Alternative Espaces Citoyens Niger
Burin shugaban kasa Tanja Mahamadu

"Sai an yi Usula, saboda al’umma ta bukaci in tsaya"

mercredi 27 mai 2009 par Souley Magé Regeto

Wannan shi ne furucin da shugaban kasa Tanja Mahamadu ya yi a cikin wata fira da ta hada shi da jaridar “Liberation” da kuma talabizon na Faransa 24 na kasar Faransa. Shugaban kasa Tanja Mahamadu ya yi wannan furuci ranar 04 ga watan Afrilu shekarar 2009, albarkacin bukukuwan aza dan faragen farko na ginin kampanin AREVA, kampanin da za ya hakar karfen Uranium na dabagar Imuraren. A yanzu dai ta tabbata Shugaban kasar Nijar Tanja Mahamadu na bukatar Zarcewa ko yana bukatar a kara masa shekaru uku, kamar yadda wasu yan kasa masoyan tazarce, suka bukata a cikin wata makala tasu da suka mika ga majalisar dokokin kasa ranar 22 ga watan Disamba na shekarar 2008.

"kundin mulkin kasa ya farlanta Usula, gashi kuma al’umma ta bukaci in tsaya, ba za ni kuma sabawa bukatar yan kasa ba".

Haka shugaban kasar ya jadaddawa kafofin labaran biyu na kasar Faransa. Yau dai fiye da watani hudu kenan da wasu yan kasa suka fara tarurukan assassa tazarcen shugaba a cikin kasa, a yayinda kuma a nasu bangaren kungiyoyin fararen hullar kasa suka jajirce kuma suka tsaya a kan bakansu na yan gwagwarmayar tabbatar da adalci tare da nuna cilas a kiyayye kundin tsarin mulkin kasa da shifida demokaradiyya a cikin kasa. A bangaren jam’iyun siyasar kasa, wadanda ake dubi su fitar da sanarwoyin kalubale a kan wannan burin tazarcen shugaban kasa Tanja Mahamadu, musamman jam’iyun adawa sunyi dogon barci, sai a lokacin da abin ya yi tsami, lokacin nan ne jam’iyar PNDS Tarayya ta fitar da wata sanarwa, tare da gabatar da wani taron gangami a unguwar Lazare birnin Yamai, inda ta kalubalanci masoyan tazarcen da tabbatar da cewa, aikata tazarce a cikin kasa, wani juyin mulki ne. Gaskiya ne kundin tsarin mulkin kasa bai haramta shiga usual ba, to amma yana da kyau ayi usular kamar yadda dokokin kasa suka gindaya, wato maganar ta shiga dakin Majalisar dokokin kasa, yan Majalisar su tattauna kana su jefa kuri’ar amincewa da gabatar da usular. Idan aka samu kashi uku cikin huda (3/4) na yan Majalisar dokokin, to a lokacin nan ne yan kasa zasu jefa kuri’ar iya ko a-a.

Babbar matsalar kuma abin fargaba a cikin zukatan yan kasa shi ne, ya ya wakilansu, wato yan Majalisar dokokin kasa zasu karbar wannan maganar shiga zaben usula a Majalisar dokokin kasa? Shin zasu aiki da abin da talakawan kasa ke so ko ko zasu aiki da abin da su yan siyasa suke bukata? Duk dan kasa mai kishin demokaradiyya da kundin tsarin mulkin kasa ba zaya rumtse ido ya rufe kunnuwansa ba yana ji yana gani a kariyar dokokin mulkin kasa don alfanun wasu yan tsirarru. Shugaban kasa Tanja Mahamadu, ya bayyana cewa “al’ummar kasa ta bukaci ya tsaya”, wacce al’umma ce wannan? Ita kuma wadda ta fito ta nuna a kiyaye kundin mulkin kasa me a sunanta? A yau abin bayyane yake karara cewa, yan gwagwarmayar tazarcen, ba ruwansu da wani kundin mulkin kasa, abin da ya dauki hankalinsu, shi ne sahihancin ci gaban mulkin shugaban kasa Tanja Mahamadu ko da kuwa abin ya keta dokokin mulkin kasa ne, ba ruwansu. Ya kamata duk inda dan Nijar yake zaune ya dauki gaban gabarar wannan magana ta tazarce, a matsayin hanyar keta kundin mulkin kasa da gurbata tafarkin mulkin demokaradiyya. Yan kasa su nuwa duniya abin da a ke ciki kowa ya sani. A mayar da wannan batu abin tattaunawa duk fadin kasar da duk inda dan Nijar yake zaune. Wannan zai ja hankalin masu fada a ji na yammacin turai su tsoma baki a cikin harkar. Hakan zai sa abubuwa su daidaita. Amma dai bai kamata a zuba ido ba tare da tunanin cewa, in ba shugaban kasa Tanja Mahamadu ba, ba wani dan Nijar da za ya ci gaba da aiwatar da kuma fitar da hanyoyin gina kasa ba. A yau Nijar ta na cikin kasashen duniya da ake alfahari da su wajen kiyaye kundin mulkin kasa, don haka bai kamata yan kasa su bi son zuciya ba, su bar wannan abu ya afku.


Accueil du site | Contact | Plan du site | Espace privé | Statistiques | visites : 45639

Suivre la vie du site ha  Suivre la vie du site Hausa  Suivre la vie du site Labarun Nijar   ?

Site réalisé avec SPIP 1.9.2c + ALTERNATIVES

Creative Commons License