Alternative Espaces Citoyens Niger http://www.alternativeniger.org/ ha SPIP - www.spip.net Fira da Musa Cangari Babban Magatakardan Kungiyar Alternative Espace Citoyen (AEC) Yamai http://www.alternativeniger.org/spip.php?article508 http://www.alternativeniger.org/spip.php?article508 2010-11-08T13:23:47Z text/html ha Souley Magé Regeto Labarun Nijar Shugaban kasar Cana Hu Jintao ya kai wata ziyar aikin kwana uku a kasar Faransa, daga ranar 4 zuwa 7 ga watan Nobamba na shekarar 2010. A karkashin wannan ziyar aiki, shugaban kasar Cana Hu Jintao da takwaransa na kasar Faransa Nikolas Sarkozi sun rattaba hannu a kan wasu yarjejeniyoyi na kwagila tsakanin kasashen biyu, wadanda suka ba Faransa damar samu tsabar kudin Amirka dala miliyan dubu 20 daidai da kudin Faransa (Yuro) miliyan dubu 14 ke nan. A cikin kwangilolin suka shiga tsakanin (...) - Labarun Nijar

Shugaban kasar Cana Hu Jintao ya kai wata ziyar aikin kwana uku a kasar Faransa, daga ranar 4 zuwa 7 ga watan Nobamba na shekarar 2010. A karkashin wannan ziyar aiki, shugaban kasar Cana Hu Jintao da takwaransa na kasar Faransa Nikolas Sarkozi sun rattaba hannu a kan wasu yarjejeniyoyi na kwagila tsakanin kasashen biyu, wadanda suka ba Faransa damar samu tsabar kudin Amirka dala miliyan dubu 20 daidai da kudin Faransa (Yuro) miliyan dubu 14 ke nan. A cikin kwangilolin suka shiga tsakanin kasashen biyu, akwai wadda ta shafi karfen Yuranium wanda kampanin Areva na kasar Faransa ke haka a cikin karkarar Arlit yakin Agadez Jamhuriyar Nijar. Kasar Cana da kasar Faransa, kasashe biyu ne dake huldar tattalen arziki da kasar Nijar musamman a kan abin da ya shafi ma'adannan kasa. To ko wadannan yarjejeniyoyi na iya taba tattalen arzikin kasar Nijar ? Me kuma yan kasar Nijar ke fargaba a ciki ? Ga nazarin da Malam Musa Cangari Babban Magatardan Kungiyar Alternative Espace Citoyen (AEC).

Malam Musa Cangari ya fara da cewa : tabbat duk abubuwan da suka wakana, sun shafi kasashen biyu, kuma sun shafi kasar Nijar. Dalilin da yasa suka shafi Nijar, shi ne, a cikin yarjejeniyoyin da suka sa hannu, akwai wadda ta shafi hakar karfen Yuranium, wanda kampanin AREVA na kasar Faransa ke haka a jamhuriyar Nijar yau fiye da shekaru 40. sanin kowa ne, a da kampanin Areva kadai ne ke hakar wannan karfe a doron kasar Nijar. To amma a cikin yan shekarun nan shuwagabanin kasar Nijar sun bude kasuwar samun kwangilar hakar Yuranium ga kowa, wato kowace kasa ta duniya na iya ta zo a yi yarjejeniya da ita saboda ita ma ta nemi wani abu daga cikin arzikin ma'adannan kasar da Allah ya albarkanci Nijar da su. A cikin kasashen da suka samu wannan kwatara ta hakar Yuranium, akwai kasar Cana wadda ta samu har da ta tonon man petur. Sanin kowane lokacin da wannan yarjejeniya ta shiga tsakanin kasar Nijar da Cana kampanin Areva bai ji dadi ba. Wato banda wurare biyu da kampanin Areva yake da shi, wato na SOMAIR da COMINAK, Areva ta so ta samu wani lasisin buda wani sabon kampanin hakar Yuranium, wannan kuma shi ne na IMURAREN. Shi ma da kyar da walahau la suka same shi, saboda kasar Nijar ta nemi a kara kudin Yuranium. Bayan ja-in-ja tsakanin kasar Nijar da Areva aka samu yarjejeniya wadda ta ba su damar tonon rijiyar ta IMURAREN. A yau ita ma kasar Cana tana nan, ke nan Areva ta samu kishiya, wato ana iya a ce Cana ta shigo gonar Areva. Shigowar Cana da wasu kasashe cikin gonar ta Areva ya ba yan kasar Nijar damar cewa, tun da masoyan Nijar masu yawa ne, irin su Kanada da Indiya da Ostaraliya da dai sauransu, ko ina mana da masoya, wato masu bukatar su ma su shigo su hako wannan karfe na Yuranium da wasu ma'adannan kasa, ke nan wata dama ce gare mu da za mu sayar da kayanmu ga wanda muke so kuma da daraja. Wannan bai yi ma Areva dadi ba. To ita ma karsar Cana ta yi yarjejeniya da kasar Nijar.

A yarjejeniyar da ta shiga tsakanin Cana da Faransa, ita Areva ta bada shawarar kasashen biyu su hada gwiwa. Su hada gwiwa tsakaninsu su biyu, don saboda harakar nukileya gabadaya. Wato tun daga hako karfen Yuranium har zuwa sarrafa shi zuwa ga wani makamashi ko wani makami mai lizzami, duk dai abin da ake iya yi da Yuranium. Takamaimai dai shi ne suna son su yi aikin tare da Cana. Tuni dai a cikin yarjejeniyar sun yi dahir da cewa, kampanin Areva za ya ba kasar Cana ton dubu 20 na karfen Yuranium kowace shekara, har tsawon shekaru 10 a nan gaba. Banda wannan kuma, za su kafa wani kafani na sarafa nukileya tsakaninsu. Haka kuma suka yarda a kan za su aikin tare da kasar Cana a kamfanin hakar karfen Yuranium na Imuraren, wato kasar Cana zata daukar wani hannun jari a cikin kamfanin na Imuraren. Idan suka cimma haka, ke nan kasar Cana da Faransa bakinsu daya, babu gasa tsakaninsu. Idan kuma tabbat ta kasance haka, kasar Nijar ba zata ji dadi ba. Saboda idan babu gasa tsakaninsu, wato idan ba su kasance kishiyoyin juna ba, to abin ba ya gyra kasar Nijar. Amma in akwai gasa tsakaninsu, to a duk lokacin da kasar Nijar ta gano da ba ta jin dadi aiki da wani daga cikinsu, sai ta je wajen wacan ta ce masa kai me ka ce? Wato abin kamar ka je kasuwa ne, idan ya kasance dan kasuwa daya ne ke sayar da wani abu, to yadda ya gadama zai sayar. To amma idan yana da abokan gasa, to sai ka kewaya wajen wanda za ku jituwa. Yau Nijar, ita ce ke da karfen Yuranium na saidawa, ke nan in akwai masu bukata da dama, irinsu Cana da Indiya da Ostaraliya da Faransa da Kanada da dai sauransu, sai ta tsayar da kudin karfen Yuranium yadda ta gadama, mai bukata ya saya, wanda kuma bay a iyawa sai ya bar wuri. Hakan kuma zai sa kasashen su yi kokowa domin kowa ya samu shiga. Amma in har ya zamanto bakinsu daya, to kamar mutum daya ne ke gaban kasar Nijar, bata iya buga teburi ta ce ga yadda take so a yi. Wannan yarjejeniya da ta shiga tsakanin Cana da Faransa ta nuna cewa, ba wai masu gasar juna ba ne. Lokacin da shugaban kasar Nijar ya nemi a kara darajar farashen karfen Yuranium, da bay a kasance akwai wasu kampanonin kasashen duniya dake bukatar ba, wadanda suka bayyana, da Areva da kasar Faransa ba za su yarda a kara wani abu ba ga yadda ake a da. To amma da yake akwai su, Areva da Faransa sun yarda, saboda sanin cewa, kasar Nijar na iya ce masu, ba su kadai ke bukatar ba, za a bada kwangilar ga wasu mabukata. Yanzu kuma sun kewaye kasar Nijar, sun je, sun hada baki da kasar da take takama da ita, wato Cana, ke nan yanzu tamkar kasa daya ce ke hakar karfen na Yuranium. A cikin yarjejeniyar da suka yi, akwai wadda ta hada kampanin nukileya na kasar Faransa da Cana, haka kuma akwai ta wani kampanin hakar man petur na kasar Faransa da na Cana. A nan ma kasar Nijar na iya fargaban cewa, watakila, a nan gaba suna iya suyi wani hadin gwiwa a kan hako man petur ma. Sanin kowane, kasar Cana ce ta samu lasisin hakar man petur din kasar Nijar, har ma da na matatar man petur din. Ke nan suna iya cewa, yadda muka bude maku shiga hakar Yuranium ta Imuraren, kuma ku bude mana hakar man petur. Ta nan suna iya samun gamin baki. Wannan kuma ya kamata ya ja hankalin yan kasa, saboda kasar Nijar ce ke da Yuranium da man petur dinta, amma wasu kasashen ketare can ke wani hadin gwiwa a kan hakarsu. Rishin tsoma kasar Nijar cikin wannan yarjejeniya, Wato kafata ba tare da shawartar Nijar ba, nada alaka da yadda muka yi yarjejeniya da kasashen masu hakar ma'adannan kasa. Da ya kasance a cikin yarjejeniyar mun ce, kamar kowane kampani zai alaka ko kafa wata yarjejeniya da wata kasa, sai an yi shawara da kasar Nijar za a yi haka, wato ya shafeta, to da a nan kasar Nijar zata iya fitowa ta ce ma kasar Faransa, kampanin SOMAIR da COMINAK da na IMURAREN da muka ba ku, ba don ku hada da wasu ba ne. Da kasar Nijar ta ce sai a yi shawara da ita da haka ne. A lokcin da ake zazzafar rigima a kan farashen Yuranium, akwai wani kampani na kasar Kanada, wanda shi ma ya samu lasisin izinin hakar Yuranium din. Shi ma wannan lasisi, Areva ce ta kewaya ta saye shi daga hannun kasar ta Kanada. Wato lasisin da kasar Nijar ta hana mata, ta bayar da shi ga kasar Kanada ya zama nata. Hada baki tsakanin Cana da Faransa, daga baya suna iya saye duk wani lasisi da aka ba wata kasa ko wani kampani, wato komai ya zama a hannunsu. Wato ya zama aikin mutum daya. Ba kuma abin mamaki ba ne Areva ta saye duk wani lasisi na kasar Cana. Ana iya zaton watakila abin ba zai yiyuwa ba, amma kuma ba za a fitar da tsammani ba. Bayan haka, wannan hadin kai tsakanin Faransa da Cana yakan iya taba farshen da aka tsayar tsakanin kasar Nijar da wadanda ta ba lasisin hakar ma'adannan kasar. Saboda da ma ba da son Areva aka basu lasisin ba, ya zama cilas ne. In ma ba su sauke farashen ba, suna iya hana ma kasar Nijar fitowa da wata hujjar nuna wata bukatar kara farashen. Dalili kuwa shi ne, sun yi baki daya, to ga wa Nijar zata dogara ta ce masa, shi tana son ya gyara zamansa da ita. Wannan kuma tabbat wani cikas ne. Bisanin wannan hadin gwiwa suna iya cewa, a je a yi magana da kasar Nijar ta rage farashe.

