Alternative Espaces Citoyens Niger
Bayan fiye da shekaru 10 da ako soma tonon karfen uranium a birnin Arli

Akwai alamun kamuwa daga curutukan hikimar kimiyya dake boye ga al’ummar birnin Arlit

lundi 8 mai 2006 par Hassane Boukar

Kamar dai yadda kungiya mai zaman kanta (ONG Aghir In’Man) ta bayyanawa ministan makamashin da ma’adanan kasa na jamhuriyar Nijar, a wata ziyara da ya kai a ma’aikatar tonon karfen uraniom ranar 17 ga watan fabrairu na shekarar 2006, cewa bayyanar wasu cututuka kamar su « canser » da kuma mutuwar wasu daga cikin ma’aikata da kuma tsafin ma’aikatan ma’aikatar tonon karfen uraniom dake Arlit, yana da alaka ne da kimiya ko hikimar gano curutukan dake boye da kuma matsalar kiyon lafiyar jama’a da dabbobin wannan karkara.
A gaban ire iren wadannan matsaloli da suka shafi rayuwar al’ummar da kuma mahalin wannan yanki, kungiyar ta Aghir In’Man bata zauna hannu yofi ba.
Yau tsawon shekara daya kenan da kungiyar take gwagwarmaya, domin ta jayo hankalin magabatan da kuma al’ummar kasar tare da na kasashen ketare a kan rayuwar al’ummar karkarar Arlit dake karkashin hatsari da kamuwa da curutukan hikimar kimiyya dake boye dalilin karfen uraniom da ake tonowa a wannan karkara.
Kungiyar dai ta kara bayyanawa ministan da cewa yada kayayyakin kimiyya ko hikimar curutukan boye iri iri a fadin kasar, musamman a cikin gidajen birnin Arlit, wata babbar matsala ce dake iya kawo wani cikas ga rayuwar dan adam da kuma mahali. Wannan kiran gaugawa da kungiyar keyi, ya zo daidai da lokacin da ake kokarin kafa wasu ma’aikatun tonon karfen uraniom da kuma wasu cibiyoyi.
Wannan sabuwar cibiyar, mallakar Somaïr, wace kuma za’a budawa a cikin wannan shekara, za’a kashe a kalla bishiyar itatuwa dari 2 domin share gurin kafa wannan cibiyar, kamar dai yadda kungiyar ta jadada. Bayan wasu munannan sakamako, tonon karfen uraniom din yake zayo mutane da dama masu neman aiki a jahar ta Arlit, abinda kuma ya kawo cinkoson mutane a wannan karkara, tare da kuma amfani da yawan itatuwan kuna da nauyinsu yakai ton dubu 27 a kowace shekara.
Tsawon wasu shekaru 10 da suka gabata, mutanen birnin Arlit na nemo itatuwan kuna ne a tazarar kilo meta 10 (10 km) da garin, yau ko sai suyi tafiyar kilo meta dari ko fiye da haka, kafin su samo itatuwan kuna.
Kungiyar dai ta Aghir In’Man ta na fargaba sosai da irin yadda ta gano da cewa, dajujukan kiyon dabboni sun kadanta, ko kuma ace ma babu su. Duk kuma abinda ya faru, ba wani dake da hannu dumu dumu a ciki, il’la hukumar nan ta kasar Faransa, cewa da Arewa dake shugabanci tonon karfen uraniom a jamhuriyar Nijar, wace ke da ma’aikatun biyu a karkara da suka hada da Cominak da Somaïr.
Hukumar dai, bata kiyayewa ba, bata kuma kawo kariya ga al’ummar karkarar ba, daga kamuwa ga curutukan kimiyya dake boye. Ma’aikatar bincike da kuma ganuwa da inganci ruwan da Somaïr ke amfani da su Algade, ta tabbattar da cewa, a watan Satumba na shekarar 2004 akwai wani babban makin curutukan kimiyya dake boye a cikin ruwan da ake amfani da su, a arewacin wannan karkara. _Kana kuma a fitowar sa ta ranar 26 ga watan Afrilu na shekarar 2005, jaridar le monde ta kasar Faransa ta bayyana cewa, sakamakon bincikken ruwan karkarar ta Arlit da ankai ya nuna cewa, akwai nau’in curutukan 2 da suka hada da Alpha da kuma Beta da suka zarce daga ka’idodin kungiyar kiyon lafiya ta duniya.
Ta hanyar irin wadannan labarai, da kuma jan kokarin kungiyar Aghir In’Man, wasu kungiyotin kasashen turai musamman SHERPA da kuma kommiti bincike da watsa labarai mai zaman kan sa a kan curutukan boye, suka bada damar ganuwa da cewa, Arewa ta kaucewa hanyoyi da matakan da ya kamata a dauka domin kare al’ummar daga curutukan boye.
Duk irin wadannan matsalolin rayuwa da al’ummar da kuma mahalin ke fuskanta, boye suke, ba a bayyane ba, ga al’ummar kasar.
Kahohin watsa labarai, ba su bada karfi ba, a kan irin wadannan labarai, kuma kadannan ne daga cikin kungiyoyi masu zaman kansu, suke bada nasu jan kokakari a game da irin gwagwarmayar da kungiyar ta Aghir In’Man ta sa a gabanta.
Wani abin kunkumi da ban takaici shine, wannan abu na faruwa ne a cikin kasar da yau kusan shekaru 5 kenan da aka gano da cewa, fiye da yara dari 4 ne suka nakasa, dalilin wasu ruwa da sun ka sha, da kampanin samarda ruwan sha a kasar Nijar SNE wace yau take a hannun VIVENDI WATER, ya sayar a garin Tsibiri Maradi , wasu daga cikin wadannan yara, sun gurgunta har il’la masha Allahu.
Ganin sakaci da kuma rishin yin wani yunkuri da zai kare al’ummar da mahali daga barnar Arewa, ya sa kungiyar ta Aghir In’Man ta nemi ministan makamashin da ma’adanan kasa, da ya kula da kuma maida himma domin kawo kariya ga mahali da Arewa ke niyar nakasarwa a dalilin tonon karfen uraniom. A cewar dai kungiyar, idan Arewa ta tsuduma rayuwar kusan mutane dubu 80 dake zaune a wannan yanki cikin wani halin kaka ni kai, to ba komai ba ne, il’la kawai saboda gwamnatin Nijar na alfahari ne da wasu yan kudade da basu taka kara suka karya ba, a karkashin kasuwanci wannan karfen uraniom da ake tonowa a kasar.
Abba Hassan

Accueil du site | Contact | Plan du site | Espace privé | Statistiques | visites : 45639

Suivre la vie du site ha  Suivre la vie du site Hausa  Suivre la vie du site Labarun Nijar   ?

Site réalisé avec SPIP 1.9.2c + ALTERNATIVES

Creative Commons License