyi masu gwagwarmaya da tsadar rayuwa su ci-gaba da shirya zanga zangogi masu mahimmanci da karbuwa ga jama’a..

Ma’anar zanga zangar 15 ga watan Maris

Kungiyoyin da suka jagoranci gwagwarmaya domin cilastawa gwamnati janye dokar ta kago harajin TVA ga kayayyakin masarufi basu yi zaton kiran zai samu karbuwa ga dimbin jama’a ba. Lalle abin mamaki ne ganin dubban matasa da mata wadanda galibinsu basu faye halartar zanga-zanga ba. Kazalika abin alfahari ne ganin dubban magoya bayan jam’iyyun adawa da masu rinjaye sun kauracewa umurnin shugabanninsu don su kalubalanci zalunci.

Dalilin kuwa shine al’umma ta fusata sosai dangane da raini da wulakanci da magabata suka nuna dangane da wannan lamari.Wannan fushi na da tushe. Da farko dai saboda gwamnati ya yi niyyar daukar wadannan matakai tun zaman taron majalisa na watan disamba 2004 amma da yake gabannin zabe ne sai ta waresu daga cikin dokar kasafin kudi don makircin sijasa. Wato kada zartar da matakan ya janyo bakin jini da rashin fahimta na jama’a kuma watakila ya zama sanadiyyar rashin nasara ga zabe.

Sa’anan kuma ga shi gwamnati bata nuna damuwa ko kadan dangane da gazawar damina da karamcin abinci da jama’a ke fuskanta ba. Bayan ya musanta labarin yunwa cikin kasa, gwamnati bata tanada komai wajen agajin al’umma ba lokacin da matsalar ta bayana. Sa’annan duk tsawon yakin zabe babu alkawurran magabata ba su dauka ba. Yau an wayi gari har sun manta alhali ko wata daya ba a yi ba da suka lashe zabe. Abin nufi shine al’umma ta gaji da siyasar zalunci, handama, rashin adalci da tausayin talakkawa ta yan siyasa marasa akida da kishin kasa.ke ayyanawa shekara da skekaru. Ba karin farashin sukari, garin alkama da ruwan sha kadai ya dame ta ba.

A takaice sai mu ce bukatar al’umma ta wuce zancen soke sabon haraji kamar yadda kungiyoyin farar fula masu jagorancin gwagwarmaya suka fahimta. Za a karfafa wannan hasashe idan aka yi la’akari da nasarar yajin aiki gama gari a duk manya-mayan birane musamman ma babban birnin Yamai inda jama’a ta amsa kira dari bisa dari.

Kwalliya bata biya kudin sabulu ba

Da yake masu jagorancin gwagwarmaya ba su fahimci ainahin bukatun jama’a ba sai suka rika tafiyar hawainiya daidai lokacin da gwamnati ke nuna damuwa da dimuwa sosai. Maimakon su daga murya, su jaddada bukatar samun haske kan yadda gwamnati ke kashe kudin kasa sai jami’an hadin gwiwa suka karkata akala wajen binciken hanyoyin da za a bi don a cike gibin kasafin kudi idan an soke harajin TVA. Abin mamaki wai gwamnatin da ake zaton a matsayinta na mai alhakin jagorancin kasa tana da fasalin ayukkan gina kasa ita ce ke neman mafita ga kungiyoyin farar fula. Idan ana son gaskiya kuma ana bin ka’ida ai ba kungiyoyin farar fula za su nunawa masu iko inda zasu samun kudin kashewa kambacin hudin harajin TVA ba. Jan ragamar mulki na da sharudda. Idan ba za a iya cika su ba to bai kamata a shiga takara don yaudarar jama’a ba.

Amsa wadatacciya ita ce a kalubalanci rashin adalcin gwamnati da ke kokarin gurbata rayuwar al’umma yayin da ministoci da yan majalisa ke cin moriyar karin albashi da kudaden kashi barkatai.Bayan haka wajibi ne a jaddada bukatar samun haske kan yanda ake amfani da dukiyar kasa. Ganin magabatan kungiyoyi masu kokowa da tsadar rayuwa basu yi ma gwamnati wannan nasiha ba sai wakilan gwamnati a teburin shawarwari suka samu hamzari da kuzarin da suka rasa yan sa’o’in da suka gabata. Tare da taimakon jam’iyyun adawa wadanda suka ruwa suka yi tsaki cikin lamarin alhali kuwa bai shafe su ba, har ma gwamnati ta samu kwarin gwiwa na kin amincewa da wadansu bukatun kungiyoyin farar fula. Haka ne aka cimma yarjejeniya inda gwamnati ta soke harajin TVA kan garin alkama da ruwan sha amma ba da sukari ba. Dangane da bukatar tanadin dukiyar kasa cikin haske kuma bisa ka’ida gwamnati bata samu abin cewa illa za ta duba ta gani. Ma’ana ba wajibi ne ta aikata hakan ba.