Abin lura a nan shi ne me? Kasar Faransa tana jan kokari ne don ta rike matsayinta da darajarta a yankin Sahel gabadaya, musamman ma a kasar Nijar. Wato ta rike makaminta na sahun gaba kuma ita ce kasar da ake aiki da ita. Yanzu ma idan aka dubi harakar ga ta Alka'ida wadda ke gudana a cikin arewacin kasar Nijar, kasar Faransa ta zo da sojojinta a cikin kasar Nijar, wannan kuma wani abu ne da ba a taba gani ba. A da sun zauna da wani karamin sansanin soje a kasar Nijar, amma yau da shekaru da dama da suka bar wuri. Yanzu, kuma watakila suna da niyar kafa ta su barikin soje a kasa. Wato kamar yadda suka yi a kasar Cote D'Ivoir da sauran kasashen Afrika. Sun nemi su kai sojojinsu a kasar Mali amma abin ya ci tur, amma sun je su yi wata yarjejeniya da kasar Moritaniya, wadda zata kawo sojojinta a kasar Mali, don su yi kokowa da alka'ida. Amma kuma ai manazarta da dama sun gano da cewa, bayan kasar Moritaniya, Faransa ce ke labe tana jagorancin dukan abubuwa. Su kuma kawo wasu yan sojoji a kasar Burkina Faso.

A shekarun baya Amirka ce ta kawo wani shiri na yaki da ta'addanci, ta kawo sojojinta da manema labarai da dai sauransu dake aiki da jami'an tsaron kasa. Wani tsari ne da suka so daukar duk yankin na Sahel ta hanyar wani furoje mai sunan PAN SAHEL INITIATIVE. Amirkawa ne ke wannan aiki tare da sojojin kasar Nijar da na Mali da dai sauransu. Yanzu ita ko Faransa na son ta shigo wannan aiki, saboda tana ganin kamar Amirka ta shigo gonarta ne. wato yanzu Faransa ta dawo da karfi tana son ta kula da duk wannan yanki na kasashen da ta mallaka. Dalili kuwa shi ne arzikin ma'adannan kasa da yankin ya kunsa, ke nan ba za su yarda ba wadansu su dauka ko su tona. Dole ita Faransa ta kare matsayinta na wadda ta mallakin kasashen a da. Wannan kuma wani sabon salo ne na mulkin mallaka suke kokarin asassawa. Abin da ya yi masu sauran yanzu shi ne, su samu damar kafa sansanin sojojinsu, watakila ma su shiga cikin harakokin zaben shuwagabaninmu. Saboda hakan zai ba su damar samu wani Karen farautarsu, dan amsar Shatansu, wanda zai kare duk wani alfanu nasu a cikin yankin. A taikaice dai wannan yarjejeniya ta shafi kasar Nijar gadan-gadan, amma da yake ba mu da bakin Magana, ana iya a zalumce mu ta wannan hanya.

"Sai an yi Usula, saboda al'umma ta bukaci in tsaya" http://www.alternativeniger.org/spip.php?article416 http://www.alternativeniger.org/spip.php?article416 2009-05-27T13:01:45Z text/html ha Souley Magé Regeto Labarun Nijar Wannan shi ne furucin da shugaban kasa Tanja Mahamadu ya yi a cikin wata fira da ta hada shi da jaridar “Liberation” da kuma talabizon na Faransa 24 na kasar Faransa. Shugaban kasa Tanja Mahamadu ya yi wannan furuci ranar 04 ga watan Afrilu shekarar 2009, albarkacin bukukuwan aza dan faragen farko na ginin kampanin AREVA, kampanin da za ya hakar karfen Uranium na dabagar Imuraren. A yanzu dai ta tabbata Shugaban kasar Nijar Tanja Mahamadu na bukatar Zarcewa ko yana bukatar a (...) - Labarun Nijar

Wannan shi ne furucin da shugaban kasa Tanja Mahamadu ya yi a cikin wata fira da ta hada shi da jaridar “Liberation” da kuma talabizon na Faransa 24 na kasar Faransa. Shugaban kasa Tanja Mahamadu ya yi wannan furuci ranar 04 ga watan Afrilu shekarar 2009, albarkacin bukukuwan aza dan faragen farko na ginin kampanin AREVA, kampanin da za ya hakar karfen Uranium na dabagar Imuraren. A yanzu dai ta tabbata Shugaban kasar Nijar Tanja Mahamadu na bukatar Zarcewa ko yana bukatar a kara masa shekaru uku, kamar yadda wasu yan kasa masoyan tazarce, suka bukata a cikin wata makala tasu da suka mika ga majalisar dokokin kasa ranar 22 ga watan Disamba na shekarar 2008.

"kundin mulkin kasa ya farlanta Usula, gashi kuma al'umma ta bukaci in tsaya, ba za ni kuma sabawa bukatar yan kasa ba".

Haka shugaban kasar ya jadaddawa kafofin labaran biyu na kasar Faransa. Yau dai fiye da watani hudu kenan da wasu yan kasa suka fara tarurukan assassa tazarcen shugaba a cikin kasa, a yayinda kuma a nasu bangaren kungiyoyin fararen hullar kasa suka jajirce kuma suka tsaya a kan bakansu na yan gwagwarmayar tabbatar da adalci tare da nuna cilas a kiyayye kundin tsarin mulkin kasa da shifida demokaradiyya a cikin kasa. A bangaren jam'iyun siyasar kasa, wadanda ake dubi su fitar da sanarwoyin kalubale a kan wannan burin tazarcen shugaban kasa Tanja Mahamadu, musamman jam'iyun adawa sunyi dogon barci, sai a lokacin da abin ya yi tsami, lokacin nan ne jam'iyar PNDS Tarayya ta fitar da wata sanarwa, tare da gabatar da wani taron gangami a unguwar Lazare birnin Yamai, inda ta kalubalanci masoyan tazarcen da tabbatar da cewa, aikata tazarce a cikin kasa, wani juyin mulki ne. Gaskiya ne kundin tsarin mulkin kasa bai haramta shiga usual ba, to amma yana da kyau ayi usular kamar yadda dokokin kasa suka gindaya, wato maganar ta shiga dakin Majalisar dokokin kasa, yan Majalisar su tattauna kana su jefa kuri'ar amincewa da gabatar da usular. Idan aka samu kashi uku cikin huda (3/4) na yan Majalisar dokokin, to a lokacin nan ne yan kasa zasu jefa kuri'ar iya ko a-a.

Babbar matsalar kuma abin fargaba a cikin zukatan yan kasa shi ne, ya ya wakilansu, wato yan Majalisar dokokin kasa zasu karbar wannan maganar shiga zaben usula a Majalisar dokokin kasa? Shin zasu aiki da abin da talakawan kasa ke so ko ko zasu aiki da abin da su yan siyasa suke bukata? Duk dan kasa mai kishin demokaradiyya da kundin tsarin mulkin kasa ba zaya rumtse ido ya rufe kunnuwansa ba yana ji yana gani a kariyar dokokin mulkin kasa don alfanun wasu yan tsirarru. Shugaban kasa Tanja Mahamadu, ya bayyana cewa “al'ummar kasa ta bukaci ya tsaya”, wacce al'umma ce wannan? Ita kuma wadda ta fito ta nuna a kiyaye kundin mulkin kasa me a sunanta? A yau abin bayyane yake karara cewa, yan gwagwarmayar tazarcen, ba ruwansu da wani kundin mulkin kasa, abin da ya dauki hankalinsu, shi ne sahihancin ci gaban mulkin shugaban kasa Tanja Mahamadu ko da kuwa abin ya keta dokokin mulkin kasa ne, ba ruwansu. Ya kamata duk inda dan Nijar yake zaune ya dauki gaban gabarar wannan magana ta tazarce, a matsayin hanyar keta kundin mulkin kasa da gurbata tafarkin mulkin demokaradiyya. Yan kasa su nuwa duniya abin da a ke ciki kowa ya sani. A mayar da wannan batu abin tattaunawa duk fadin kasar da duk inda dan Nijar yake zaune. Wannan zai ja hankalin masu fada a ji na yammacin turai su tsoma baki a cikin harkar. Hakan zai sa abubuwa su daidaita. Amma dai bai kamata a zuba ido ba tare da tunanin cewa, in ba shugaban kasa Tanja Mahamadu ba, ba wani dan Nijar da za ya ci gaba da aiwatar da kuma fitar da hanyoyin gina kasa ba. A yau Nijar ta na cikin kasashen duniya da ake alfahari da su wajen kiyaye kundin mulkin kasa, don haka bai kamata yan kasa su bi son zuciya ba, su bar wannan abu ya afku.

Sharhin Jaridun Mako http://www.alternativeniger.org/spip.php?article398 http://www.alternativeniger.org/spip.php?article398 2008-07-08T15:56:52Z text/html ha Souley Magé Regeto Labarun Nijar A wannan mako rinjayen jaridun kasar Nijar masu fitowar mako-mako sun mayar da akalar labaransu ne a kan tsarewar tsohon faraminista kuma shugaban jam'iyar MNSD Nassara Hama Amadu a gidan kason Kutukale, bayanda yan majalisar dokokin kasa suka jefa kuri'ar amincewa da a gurfanar da tsohon faraministan a gaban kotu. Sai kuma labarin k'ik'i-k'ak'ar neman shugabanci jam'iyar MNSD Nassara bayan Hama Amadu.
A fitowarta ta makon jaridar La Griffe ta (...) - Labarun Nijar
A wannan mako rinjayen jaridun kasar Nijar masu fitowar mako-mako sun mayar da akalar labaransu ne a kan tsarewar tsohon faraminista kuma shugaban jam'iyar MNSD Nassara Hama Amadu a gidan kason Kutukale, bayanda yan majalisar dokokin kasa suka jefa kuri'ar amincewa da a gurfanar da tsohon faraministan a gaban kotu. Sai kuma labarin k'ik'i-k'ak'ar neman shugabanci jam'iyar MNSD Nassara bayan Hama Amadu.

