Alternative Espaces Citoyens Niger

Sharhin Jaridun Mako

mardi 8 juillet 2008 par Souley Magé Regeto

A wannan mako rinjayen jaridun kasar Nijar masu fitowar mako-mako sun mayar da akalar labaransu ne a kan tsarewar tsohon faraminista kuma shugaban jam’iyar MNSD Nassara Hama Amadu a gidan kason Kutukale, bayanda yan majalisar dokokin kasa suka jefa kuri’ar amincewa da a gurfanar da tsohon faraministan a gaban kotu. Sai kuma labarin k’ik’i-k’ak’ar neman shugabanci jam’iyar MNSD Nassara bayan Hama Amadu.

A fitowarta ta makon jaridar La Griffe ta ruwaito cewa, bayanda zababin yan majalisar dokokin kasa, suka jefa kuri’ar amincewa da a gurfanar da tsohon faraministan a gaban kotun shara’a, kotun ta bada izinin a tsare tsohon faraministan kuma shugaban jam’iyar MNSD Nassara a gidan kurkukun Kutukale dake a tazarar kilo mita 45 da babban birnin kasa(Yamai). Jaridar ta bayyana cewa an dai gaggauta awaitar da abubuwan ga tsohon faraminista kuma shugaban jam’iyar dake mulkin kasar a yanzu. Tura keyar Hama Amadu a gaba zuwa gidan kurkuku Kutukale ya biyo bayan kwana biyu ne da yan majalisar dokokin kasa suka jefa kuri’ar a gurfanar da shi a gaban babban kotun shara’a. To, yanzu da shugaban jam’iyar ta MNSD Nassara yake tsare a gidan kaso, mine ne makomar jam’iyar?

A ranar ta 26 ga watan Yuni magoya bayan tsohon faraministan da dama ne suka tabbatar da cewa Hama Amadu ba zaya komawa gidansa ba. Bayanda ya kwashe awa biyu a gaban masu shara’a, sai tsohon jagoran ministocin ya samu kansa a hannun yan sanda da suka rakasa zuwa Kutukale. Jami’an tsaron sun yi amfani da barkonon tsohuwa ne, don watsar da magoya bayan Hama Amadu dake jiran ganin irin wainar da za’a toyawa a wannan rana. Wasu sun tsira da cinansu, wasu kai saida aka kai su babban assinbiti kasa domin tserar da rayuwarsu kamar yadda jaridar ta la Griffe ta ruwaito.

Ranar Alhamis 26 ga watan Yuni shekarar 2008, rana ce da ta rubutu a cikin kundin rike tarihin kwakwalwar Hama Amadu da kuma mazauna unguwar Yantala Bas makwabta ga babban kotu kasa. An jingine Hama Amadu a gidan kaso, saboda kotun ta zargesa da sama da fadi da kudaden tallafi ga kahohin watsa labarai da gwamnati ta bayar a shekarar 2001 lokacin yana shugaban gwamnati. Kamar yadda jaridar le Republicain ta rubuto.

Jaridar la Roue da l’histoire ta rubuto cewa yanzu da shugaban jam’iyar MNSDA Nassara yake a kurkuku sai ya ya? Wasu majiyoyin labarai masu kusantar jam’iyar su bayyana cewa, ana gobe ranar kai Hama a gaban kotun, ya mika shugabanci jam’iyar ga babban magatakardan jam’iyar Salisu Mahamadu Habi, to sai dai kuma ba san abinda dokokin jam’iyar suka ce ba lokacin da shugaban jam’iyar baya nan. Wannan harakar kudaden kahohin watsa labarai ta kara munanta ajajjiyar dake tsakanin magoya bayan Hama Amadu da kuma faraminista Seini Umaru, wanda tun lokacin da Hama ya fara karbar kira a gaban kotu magoya bayan Hama suke neman faraministan da ya yi murabus, to sai dai abin ya ci tur har suna ganinsa a matsayin wanda bai san ciwon kansa ba.

A nata bangare jaridar le Democrate ta zakulo da maganar da Hama Amadu ya yi a lokacin da ya kirai taron manema labarai a gidansa, wato cewa, idan aka kamasa hanya zata magana. Gaskiya ne birnin Yamai yana kumshe da dumbi jama’a magoya bayan jam’iyar MNSD Nassara, wadanda Hama yake gani tamkar jama’arsa ce. To, amma da yake gwamnati ta zuba jami’an tsaro ko ina, kuma ta bukaci gaskiya ta bayyana ko ina take, hanyar bata yi Magana ba. Birnin na Yamai da ake ganin tamkar gidan MNSD Nassara ne, ba hakan ba ne, saboda a cikin Yamai din ma jam’iyar ta samu rabuwar kawuna kamar yadda ta samu barakar a sauran rassanta dake cikin kasa.

Jaridar ta le Democrate ta fassara cewa, hanyar bata yi Magana ba kamar yadda Hama Amadu da sauran yan amshinsa suka yi fata, saboda mutane sun gaji da haihuwa rana na kashewa, suna gwagwarmaya saboda kyautata rayuwar wasu, a yayinda su tasu rayuwar sai kara lalacewa take. Hanyar ba zata Magana ba, saboda magoya bayan Hama su razana sosai, suna gudun kar su ce kala abin ya fado a kansu. Hanyar bata Magana, saboda yanzu kowa ya san mahimmanci demokaradiya a cikin kasar.

Wane ne zaya jagorancin jam’iyar MNSD Nassara bayan Hama Amadu? Kalmar tambayar da jaridar le Canar Déchainé ta yi kenan. Amshar wannan tambaya ta zamanto tamkar cacar kale-kale, wato akwai tabbatatu, akwai kuma wadanda ake shakku a kansu. Idan jam’iyar MNSD Nassara kungiyar farar hula ce mai zaman kanta to da Salisu Mahamadu Habi ne ya cancanta. To, amma da yake siyasa ce, wadda a cikinta ba a kiyayewa da komai akwai matsala. A cikin hasashen neman gaskiya, wato wanda za ya canji Hama Amadu, ta kan yi yuwa ya zamanto wani shugaban reshen jam’iyar ne na wata jaha, kamar Seini Umuru shugaban jam’iyar reshen Tilliberi ko Ali Sabo shugaban jam’iyar reshen Maradi. Akwai kuma wani shugaban reshen jam’iyar wanda aka yawaita maganarsa a cikin jaridu, wato Ibrahim Fukuri na reshen Diffa kuma makusanci shugaban kasa kana kuma ga ministan cikin gida na yanzu Albade Abuba shi ma ana ganin kamar za’a yi da shi. Bayan haka akwai wasu jigogi biyu dake ketare, wato tsohon faraminista Maman Umaru da kuma tsohon faraminista Amadu Bubakar Cise wadanda ke iya dawowa gida su nemi wannan matsayi. Kamar yadda jaridar le Canard Déchainé ta ruwaito.


Accueil du site | Contact | Plan du site | Espace privé | Statistiques | visites : 45639

Suivre la vie du site ha  Suivre la vie du site Hausa  Suivre la vie du site Labarun Nijar   ?

Site réalisé avec SPIP 1.9.2c + ALTERNATIVES

Creative Commons License