Kenan nasarar da aka cimma gajera ce alhali kuwa akwai halin cimma mahimman gurori wadanda suka jibanci akidojin siyasa da tattalin arziki da sauransu.

Gazawar kungiyoyin Farar fula

Rashin nasara mai gamsarwa cikin yaki da tsadar rayuwa ta dogara ne bisa dalilai har uku : Na daya shine rashin alakanta yaki da tsadar rayuwa da kuma shirin <> da gwamnati ke ayyanawa bisa umurnin asusun bada lamani na duniya (FMI). Ganin yanda fiye da shekaru ashirin magabatan Nijar wannan akida su ka sa gaba abin mamaki ne a ce kungiyoyin kishin dimokaradiyya sun cimma bukatun su ba tare da sun saba ma wannan akida ba. Idan gwamnati ta ce a bar kasuwa ta yi aikinta, to kaka za a magance matsalolin rayuwa na marasa galihu ? Mai yiyuwa kuwa ne a inganta tsarin koyarwa idan kashi 80% (tamanin daga cikin dari) na malaman makaranta sun kasance yan sa-kai ne ?

Na biyu tunanen galibin jami’ai masu jagorancin wannan dawainiya shine babu siyasa cikin yunkurinsu. Saboda haka bai kamata a samu wata hulda tsakaninsu da jam’iyyun siyasa ba. Suna daukan cewa ba cikin ajandar kungiyoyin farar fula ne a binciki manufofin siyasa da tattalin arziki da magabata ke zartaswa.

Dalilin karshe ya shafi rashin ingantattun hanyoyi na tuntubar juna da tattaunawa da magoya bayan hadin gwiwa. Hakika kungiyoyin da suka kirkiro hadin gwiwa sun shinfida ka’idojin aikinsu da gurin da suka sa gaba. Amma daga bisani lokacin da hasumi ya tashi da gwamnati ai aka daina amfani da su akai akai. Bugu da kari ba a samu fahimtar juna ba dangane da yanda za a fuskanci barazanar gwamnati da kuma matsalar sadarwa da dimbin mahalarta zanga zanga a duk fadin kasa wadanda akasarinsu ba mambobin kungiyoyin da suka kira gwagwarmaya ba ne.

Ina Mafita ?

Idan ana son nan gaba yunkuri al’umma ya sami sakamako mai dorewa dole ne kungiyoyin farar fula su yi la’akari da abubuwan da ke biye. Da farko ya kamata a kiyaye da alakar ke akwai tsakanin matsalolin da jama’a ke fuskanta da manufofin siyasa da gwamnati ke ayyanawa. Yau ko’ina cikin duniya kungiyoyin farar fula sun yi imanin cewa ba za a cimma gurin kyautata rayuwar al’umma ba tare da an kawo sauye-sauye ga yanayin siyasa ba. Wato ba za su biya bukatunsu muddin suka ci-gaba da kauracewa duba matsalolin siyasa da kyamar yin ma’amala da jam’iyyun siyasa. Wannan la’akari ne ya karfafa tasirin kungiyoyin da ke fafitika da tsarin jari hujja da yaudara na duniya.

Na biyu wajibi ne a canza ra’ayi game da dimokaradiyya. Bai kamata a ce al’umma ta kan ci moriyar dimokaradiyya kawai ta hanyar jefa kuri’a ranar zabe. Tabbatar da yanci da walwala, kare hakkin dan Adam da kyautata rayuwar al’umma suna da wuya ainun idan kungiyoyin farar fula basu dauki nauyin bin sau da kafa yanda a ke gudanar da mulki da tanadin dukiyar kasa. Kazalika tsarin dimokaradiyya ba zai dore ba idan al’umma ta jahilci irin wainar da masu iko ke toyawa, wato idan bukatunta basu kasance alkiblar gudanar da mulki.


Accueil du site | Contact | Plan du site | Espace privé | Statistiques | visites : 298671

Suivre la vie du site ha  Suivre la vie du site Hausa  Suivre la vie du site Taron Al’Umma  Suivre la vie du site Sharhi   ?

Site réalisé avec SPIP 1.9.2c + ALTERNATIVES

Creative Commons License