A fitowarta ta makon jaridar La Griffe ta ruwaito cewa, bayanda zababin yan majalisar dokokin kasa, suka jefa kuri'ar amincewa da a gurfanar da tsohon faraministan a gaban kotun shara'a, kotun ta bada izinin a tsare tsohon faraministan kuma shugaban jam'iyar MNSD Nassara a gidan kurkukun Kutukale dake a tazarar kilo mita 45 da babban birnin kasa(Yamai). Jaridar ta bayyana cewa an dai gaggauta awaitar da abubuwan ga tsohon faraminista kuma shugaban jam'iyar dake mulkin kasar a yanzu. Tura keyar Hama Amadu a gaba zuwa gidan kurkuku Kutukale ya biyo bayan kwana biyu ne da yan majalisar dokokin kasa suka jefa kuri'ar a gurfanar da shi a gaban babban kotun shara'a. To, yanzu da shugaban jam'iyar ta MNSD Nassara yake tsare a gidan kaso, mine ne makomar jam'iyar?

A ranar ta 26 ga watan Yuni magoya bayan tsohon faraministan da dama ne suka tabbatar da cewa Hama Amadu ba zaya komawa gidansa ba. Bayanda ya kwashe awa biyu a gaban masu shara'a, sai tsohon jagoran ministocin ya samu kansa a hannun yan sanda da suka rakasa zuwa Kutukale. Jami'an tsaron sun yi amfani da barkonon tsohuwa ne, don watsar da magoya bayan Hama Amadu dake jiran ganin irin wainar da za'a toyawa a wannan rana. Wasu sun tsira da cinansu, wasu kai saida aka kai su babban assinbiti kasa domin tserar da rayuwarsu kamar yadda jaridar ta la Griffe ta ruwaito.

Ranar Alhamis 26 ga watan Yuni shekarar 2008, rana ce da ta rubutu a cikin kundin rike tarihin kwakwalwar Hama Amadu da kuma mazauna unguwar Yantala Bas makwabta ga babban kotu kasa. An jingine Hama Amadu a gidan kaso, saboda kotun ta zargesa da sama da fadi da kudaden tallafi ga kahohin watsa labarai da gwamnati ta bayar a shekarar 2001 lokacin yana shugaban gwamnati. Kamar yadda jaridar le Republicain ta rubuto.

Jaridar la Roue da l'histoire ta rubuto cewa yanzu da shugaban jam'iyar MNSDA Nassara yake a kurkuku sai ya ya? Wasu majiyoyin labarai masu kusantar jam'iyar su bayyana cewa, ana gobe ranar kai Hama a gaban kotun, ya mika shugabanci jam'iyar ga babban magatakardan jam'iyar Salisu Mahamadu Habi, to sai dai kuma ba san abinda dokokin jam'iyar suka ce ba lokacin da shugaban jam'iyar baya nan. Wannan harakar kudaden kahohin watsa labarai ta kara munanta ajajjiyar dake tsakanin magoya bayan Hama Amadu da kuma faraminista Seini Umaru, wanda tun lokacin da Hama ya fara karbar kira a gaban kotu magoya bayan Hama suke neman faraministan da ya yi murabus, to sai dai abin ya ci tur har suna ganinsa a matsayin wanda bai san ciwon kansa ba.

A nata bangare jaridar le Democrate ta zakulo da maganar da Hama Amadu ya yi a lokacin da ya kirai taron manema labarai a gidansa, wato cewa, idan aka kamasa hanya zata magana. Gaskiya ne birnin Yamai yana kumshe da dumbi jama'a magoya bayan jam'iyar MNSD Nassara, wadanda Hama yake gani tamkar jama'arsa ce. To, amma da yake gwamnati ta zuba jami'an tsaro ko ina, kuma ta bukaci gaskiya ta bayyana ko ina take, hanyar bata yi Magana ba. Birnin na Yamai da ake ganin tamkar gidan MNSD Nassara ne, ba hakan ba ne, saboda a cikin Yamai din ma jam'iyar ta samu rabuwar kawuna kamar yadda ta samu barakar a sauran rassanta dake cikin kasa.

Jaridar ta le Democrate ta fassara cewa, hanyar bata yi Magana ba kamar yadda Hama Amadu da sauran yan amshinsa suka yi fata, saboda mutane sun gaji da haihuwa rana na kashewa, suna gwagwarmaya saboda kyautata rayuwar wasu, a yayinda su tasu rayuwar sai kara lalacewa take. Hanyar ba zata Magana ba, saboda magoya bayan Hama su razana sosai, suna gudun kar su ce kala abin ya fado a kansu. Hanyar bata Magana, saboda yanzu kowa ya san mahimmanci demokaradiya a cikin kasar.

Wane ne zaya jagorancin jam'iyar MNSD Nassara bayan Hama Amadu? Kalmar tambayar da jaridar le Canar Déchainé ta yi kenan. Amshar wannan tambaya ta zamanto tamkar cacar kale-kale, wato akwai tabbatatu, akwai kuma wadanda ake shakku a kansu. Idan jam'iyar MNSD Nassara kungiyar farar hula ce mai zaman kanta to da Salisu Mahamadu Habi ne ya cancanta. To, amma da yake siyasa ce, wadda a cikinta ba a kiyayewa da komai akwai matsala. A cikin hasashen neman gaskiya, wato wanda za ya canji Hama Amadu, ta kan yi yuwa ya zamanto wani shugaban reshen jam'iyar ne na wata jaha, kamar Seini Umuru shugaban jam'iyar reshen Tilliberi ko Ali Sabo shugaban jam'iyar reshen Maradi. Akwai kuma wani shugaban reshen jam'iyar wanda aka yawaita maganarsa a cikin jaridu, wato Ibrahim Fukuri na reshen Diffa kuma makusanci shugaban kasa kana kuma ga ministan cikin gida na yanzu Albade Abuba shi ma ana ganin kamar za'a yi da shi. Bayan haka akwai wasu jigogi biyu dake ketare, wato tsohon faraminista Maman Umaru da kuma tsohon faraminista Amadu Bubakar Cise wadanda ke iya dawowa gida su nemi wannan matsayi. Kamar yadda jaridar le Canard Déchainé ta ruwaito.

Akwai alamun kamuwa daga curutukan hikimar kimiyya dake boye ga al'ummar birnin Arlit http://www.alternativeniger.org/spip.php?article170 http://www.alternativeniger.org/spip.php?article170 2006-05-08T18:40:00Z text/html ha Hassane Boukar Labarun Nijar Kamar dai yadda kungiya mai zaman kanta (ONG Aghir In'Man) ta bayyanawa ministan makamashin da ma'adanan kasa na jamhuriyar Nijar, a wata ziyara da ya kai a ma'aikatar tonon karfen uraniom ranar 17 ga watan fabrairu na shekarar 2006, cewa bayyanar wasu cututuka kamar su « canser » da kuma mutuwar wasu daga cikin ma'aikata da kuma tsafin ma'aikatan ma'aikatar tonon karfen uraniom dake Arlit, yana da alaka ne da kimiya ko hikimar gano curutukan dake boye da kuma matsalar kiyon lafiyar jama'a (...) - Labarun Nijar
Kamar dai yadda kungiya mai zaman kanta (ONG Aghir In'Man) ta bayyanawa ministan makamashin da ma'adanan kasa na jamhuriyar Nijar, a wata ziyara da ya kai a ma'aikatar tonon karfen uraniom ranar 17 ga watan fabrairu na shekarar 2006, cewa bayyanar wasu cututuka kamar su « canser » da kuma mutuwar wasu daga cikin ma'aikata da kuma tsafin ma'aikatan ma'aikatar tonon karfen uraniom dake Arlit, yana da alaka ne da kimiya ko hikimar gano curutukan dake boye da kuma matsalar kiyon lafiyar jama'a da dabbobin wannan karkara.
A gaban ire iren wadannan matsaloli da suka shafi rayuwar al'ummar da kuma mahalin wannan yanki, kungiyar ta Aghir In'Man bata zauna hannu yofi ba.
Yau tsawon shekara daya kenan da kungiyar take gwagwarmaya, domin ta jayo hankalin magabatan da kuma al'ummar kasar tare da na kasashen ketare a kan rayuwar al'ummar karkarar Arlit dake karkashin hatsari da kamuwa da curutukan hikimar kimiyya dake boye dalilin karfen uraniom da ake tonowa a wannan karkara.
Kungiyar dai ta kara bayyanawa ministan da cewa yada kayayyakin kimiyya ko hikimar curutukan boye iri iri a fadin kasar, musamman a cikin gidajen birnin Arlit, wata babbar matsala ce dake iya kawo wani cikas ga rayuwar dan adam da kuma mahali. Wannan kiran gaugawa da kungiyar keyi, ya zo daidai da lokacin da ake kokarin kafa wasu ma'aikatun tonon karfen uraniom da kuma wasu cibiyoyi.
Wannan sabuwar cibiyar, mallakar Somaïr, wace kuma za'a budawa a cikin wannan shekara, za'a kashe a kalla bishiyar itatuwa dari 2 domin share gurin kafa wannan cibiyar, kamar dai yadda kungiyar ta jadada. Bayan wasu munannan sakamako, tonon karfen uraniom din yake zayo mutane da dama masu neman aiki a jahar ta Arlit, abinda kuma ya kawo cinkoson mutane a wannan karkara, tare da kuma amfani da yawan itatuwan kuna da nauyinsu yakai ton dubu 27 a kowace shekara.
Tsawon wasu shekaru 10 da suka gabata, mutanen birnin Arlit na nemo itatuwan kuna ne a tazarar kilo meta 10 (10 km) da garin, yau ko sai suyi tafiyar kilo meta dari ko fiye da haka, kafin su samo itatuwan kuna.
Kungiyar dai ta Aghir In'Man ta na fargaba sosai da irin yadda ta gano da cewa, dajujukan kiyon dabboni sun kadanta, ko kuma ace ma babu su. Duk kuma abinda ya faru, ba wani dake da hannu dumu dumu a ciki, il'la hukumar nan ta kasar Faransa, cewa da Arewa dake shugabanci tonon karfen uraniom a jamhuriyar Nijar, wace ke da ma'aikatun biyu a karkara da suka hada da Cominak da Somaïr.
Hukumar dai, bata kiyayewa ba, bata kuma kawo kariya ga al'ummar karkarar ba, daga kamuwa ga curutukan kimiyya dake boye. Ma'aikatar bincike da kuma ganuwa da inganci ruwan da Somaïr ke amfani da su Algade, ta tabbattar da cewa, a watan Satumba na shekarar 2004 akwai wani babban makin curutukan kimiyya dake boye a cikin ruwan da ake amfani da su, a arewacin wannan karkara. _Kana kuma a fitowar sa ta ranar 26 ga watan Afrilu na shekarar 2005, jaridar le monde ta kasar Faransa ta bayyana cewa, sakamakon bincikken ruwan karkarar ta Arlit da ankai ya nuna cewa, akwai nau'in curutukan 2 da suka hada da Alpha da kuma Beta da suka zarce daga ka'idodin kungiyar kiyon lafiya ta duniya.
Ta hanyar irin wadannan labarai, da kuma jan kokarin kungiyar Aghir In'Man, wasu kungiyotin kasashen turai musamman SHERPA da kuma kommiti bincike da watsa labarai mai zaman kan sa a kan curutukan boye, suka bada damar ganuwa da cewa, Arewa ta kaucewa hanyoyi da matakan da ya kamata a dauka domin kare al'ummar daga curutukan boye.
Duk irin wadannan matsalolin rayuwa da al'ummar da kuma mahalin ke fuskanta, boye suke, ba a bayyane ba, ga al'ummar kasar.
Kahohin watsa labarai, ba su bada karfi ba, a kan irin wadannan labarai, kuma kadannan ne daga cikin kungiyoyi masu zaman kansu, suke bada nasu jan kokakari a game da irin gwagwarmayar da kungiyar ta Aghir In'Man ta sa a gabanta.
Wani abin kunkumi da ban takaici shine, wannan abu na faruwa ne a cikin kasar da yau kusan shekaru 5 kenan da aka gano da cewa, fiye da yara dari 4 ne suka nakasa, dalilin wasu ruwa da sun ka sha, da kampanin samarda ruwan sha a kasar Nijar SNE wace yau take a hannun VIVENDI WATER, ya sayar a garin Tsibiri Maradi , wasu daga cikin wadannan yara, sun gurgunta har il'la masha Allahu.
Ganin sakaci da kuma rishin yin wani yunkuri da zai kare al'ummar da mahali daga barnar Arewa, ya sa kungiyar ta Aghir In'Man ta nemi ministan makamashin da ma'adanan kasa, da ya kula da kuma maida himma domin kawo kariya ga mahali da Arewa ke niyar nakasarwa a dalilin tonon karfen uraniom. A cewar dai kungiyar, idan Arewa ta tsuduma rayuwar kusan mutane dubu 80 dake zaune a wannan yanki cikin wani halin kaka ni kai, to ba komai ba ne, il'la kawai saboda gwamnatin Nijar na alfahari ne da wasu yan kudade da basu taka kara suka karya ba, a karkashin kasuwanci wannan karfen uraniom da ake tonowa a kasar.

Abba Hassan
Matsalar kananan yan kasuwa http://www.alternativeniger.org/spip.php?article169 http://www.alternativeniger.org/spip.php?article169 2006-05-08T18:35:00Z text/html ha Labarun Nijar Lokacin da dubun dubatar yan kasa suka fito a kan titunan birnin Yamai, tsawon wasu makonni, domin su nuna rishin amincewar su ga tsadar rayuwa da suka tsinci kansu a ciki. A yayin da mahukuntan Nijar sun kai kunnuwan uwar shegiya ga matsalar tsadar cimaka, su kuma manya yan kasuwa sun tankware kanana.
A karshe wasu daga cikin makarabban kungiyoyin fararen fula suka rumtse idon, sunka sa hannu tare da gwamnatin a kan wata yarjejeniyar banza, a yayin da kuma fiye da million 7 na al'ummar (...) - Labarun Nijar
Lokacin da dubun dubatar yan kasa suka fito a kan titunan birnin Yamai, tsawon wasu makonni, domin su nuna rishin amincewar su ga tsadar rayuwa da suka tsinci kansu a ciki. A yayin da mahukuntan Nijar sun kai kunnuwan uwar shegiya ga matsalar tsadar cimaka, su kuma manya yan kasuwa sun tankware kanana.

A karshe wasu daga cikin makarabban kungiyoyin fararen fula suka rumtse idon, sunka sa hannu tare da gwamnatin a kan wata yarjejeniyar banza, a yayin da kuma fiye da million 7 na al'ummar kasar ke fama da talauci da fatara, su kuma a na su bangare yan kasuwa suna cikin zullumin rishin abukan cinikayya.
A lokacin nan ne muka tarda wani karamin dan kasuwa mai suna Insa a zaune, fuskar sa a turnike, yayi tagumi, ya na zullumi da tunanin, inda zaya fito da tsabar kudi jika dari 3 da tamanin (80) kirar CFA, da ya kamata ya zubawa Alhaji, nan zuwa sabkowar ruwan damana.
Insa, daya daga cikin yan kasuwar dake saye da sayarwa, a kasuwar Complexe, da aka fi sani da sunan kasuwar hatsi birnin Yamai, kuma yau fiye da wata biyar (5) kenan, da ya dauko bashin buhunan hatsi gurin Alhaji, to amma har sakunan sun fara yoyewa bai sayar ba.
A cewar shi Insa, « A da kasuwancin hatsin da muke yana tafiya kamar yadda ya kamata, to amma a yanzu, harakar ta canza zanne, masaya ba karfin sayen sakuna, ma'ana dai ba su da kudi ». Irin wadannan yan kasuwa, suna da dama a kasuwune daban daban, wadanda suka tsunduma cikin irin wannan hali.
Kasuwar hatsin dake kusan cibiyar yada al'adu da galgajiya ta kasa Umaru Ganda (CCOG), itace babbar kasuwar kasuwanci cimaka iri iri, kamar su hatsi, masara, dawa, wake da dai sauransu.
A cewar Alhaji Sumaila, daya daga cikin yan kasuwar dake sana'a a kasuwar hatsi, (idan kaga shagunan mu makil da cimaka, to wannan lokaci, mu, muna fargaba sosai da shi, ma'ana dai yana nuna muna cewa ba kasuwa). A na iya gane wannan lisafi a cikin sauki, ma'ana hawan farashen cimaka a kasuwar abu ne da ake ganewa, ta bangaren yawan masu zowa sayen cimakar, ga shi kuma a wannan lokaci da muke ciki ba masayan. Kana kuma za'a gano da rishi masayan a duk lokacin da aka gano da cewa, masu sayen tiya tiya ne suka yawaita a kasuwar. Alhaji Sumaila ya kara da cewa, yanzu kai, ta kare a gare mu, sai dai mu koma kauye da zama, tunda kasuwanci ya tsaya.
Kamar yadda hukumar kasa mai bada sanarwar farashen cimaka a kasuwunen kasar ta bayyana (SAP) za'a iya gano da cewa, akwai hawa hawan farashen cimaka a kasuwunen kasar, musamman a kan hatsi da dawa, wadanda kudin su, suka karu da kashi 4 cikin dari (4 %) a watan fabrairu .
Kamar dai yadda Yunusa ya shaida muna da cewa, yau farashen saku hatsi mai nauyin kilo dari, ya kai jika 15 a kasuwar hatsi birnin Yamai. Sanarwar SAP din ta bayyana cewa, farashen saku wake mai nauyin kilo dari ya kai jika 19 a kasuwa, farasjen ya karu da kashi 8 cikin dari (8%) tun a watan janairu.
Wannan hawa- hawan farashen sauran cimaka yake iya zayo karuwar farashen wasu daga cikin cimakokin da ake samu da rahusa. Hakan kuma yake zakulu fusantar masu amfani da ire iren wannan cimaka, kamar dai yadda, Afisa wata mata, mai tuyar kosai, take mamaki da kuma cewa, « Mu fa ba mugane komai ba a cikin wannan haraka, a bara anyi zangazangar yaki da tsadar rayuwa a kasa, saidai har yanzu komai bai canza ba, cimakar sai kara kudi take ».
A yanzu haka a kan dala dari da ashirin nake sayo tiyar wake daya, butar man kwalanshe a dala dari da sittin, bada wasu kayayyaki hadayya da nike amfani da su ba, dan in toya kosai ».
Hawa- hawan farashen a kan cimakokin da yan kasa suka fi yawan amfani da su da suka hada da hatsi, masara da shinkafa , ya zamanto bako ne ga yan kasa, farashen hatsin ya karu da kashi 4 cikin dari (4%) a yayin da kuma ita shinkafar da ake shigowa da ita, farashen na ta ya karu da kashi 6 cikin dari (6%).
Tsadar cimakar da wasu kayan masarufi, ya sa wasu daga cikin yan kasuwar sun talauce,kamar yadda mu ka samu malam Samuel Subu wani dan kasuwanci shinkafa da kayan masarufi, yayi tagumi, ba ma su saye. Ya kuma bayyana muna da cewa, tunda na kara farashe a kan kayayyaki na, kasuwanci ya tsaya, dalili kuwa shine mutane sun saba da arha.
Hawan TVA a kan sauran kayayyakin masarufi, shine ya kawo hawa-hawan farashen cimakar, wanda hakan ya sa , su kuma manyan yan kasuwa suke cin kajin su ba babbaka a doron kananan yan kasuwa.
Hakan kuma ya sa, yan kasuwar sunyi rishi masaya da dama, kamar yadda Samuel ya jadada muna da cewa, yau, ya rasha kashi 3 daga cikin kashi 4 mutanen dake sayen cimaka da kayayyakin masarufi a gurin sa.
Tun a wannan lokaci, kasuwancin sai ja da baya yake, da kuma ya gano ba ci gaba ga sayarda shinkafa da wasu kayayyakin masarufi sana'ar sa ta yau da kullum, Samuel ya sake sana'a. Yake sayarda kayayyakin marmari , dagin su (coca cola) , nonon campani da yake daukowa bashi a campanonin. To, saidai wannan kasuwanci, ba zai biya ma sa bukatun sa ba, kamar yadda ya saba.
Da ganin sa malam Abubakar wani mai shagon sayarda kayayyakin marmari, shi kai, ya na cikin sukuni fiye da Samuel, ya kuma nuna muna cewa, « A yanzu fa harakokin lafiya lau ne, tunda aka kara farashen kayayyakin masarufi, a da dai ina sayen saku sukari a jika 16, yanzu ko da farashe ya karu muna sayo saku a jika 20, dan haka, ni ma dole ne, ni kara farashen kilo sukari, yanzu kuma kari yakai kashi 70 cikin dari (70%), ba kamar shekarar bara ba.
To, amma duk da haka, mutane na zowa su saya, saidai kananan yan kasuwa, su kai suna kuka da mu.
A cewar wasu kanana yan kasuwa, harakar kasuwanci a jamhuriyar, akwai matsala, yanzu kai saidai suyi murabus,kamar yadda Samuel dan asalin Fada N'gurma cikin kasar Burkina Faso ya jadada muna.
Babbar matsalar, shine wasu daga cikin yan kasuwar, basu da ma kudin shiga motar dawayya a kauyuyukan su, kamar yadda wani daga cikin yan kasuwar ya bayyana muna.
A yanzu haka dai Samuel ya shiga neman aikin kowace ta samu, kofa kofa yana bidar aikin yi, ko boyi, ko tsaron gida, da dai sauransu.
A cewar shi Samuel din, dan shekaru talatin da haihuwa, dakyar da lahaula walakoti yake samu abinda suka kore yawun bakinsu a rana daya, sanin kowane, ciyar da gida a birnin Yamai , ba karamin aiki ba ne, gashi kuma, shi Samuel din bayada karfi , Ya kuma jadada muna da cewa yanzu haka shi da iyalin sa saida suka samu daidaito rage yawan cimakar da suke amfani da ita a rana daya, ya kuma gaskanta cewa, in mutun ba yada komai, to dole ne ya wahala, aiki baya samuwa a birnin ya.

Saidu Jibril
Gwamnatin Nijar ta ba wasu talakawan kasa wa'adin mako 2 su cire dakunan su daga inda suke zaune http://www.alternativeniger.org/spip.php?article168 http://www.alternativeniger.org/spip.php?article168 2006-05-08T18:30:00Z text/html ha Souleymane Maâzou Labarun Nijar «Dakunan cawa a kauye aka sansu, ba a birnin ba, dan haka ba a bukatar ganin su a birnin Yamai»
Tsawon shekaru 10 kenan da aka soma gani irin wadannan unguwane yan rabana ka wadata mu, cewa, da share ka zauna a kewayen birnin Yamai. Wadannan unguwane dai an fi samu su ne a kewaye da kuma cikin yankin bishiyoyin milian nan da ake kira « ceinture verte » da faransanci, wani guri ne da aka shuka itatuwa tun a shekarar 1965 domin kare birnin Yamai daga iska.
«Ku cire bukkokin ku nan da (...) - Labarun Nijar

«Dakunan cawa a kauye aka sansu, ba a birnin ba, dan haka ba a bukatar ganin su a birnin Yamai»

Tsawon shekaru 10 kenan da aka soma gani irin wadannan unguwane yan rabana ka wadata mu, cewa, da share ka zauna a kewayen birnin Yamai. Wadannan unguwane dai an fi samu su ne a kewaye da kuma cikin yankin bishiyoyin milian nan da ake kira « ceinture verte » da faransanci, wani guri ne da aka shuka itatuwa tun a shekarar 1965 domin kare birnin Yamai daga iska.

«Ku cire bukkokin ku nan da kwanakin mako biyu»,wannan furuci ne ko kuma muce niyar da gwamnati ta dauka a kan talakawan kasa, dake zaune a cikin unguwune share ka zauna dake birnin yamai. Babban buri gwamnatin shine birnin Yamai ya kasance ba bukka. Tun lokacin da gwamnati ta baiwa wadannan bayi Allah wannan wa'adi, ba kwana, ba kwonciyar hankali ga kuma yawan tunani a kan wannan niya da mahukuntan suka dauka a kan su.
“Idan suka kore mu daga wannan guri, to, ina zamu shiga”, cewar malam Musa wani mazauni a unguwar. “Ya kamata su magabatan su gane da cewa, idan muna da mashiga, to, da ba za mu zo, mu zauna a cikin shara da dauda da datti ba, ku diba a bayan daki na, wannan jibji ne fa, shara ce da mutanen birnin ke zubdawa a nan, yau ko shekaru na 13 a wannan gurin, dole ne nayi hankuri da ikon Allah.”
Tun a lokacin da gwamnan birnin Yamai Jules Ouguet ya kai wata ziyara a unguwar Golf, daya daga cikin unguwunen share ka zaunan dake birnin Yamai, bayanda wata wutar gobara ta ranar 11 ga watan Afrilu ta haifar da marasa makwani da dama da kuma rishin dukiya da dama, ake kyautata zaton cewa talakawan, sun tabbattar da cewa, irin wannan sakamako daga bangaren gwamnati zaya faruwa a gaba.
Tunda, tun a wannan lokaci ne Jules Ougues yayi furucu kamar haka : «Ya kamata gwamnati ta tada duk talakawan da ke zaune a cikin wadannan unguwune, kana ta ba su wani guri can nesa ga birnin». A gaban jama'ar ne, shugaban hukumar mashawarta birnin Yamai Abuba Ganda ya bayyana cewa, lokacin da gwamnati tayi zaman bada wuraren zama kyauta, ya wuce, maganar da shi ma Jules Ouguet ya tabbattar mu su, a lokacin ziyarar da yakai a gun mazauna share kazauna, ya kuma kara da cewa, dakunan cawa, kauye anka sansu, ba a birni ba. Dan haka ya kamata kowa yayi kokarin ginin mazaunar sa, amma kuma kada a manta da cewa, akwai ka'ida da ya kamata a kiyaye da ita.
Wannan furuci dai, bai bi a saman kunnuwan kurame ba, a kai tsaye wani da ya rasa aikin sa kuma ya zabi mazauna a gurin, malam Abass, ya mayar da martani da cewa :« Mu ma dake zaune a nan rishi ne ya kai mu a cikin wannan hali, kuma ba wanda bai bukatar rayuwa a cikin yalwantacen gida, to amma da ta kasance ba kowa ke da karfin hakan ba, dole ne a sha ta yadda aka dama ta ».
Bukatar mutanen ba komai ba ne il'la kawai a barsu, su ci gaba da rayuwar su a gurin.To duk da haka, a na ganin cewa har yanzu hali hau ila'a, da talawan suka shiga ciki, bai kawo karshen sa ba, tunda wa'adin da gwamnati ta bayarma talawan ya kawo karshen sa.
Bayanda talakawan sun kai kuka sun kai kururuwa, domin magabatan su ji su, kuma su gane matsyin su na yan kasa wadanda ba su da komai, kuma suke jadada cewa, nan fa inda suke, sun fi kusanta da birnin, wanda haka zaya ba su damar shige da fice domin su samu abinda za su ci su sha.
A cewar wani daga cikin wadanda dokar ta magabatan ta hau kan sa, cewa ya yi,« lalle akwai Allah, to, amma ya kamata magabatan su san cewa, mu ma mun san barnar wutar gobara, kuma ba mai hankalin da ke kunnawa dakin sa wuta, kenan abu ne da ya fito daga sarkin kowa. Idan kana cikin dakin cawa, Allah kadai ne mai kare ka ».
Mafi yawan daga cikin wadannan bayin Allah mutanen karkara ne, kuma ma su rinjaye daga cikin su, sun fito ne daga jahar Filinge. Sun ka kama wuraren a matsayin wucin gadi, yau ko da shekaru 11 kenan da wasu daga cikin su, suke zaune a wadannan wurare.
Tsawon wadannan shekaru, wadansu daga cikin su, sun dawai a kauyuyukan su, wadansu ko ba su iya dauriya da juriyar wahalar zaman kauye, suke sana'o-in su na saye da sayarwa, ayukan gida, da kuma lebranci birnin Yamai domin su samu abinda suka korewa bakin su yawu.
A cikin wannan jama'a, akwai yan birni da suke zaman kashin wando, ba aikin yi, ga kuma matsala, da tsadar kudin haya a birnin Yamai, abubuwan da suka sa, suka je suka nemi mafaka a share ka zaunan, kai har ma akwai yan kasashen waje a cikin wadannan bayin Allah, kamar yan kasar Mali da Benin.
A karshen kowane wata, mazauna wadannan unguwune suke biyan kudin CFA jika daya ga mamallakin gonar da suke zaune a ciki. Idan kuma aka waigaya baya, da tsawon shekaru 15 da suka gabata, wasu bukkoki kadan ne a wannan unguwar ta share ka zauna Golf, yau ko an washe gari da kusan irin wadannan unguwunen yan rabana ka wadata mu, 10 a kewayen birnin Yamai, wadanda kowace unguwa daga cikin su, ta kumshi a kala ba a kasara ba, mutane dari 2.
Dalili da ke kawo yawan wutar gobara a cikin irin wadannan unguwani shine dukan dakunan anyi su da cawa da zanaku da kuma katako. A ranar juma'a 24 ga watan Maris da ya gabata, wata wutar gobara ta tashi cikin irin wadannan unguwane dake dab da « ceinture verte », wutar gobarar tayi sanadiyar mutuwar wata tsofuwa da yan tawaye 2 da kuma dumbi kayayaki da dabbobi.
Babban abinda wadannan talakawar ke fargaba da shi, shine cewa, su fa suna da yara yan makaranta, to, idan mahukuntan suka koresu daga wannan gurin, ina zasu kai su, kuma yaya ne yaransu zasu zo makaranta, tunda ba wani a cikin su dake da karfin biyama yaron sa kudin taxi a kowace safiya.

Suleiman Maazu
Matsalar karamcin abinci, wani asirin Kasa http://www.alternativeniger.org/spip.php?article165 http://www.alternativeniger.org/spip.php?article165 2006-05-04T09:31:20Z text/html ha Labarun Nijar Hukumomin kasar Nijar sun yanke shawarar haramtawa duk wata kafar yada labarai ta waje dake da niyyar gudanar da rahoto a kan zance karamcin abinci shigowa cikin kasar. Tuni ma tashar gidan talabijin ta BBC ta hadu da fushin hukumomin akan wannan zancen, domin kuwa an tuso keyar Olma Gerin na BBC da kuma wadansu abokannin aikinsa zuwa Niamey, bayan da suka watsa rahotonsu na farko a kan yara kanana masu fama da tamowa, rahoton da suka dauka a cikin wata cibiyar kula da yara masu fama da (...) - Labarun Nijar
Hukumomin kasar Nijar sun yanke shawarar haramtawa duk wata kafar yada labarai ta waje dake da niyyar gudanar da rahoto a kan zance karamcin abinci shigowa cikin kasar. Tuni ma tashar gidan talabijin ta BBC ta hadu da fushin hukumomin akan wannan zancen, domin kuwa an tuso keyar Olma Gerin na BBC da kuma wadansu abokannin aikinsa zuwa Niamey, bayan da suka watsa rahotonsu na farko a kan yara kanana masu fama da tamowa, rahoton da suka dauka a cikin wata cibiyar kula da yara masu fama da yinwa da kungiyar ''Reporters Sans Frontières'' ta girka a garin Maradi. Domin kara jaddada hakan gwamnati ta kwace takardar izinin shigowa da kuma damar gudanar da aiki da ta baiwa wadannan ma'aikata na watsa labarai. Wannan dai yana mai tabbatarwa jama'a cewa duk wani zance da ya shafi yunwa ko karamcin abinci a Nijar, gwamnatin kasar ta sanya takukumi a kai ko kuma ta dauke shi a matsayin wani zance na siyasar kasa da bai kamata wani ya san abin da ake ciki ba.
Shi ma dai minista kana kakakin gwamnati, ya fito fili karara inda yake cewa zancen karamcin abinci, zance ne na musamman ga kasar, kana Nijar ba za ta zura ido wadansu na farfagandi a kansa ba domin samun kudaden da ba wanda ya san inda suke shiga.
A shekarar 2005 irin hakan ya faru akan wata yar jarida ta gidan radiyon RFI, inda har ma aka bayar da umurni ga yan jaridar gwamnati domin yin sharhi na musamman a kanta da kuma sauran yan jaridu na kasashen waje domin kawai sun yi aikinsu. To amma da yake karya fure ta ke ba ta yaya, a kwana a tashi yar jaridar da minista kakakin gwamnati Ben Omar ya karyata a bara, sai aka wayi gari yana mai yaba mata sanadiyyar cewar da ya yi shi da kansa, “a sauwake wata yar jarida ta gano cutar murar tsuntsaye'' ba tare da ya san cewa wannan yar jaridar ce ta kasance bara a wannan kasa ta kuma bayar da bayanai akan yunwa da ya karyata. A game da kwance izinin gudanar da aiki da ta yi wa wadannan yan jaridar, gwamnatin Nijar ta bayyana aniyarta ta boye labarai da kuma takurawa yan jarida. Ma'ana anan shi ne, ita ce take da izinin shaidawa al'umma halin da ake ciki tare da kaucewa watsa duk wani labari da zai bata mata da rayuwa.
Ga alama hukumomin kasar ta Nijar sun dauki wannan mataki na korar yan jaridar na BBC ne ba tare da sun yi tunaninin abin da zai haifar ba nan gaba. Ko ba komai wannan zai sa a surka sunan kasar ta Nijar a cikin jerin sunayen kasashen da suke tauye yancin aikin jarida. A hannu daya kuwa, fitowar da ministan da ake wa lakani da suna ''komai da ruwanka'' wato Ben Omar a cikin kafofin watsa labarai domin cin zarafin wadannan yan jarida, ya kara baiwa jama'a kwarin gwiwar neman su kallaci wannan rahoto da ake zance akai, rahoton da yanzu haka yake a kan layin gizo-gizo na tashar BBC ga duk wanda ke bukata. Wannan kuwa yana kara bata sunan kasar ne kawai a idanuwan sauran kasashe na duniya
Zancen samarwa matasa da ayyukan yi http://www.alternativeniger.org/spip.php?article163 http://www.alternativeniger.org/spip.php?article163 2006-05-04T09:28:46Z text/html ha Mamane Sani Adamou Labarun Nijar A lokacin taron koli na kungiyar tarayyar Afrika game da zancen samarar da ayyukan yi wanda ya gudana cikin watan satumbar 2004 a birnin Ouagadougou na kasar Burkina Faso, shuwagabannin na Afrika sun gano cewa tsarin siyasar da ake amfani da shi yau shekaru da dama kamar dai yadda kungiyoyin bayar da lamuna da kuma sauran kasashe masu karfin tattalin arziki na duniya suka shata, ya manta da zancen samarda ayyuka yi ga jama'a. Har ila yau game da irin illar dake tattare da wannan matsala ta (...) - Labarun Nijar
A lokacin taron koli na kungiyar tarayyar Afrika game da zancen samarar da ayyukan yi wanda ya gudana cikin watan satumbar 2004 a birnin Ouagadougou na kasar Burkina Faso, shuwagabannin na Afrika sun gano cewa tsarin siyasar da ake amfani da shi yau shekaru da dama kamar dai yadda kungiyoyin bayar da lamuna da kuma sauran kasashe masu karfin tattalin arziki na duniya suka shata, ya manta da zancen samarda ayyuka yi ga jama'a. Har ila yau game da irin illar dake tattare da wannan matsala ta rashin kyaukyawar siyasar samarda aikin yi ga al'umma da kuma mahimmanci dake ga yin hakan, bai kamata a ce zancen bai damu dukkannin shuwagabannin Afrika ba. A cikin hali na tabarbarewar tattalen arziki da kuma koma-baya ta fannin kyautata jin dadin rayuwar dan Adam, zancen rashin aikin yi ba wanda yafi shafa face matasa. A kasar Nijar alal misali rashin aikin yi ga matasa ya kai intaha, abin dake shafar hatta ma zancen ci gaban dan Adam

Wadansu alkalumman dake tabbatar da hakan

Idan har aka yi bitar alkalumman da ake da su za'a tarar da abubuwa kamar haka:
Rage yawan kudin albashin ma'aikata, wanda ke shafar irin bukatun da jama'a suke da su, kana a hannu daya ga asarar ayyukan yi da jama'a ke fuskanta. A cikin ma'aikatun gwamnati wadannan dalillai guda biyu sun faru a karkashin gwamnatin jamhuriya ta hudu, wato daga shekarar 1996 zuwa 1999 musamman ma a cikin watan maris na 1997, inda aka ragewa ma'aikata albashinsu da kimanin kashi 30 cikin 100, ga kuma rashin samun albashin a karshen kowa ne wata, abin da ya haddasa taruwar watanni da dama na albashin ma'aikata. Har ila yau akwai wadansu matsalolin da suka hada da daina biyan wasu kudaden alhaki daban-daban ga ma'aikata, daina karawa ma'aikaci girma, zancen bitar tsarin biyan albashi da kuma kin yi wa kundin tafiyar da ma'aikatan gwamnati gyaran fuska. Uwa uba an fuskanci sabuwar matsala ta tura ma'aikata zuwa ritayar gaugawa abin da nan take ya sa ma'aikata dubu biyu(200)0 suka rasa ayyukansu kuma akasarinsu malaman makaranta ne. A karkashin gwamnatin jamhuriya ta biyar kuwa lamurran sun kara tabarbarewa ne sanadiyyar hauhawar frashin kayan masarufi a kan kasuwa, alhali kuwa albashi bai kyautatu ba. Dora haraji na kimanin kashi 19 cikin dari akan kayayyakin masarufi irin na yau da kullum ya yi matukar shafuwar rayuwar jama'a.
Haka zalika an ga cewa akwai tafiyar hawainiya ta fannin daukar ma'aikata a wannan kasa. Da farko dai fannin ma'aikatun gwamnati wanda dama shi ne ya fi samarwa yan kasa da aiki yi, an wayi gari wannan fannin ya rage daukar ma'aikatan matuka. Hasali ma jimillar ma'aikatan kwadago na gwamnati ya rage daga ma'akata dubu 40 manya da kanana da ake da su a can cikin shekarun 1990 zuwa mutun dubu 35 da 701 a cikin shekara ta 2004. Soma aiki da wannan tsari ya sa gwamnatin ta dogara ga tsarin daukar ma'aikata da ake kiran yan barema da kuma masu aikin bautawa kasa wadanda albashinsu bai taka kara ya karya ba. A game da fannin ma'aikatu masu zaman kansu irin na zamani da ake da su cikin wannan kasa, ana iya cewa adadinsu bai kai inda ake bukata ba. Sakamakon wani bincike da hukumar samarwa yan kasa ayyukan yi a Nijar mai suna ANPE ta aiwatar cikin 2002, ya yi nuni da cewa akwai ma'aikatu da masana'antu ko kuma kamfanoni masu zaman kansu guda 2032 a cikin kasar kana akasarinsu a birnin Niamey suke. A cikin irin wadannan masana'antu akwai ma'aikata da yawansu ya kai dubu 36 da 960 kuma dubu 30 da 981 maza ne, sai kuma mata dubu 5 da 979.
Rashin aikin yi ba karamar matsala ba ce a nan, a zahirin gaskiya ma tsarin siyasar tsuke bakin aljihu da gwamnati ta runguma wanda ya tilasta mata sayarda hannayaen jarin kamfanoninta da dama, yana a matsayin ummulhaba'isar raguwar gurabobin aiki a Nijar. Wani bincike da wata cibiya mai suna Afrisat da kuma Dial ta gudanar game da matsalar samun aiki daga shekarar 2001 zuwa 2002 a cikin manyan biranen kasashe mambobin kungiyar UEMOA wanda kasar Guinée-Bissau kawai ce bai shafa ba, ya tabbatar da hakan. Rashin aiki ga matasan da suka haura shekaru 10 ya kai kashi 59 cikin dari a cikin manyan biranen wadannan kasashe. Wani rahoton kuma ya nuna cewa tsawon lokacin da mutum kann share ba tare da ya samu aikin yi ba a cikin wadannan kasahe ya kai na akalla watanni 41, kuma samun aikin ya kasance wani zance na zumunci da dangantaka. Yawan wadanda ke bi ta hanyar hukumomin samarda gurabobin aiki domin samun sa a cikin ka'ida bai wuce kashi 2 cikin dari ba a wadannan kasashe. A nan Nijar ANPE ta ce yawan mutanen da suka tuntube ta domin samun aiki a cikin shekara 2005 duka duka su dubu 18 ne. An bayyana cewa yawan matan dake gudanar da ayyuka a cikin wadannan birane ya kai kashi 46 bisa dari , to amma a Niamey an samu kashi 36 ne bisa dari.
Sashen masana'antu ko kuma ma'aikatun da ba su da cikakkaen tsari su ne suka fi samarwa da jama'a aikin yi a Nijar. Wannan sashe yana kuma taimakawa arzikin kasa da kimanin kashi 77 cikin dari game da kudaden shiga a cikin kowa ce shekara, tare kuma da taimakawa ta fannin biyan albashi ga ma'aikata da yawansa ya kai kashi 14 da digo biyar cikin dari.
A wani sakamakon bincike da ma'aikatar fasali ta kasa ta wallafa a cikin shekarar 1987, an gano cewa kimanin kashi 98 na gurabobin ayyuka da ba na fannin noma ba, sun dogara ne ga masana'antun da ba su da cikkaken tsari. A shekarar 1997 kuwa wani kiyasi ya nuna cewa akwai masana'antu matsakaita da yawansu ya kai dubu 135 inda a cikinsu ake yin ayyuka iri daban daban da yawansu ya kai 160, wadanda kuma ke samarda ayyuka ga mutane dubu 240 a fannin kamfanoni da masana'antun da ba su da cikakken tsarin tafiyar da su., yayinda a fannin tsararrun masana'antu da kamfanoni mutane dubu 58 da 273 kawai ne suke iya samun aiki a can. A game da jinsi kuwa, an gano cewa kimanin kashi 72 maza ne ke aikin, inda su kuma mata suke da kashi 27 da digo uku cikin dari. To amma kuma a game da hakan mata dake rayuwa a yankunan karkara sun fi samun damar yin aiki fiye da takwarorinsu dake rayuwa a cikin birane, domin kuwa matan na karkara suna da akalla kashi 83 bisa dari ne. Akwai wani abin lura anan, wato yadda wannan fanni da baya da cikakken tsari ba'a kasafai ake zancen albashi ba, inda yawan wadanda kesamun albashi akai-akai bai wuce kashi 5 da digo shida cikin dari ba. A nan fanni kamfanoni ko masana'antun da ba su da cikakken tsari na tafiyar da su a wannan kasa, ya kasance wani wuri ne da jama'a ke tunkara domin magance matsalar zaman kashe wando kawai.

Wadansu dalilai masu fayyacewa

A lokacin da ta samu yancin kanta, kasar Nijar yawan mutanen dake samun damar zuwa makarantun firamire bai wuce kashi 5 cikin dari ba, yayinda a makarantun sakandari ake da sifili da digo uku cikin dari wanda kuma shi ne kaso mafi kankanta a cikin nahiyar Afrika. A duk tsawon shekarun 1960 zuwa 1970 kasar ta fuskanci karamcin kwararrun ma'aikata. To amma sanadiyyar hauhawar Frashin makamashin uranium da kasar ta sama a cikin wannan lokaci, ya sa yawan masu bukatar aikin ya karo sosai. Wannan yana tabbatar da cewa sashen ilimi ,na kasar yana mai samun bunkasa ne amma a makare bayan an sami kwararrin malamai da suke da cikakken horo a akan aikinsu.
Da a ce a wannan lokaci kasa ba ta da wadansu hanyoyin samar da ayyukan yi ga al'ummarta, da lalle kuwa sha'anin aiki ya tsinci kansa a cikin wani mummunan hali da zai kai ga durkushewar masana'antun da ake da su a wancan lokacin, wadanda duk da haka daga bisani suka fada a cikin tarkon sayarda hannayen jari dake shimfide a kasar.
A wancan lokacin yawan ma'aikata ya kai mutum dubu 53 da 200( a cikinsu kuwa dubu 22 ma'aikatun gwamnati ne) a shekarar 1978 inda kuma nan take yawansu ya karu zuwa dubu 64 (dubu 27 da 100 ma'aikatan gwamnati) a shekarar 1981 sai kuma suka dawo mutum dubu 52 da 800 a shekarar 1984. Tun daga shekarar 1986 gwamnatin Nijar ta kawo sabon salo game da daukar ma'aikata ta hanyar cewa ba kowa ne dalibi ba ne ke da gurbin aiki kafin ya kammala karatunsa kamar dai yadda yake a da, alhali kuwa yawan dalibai dake kammala karatu sai karuwa yake a kowa ce shekara, abin da ya sa yawan masu neman aiki yake karuwa a kowa ce safiya ta Allah. A game da zancen aiki a cikin yankunan karkara kuwa, sanin kowa ne cewa kimanin kashi 80 cikin dari na al'ummar kasar sun dogara ne akan ayyuka irin na cikin karkara, kuma har ila yau a can ne ake da fannonin gudanar da ayyuka wadanda ba su da cikakken tsari da yawansu ya kai kashi 85 cikin dari na illahirin ayyukan da ake yi a can din. A can ma an samu cikas matuka wanda ya yi sanadiyyar raguwar gurabobin aiki, bayan soma aiwatar da tsarin nan na tsuke bakin aljihun gwamnati da kuma shimfida siyasar dake cewa dole ne a rage bayar da tallafi ga wadansu fannoni cikinsu kuwa har da sha'anin noma tun daga farkon shekara ta 1982.

Aiki da kuma yaki da fatara

Ba za'a taba cimma gurin kawar da talauci a cikin al'umma ba face an samarwa wannan al'ummar da ayyukan yi. Dangane da haka ne duk wani zance da ya shafi samarwa jama'a aikin yi yake bukatar shimfida siyasa tagari a game da tsarawa da kuma zana hanyoyin samun aiki ga jama'a, to amma anan mi muke gani face siyasa irin ta tsarin jari hujja, inda hatta zancen samun aiki yi ya rataya ne a wuyan kungiyoyi masu zaman kansu, da kamfanoni masu zaman kansu na cikin gida ko kuma na kasashen duniya. Wani minista na kasar Burkina Faso ya bayyana a lokacin wannan taro cewa, “Gwamnatocin kasashe su ne ke kirkiro dokoki tare da samo kudade, to amma wannan ba ya nufin cewa gwamnatoci kawai ne za su samarda gurabobin aiki ga jama'arsu'' Ministan ya ci gaba da cewa '' ya kamata a ce su ma mutanen Afrika sun mayarda hankali ta fannin bayar da tasu gudummuwa ta hanyar samarda kudi domin magance wannan matsala.“ Ma'ana lokaci ya yi da Afikrikawa za su nuna tasu bajinta wadda za ta kawo karshen dogaro da wadansu kasashe a koda yaushe.

To ko ina mafita ?

Ba zai taba yiyiwa ba a yi hasashen kyautatuwar lamurra nan gaba matukar dai ya kasance kasuwa ce kawai wata hanya ta saka jari, haka-zalika canza dangantakar al'umma ba zai iya yin wani katabus ba a irin wannan hali.
Alal misali a cikin shekaru 50 arzikin duniya ya rubanya har sau bakwai. A irin wannan hali ya kamata a ce gurin kasashen duniya na kowa ne talaka daya ya mallaki dalar Amurka daya a rana ya wuce hakan, yaki da talauci ba zai wadatar ba domin kuwa tsarin da aka dogara akan shi yana kara nisanta kasashe matalauta ne daga cimma burinsu.
A zahirn gaskiya kamata ya yi a ce an bullo da wani sabon shiri na ci gaban al'umma amma wanda ya dace da manufofin bunkasa tattalen arziki nagari wadanda kuma ke kula da matsalolin jama'a. Wannan shirin har ila yau dole ne ya kula da zumunci da kuma kaucewa yaudara da kuma yaki da duk wadansu manufofi dake nuna bambanci tsakanin al'ummar duniya, wanda ta haka kawai ne matasa za su iya samun aikin yi .

Zanga-zangar ranar 15 ga watan maris na shekara ta 2005 http://www.alternativeniger.org/spip.php?article164 http://www.alternativeniger.org/spip.php?article164 2006-05-04T09:28:38Z text/html ha Labarun Nijar Babbar zanga-zangar ranar 15 ga watan maris na shekarata 2005 ta kasance mai cike da guri da kuma fata nagari ga dubban al'ummar wannan kasa, wadanda suka fito domin yin tir da wani tsari da gwamnati ta nemi aiwatarwa, wanda kuma yake da matukar illa ga tattalen arziki da haddasa tsadar rayuwa. Shekara daya bayan shirya zanga-zangar, kowa ne darasi aka koya?
A dai dai lokacin da kamfanonin samarda ruwan sha da na makamashin wutar lantarki da yan kasuwa suke ci gaba cin karensu babu babbaka (...) - Labarun Nijar
Babbar zanga-zangar ranar 15 ga watan maris na shekarata 2005 ta kasance mai cike da guri da kuma fata nagari ga dubban al'ummar wannan kasa, wadanda suka fito domin yin tir da wani tsari da gwamnati ta nemi aiwatarwa, wanda kuma yake da matukar illa ga tattalen arziki da haddasa tsadar rayuwa. Shekara daya bayan shirya zanga-zangar, kowa ne darasi aka koya?

A dai dai lokacin da kamfanonin samarda ruwan sha da na makamashin wutar lantarki da yan kasuwa suke ci gaba cin karensu babu babbaka ta hanyar tsadada hajojinsu, su kuwa masu karamin karfi sun tsinci kansu ne a cikin wani halin rayuwa na wahala, yayin da su kuma yan majalisar dokoki na kasar suka tsarawa kansu doka mai kyautata makomarsu, firaminista ma haka-zalika illa kawai talaka da zai ci gaba da dandana kudarsa. A game da haka za'a iya cewa an shimfida wadansu munanan halaye guda uku dake cutar da jama'a; na daya kuwa shi ne nunawa jama'a cewa dole a darajjanta duk wadansu abubuwa da gmwamnatin kasar ta bullo da su, na biyu shi ne kowa ya kauda kaigame da irin siyasar da ake amfani da ita a kasar ko da kuwa tana cutarwa, na uku shi ne a yaki wannan doka mai neman kara tsunduma talaka cikin mawuyacin hali, abin da kuma shi ne al'umma ta zaba har ma ta shirya zanga-zangar ta ranar 15 ga watan na maris 2005.

Wani fata da bai kai ga samun galaba ba

Kamar dai mutum daya, haka al'umma ta fito a wannan rana domin yin watsi da wannan doka. Wannan kokowar ta ci nasara ne ba wai domin wadanda suka shirya ta sun kasance wasu gwarzaye ba, a'a domin kawai jama'a ta fito ne da guri da kuma manufa daya : Na daya kuma akwai zancen kasawar gwamnatin wa'adin farko na shugaba Tanja, wadda ta kasa cikawa yan kasa irin alkawullan da ta dauka masu lokacin yakin neman zabe. Na biyu kuma akwai zancen kin darajjanta dokokin kasa ta fannin bayar da kasuwa a cikin ma'aikatun gwamnati ba akan ka'ida ba ; wani abun kuwa da ya sa gwagwarmayar ta kai ga samun galaba ya hada har da fahimtar da manyan kungiyoyin kwadago na kasar suka yi kan cewa lokaci ya yi da za'a yi yaki da wannan doka ta kasafin kudin kasa na shekarar 2005 Dubban mutane sun karba kiran da aka yi masu a cikin titunan birnin Niamey domin nuna rashin amincewarsu kan wannan doka ta gwamnati.
Yau shekara daya bayan shirya zanga-zangar ko ana iya cewa tsadar rayuwa ta ragu a kasar nan ? A zahirin gaskiya amsar ita ce a'a, domin kuwa kowa ya tabbatar da cewa kayan masarufi frashinsu ya hau zuwa sama ne kawai. Amma watakila abin da ya fi daurewa jama'a kai anan shi ne ; yadda ake ganin cewa tamkar dai wasu daga cikin wadanda suka shiga gaba domin shirya zanga-zangar ta bara suna da alamar gazawa ko kuma sam sun shige cikin gungun wadanda ke tsara dokokin masu cutawa jama'a.

Sabin dabi'u da suka biyo bayan wannan zanga-zangar

A zahiri take cewa wasu daga cikin shuwagabannin da suka shirya bijirewa dokar a shekarar bara, a yau an wayi gari tare da ganin su cikin sha'anin tafiyarda mulkin kasar, tamkar dai manufofin wannan kokowar su ne samarmasu da wata malaba a cikin madafan iko. Har ila yau ana iya cewa wannan kokowar ta haifar da wasu sabbin jagora da suke da ra'yi irin na tsohon soja wanda a koda yaushe ake yaki yake daukar sojojin dake yakin a matsayin wadanda ba su da wata gwaninta ko bajinta a fagen fama tamkar irin wadda yake da ita lokacin da yake sanye da kaki. Wata hujjar fadin wannan magana kuwa shi ne yadda wasu daga cikin irin wadannan mutane suke shiga kafofin watsa labarai suna yin irin na magori wanda hausawa ke cewa wasa kanka da kanka, suna masu nuni da cewa duk wata gwagwarmaya da za'a yi matukar dai ba su ne suka tsara ta ba, to lalle ba za ta samu nasara ba.
Wannan dabi'a da suka runguma ta mayar da su tamkar su ne kawai shuwagabannin na kungiyoyin farar hula a wannan kasa, kuma duk wanda ya yi magana da sunan kungiyoyin farar hula idan har ba su ba ne to lalle kuwa ya kaucewa ka'ida.
Wannan dai wata shaida ce kan yadda suke neman kare martabarsu a idanuwan al'ummar kasar da suka yaudara, sakamakon yadda suka karkata manufofin wannan zanga-zanga a dai dai lokacin da take gaf da smun nasara, kana a yanzu sun zama neman kare manufofin gwamnatin ne ta hanyar yiwa duk wata gwagwarmaya da za'a shirya nan gaba zagon kasa.
Karkashin wata yarjejeniyar sulhu da wannan reshe na kungiyoyin farar hula na kasar dake kumshe da makwadaita ya sanyawa hannu domin dakatar da kokowar, an ga sabbin ma'aikata da suka kutsa kai domin kaddamar da wani gagarumin aiki na karbo harajin kasa da karfi tamkar dai su ne cikakkin ma'aikatan hukumar karbar haraji ta kasa. Ba shi kenan ba domin an samu wasu daga cikinsu sun kasance a cikin kwamitoci daban daban har ma da na rabon taimako abinci a lokacin yunwa.

Rigangantu zuwa kwasar garabasa

Watakila cikin rashin sani ko kuma rudanin da kalaman gwamnatin kasar suka haddasa masu, wadannan shuwagabanni na kungiyoyin farar hula sun rugumi tsari na a tafiyar da sha'anin gwamnati tare da su ba tare da sun yi la'akari da abin da zai biyo baya ba.
A ce yau shugaban gwamnati ya kebewa kansa wani romo amma irin wadannan mutanen ba ruwansu, a ci gaba gudanarda mummunan jagoranci a kasa ba su damu da hakan ba, su abin da ya dame su kawai, shi ne a tafiyar da kasa tare da su ba kumya ba tsoron Allah, domin kuwa su abin diniya kawai ya rufe masu ido.
Dangane da haka kirkiro wani kwamiti ko hukuma da za su shigewa, ko shirya taron karawa juna sani kadai ya damesu . To amma duk da haka ba za'a hadu a zama daya ba, domin kuwa cikakkun kungiyoyin farar hula irin wadanda suke yi domin ci gaban kasa kamar CDSCN, sun dukufa sosai ta fannin gwagwarmayar kwato hakkin jama'ar kasar, wanda dama yake wani gimshiki ne a shigarsu cikin waccan kokowar ta ranar 15 ga watan maris na shekarar 2005. Abinka da tarihi a kwana a tashi ranar 15 ga watan maris na wannan shekara 2006 ta zagayo, wato cikon shekara daya cur kenan, CDSCN da wadansu kungiyoyi da suka hada har da na malaman makaranta suka kira jama'ar kasar da su fito a shirya zanga zanga domin neman gwamnati ta kyautata tsarin bayar da ilimi a kasar, to amma me zai faru, sai aka ji wadancan kungiyoyi na makwadaita tsintsa sun shiga cikin kafofin watsa labarai suna yin kira ga jama'a da kada su fito wannan zanga-zangar.
A yau ba wai kawai kungiyar USTN ba da ta saba kauda kai game da shiga zanga zanga da ake tsarawa a Nijar, hatta ma sauran kungiyoyi guda biyu sun bi sahunta. To amma duk da haka sauran kungiyoyin malamai kamar su SNEN da kuma SNECS da na sauran ma'aikatan jami'a sun bayar da goyon bayansu ga wannan kokowar da ake yi. Su kuwa matasa, dalibai maza da mata sun nuna kishin kasa ta hanyar shiga wannan gwagwarmaya mai yin tir da Allah wadai da irin salon siyasar da ake amfani da shi a wannan kasa mai cutawa talaka. Sauran shuwagabannin kungiyoyi masu zaman kansu, da manyan kungiyoyin ma'aikatan kwadago sun kauda kai game da kokowar, irin wadannan yan amshin Shatar gwamnati, yan tumka da warwara, a yau kowa ya tabbatar ba su da wani ra'ayi na yin gwagwarmayar kare yancin dan Adam. Kenan me suke yi illa kawai wargaza duk wani tsari da zai kawowa talaka amfani a rayuwa da kuma ci gaba da yakar sauran takwarorinsu na kungiyoyin farar hular da suke da ra'ayin kyautata rayuwar al'umma. Irin wadannan mutane yau sun zama masu cutawa jama'a a cikin rigar kungiyoyin kare yancin dan Adam, alhali kuwa ba wannan aiki su ke yi ba a zahirin gaskiya sai dai kawai ci da gumin talaka. Kowa ya shaida cewa zanga-zangar da aka shirya ranar 15 ga watan maris na wannan shekara(2006) duk da yake mutane kalilanne suka fito, to amma ana iya cewa an samu galaba musamman idan aka yi la'akari da cewa akwai dubban dalibai da masana sha'anin ilimi da dai sauran jama'ar da suka fito a wannan rana, kuma abu ne mai wuya wani mutum ya iya takawa kungiyoyin da suka shirya zanga-zangar birki akan manufofinsu na kyautata sha'anin ilimi cikin wannan kasa ta Nijar.

Sule Aji
Ma'anar sabon yunkurin shugaban kasar Nijar http://www.alternativeniger.org/spip.php?article161 http://www.alternativeniger.org/spip.php?article161 2006-04-29T10:05:04Z text/html ha Mamane Sani Adamou Siyasa Duk masu lura da al'amurran siyasa na yau da kullum sun yi la'akari da canje-canjen da aka samu a dangataka tsakanin shugaban jamhuriya da mataimakinsa paraminista Hama Amadu. Ganin yanda tsawon shekaru biyar shugaba Tandja ya damka wa paraminista akalar gudanar da harakokin mulki, abin mamaki ne yau a ce shugaban gwamnati ya jahilci manufofin abokinsa. Har ma yan kallo na daukan cewa ai ba da bata lokaci za a kori Hama daga matsayinsa. A cikin wannan takarda za mu bincikin gaskiyar wannan (...) - Siyasa
Duk masu lura da al'amurran siyasa na yau da kullum sun yi la'akari da canje-canjen da aka samu a dangataka tsakanin shugaban jamhuriya da mataimakinsa paraminista Hama Amadu. Ganin yanda tsawon shekaru biyar shugaba Tandja ya damka wa paraminista akalar gudanar da harakokin mulki, abin mamaki ne yau a ce shugaban gwamnati ya jahilci manufofin abokinsa. Har ma yan kallo na daukan cewa ai ba da bata lokaci za a kori Hama daga matsayinsa. A cikin wannan takarda za mu bincikin gaskiyar wannan hasashe kana mu dubi halin cimin kasa da sauran dalilai da suka cilasta shugaban kasa canza salon jagorancinsa.

Alamar dagulewar aikin bariki

Shekara daya tak bayan kammala zaben da shugaba Tanja ya lashe, murna ta koma ciki. Daidai lokacin da kafofin watsa labarai na hukuma tare da magoya bayan gwamnati ke guda da ikirarin taka rawar gani ne abin mamaki ya faru.
Shugaban kasa ya soma da ganawa da jami'ai ma su aiki a sashen harakokin kudi, inda a fusace, ya kuma nuna matukar rishin jin dadinsa, game da irin yadda jami'an kasa ke tafiyar da ayukkan su. Ma'ana aikin da kusoshin bariki ke yi bai dace da ka'idojin tanadin dukiyar kasar ba ko miskala zaratin. Shugaban jamhuriya ya zarge su da karbar rashawa, cin hanci da sauran miyagun halaye. Wannan la'akari kuwa ya zo daidai da irin tsokaci da kuma furucin da yan adawar kasa sun ka sha yi tun shekaru biyar da suka gabata, cewa da, a na almabazaranci da kuma kashe mu raba da dukiyar kasa, ba a kan ka'ida ba.
Ganawa ta biyu shugaba Tanja da tawagar shi sun yi ta ne tare da sauran sassan ma'aikatun kasa. Sakatarori da daraktocin fadar ofisoshin ministoci su ma basu taka rawar gani ba. An gano cewa ma'aikatan gwamnati, ba su aiki tsakani da Allah, wato babu ladabi da hamzari kazalika ga rashin da'a a kan ayukkan da suka rataya a wuyan su. Wato wasu yan tsiraru sun maida dukiyar jama'a tasu sai kuma wanda ake damawa da shi. Hankan ya sa yanzu talaka mai wata bukata ko ya zo a wani ofishi domin magance matsalar da take damun shi, ba ya samu ma'aikatan a gurin, kowa ya kama gaban sa.
Wannan lamari na da alaka da tsarin daukar ma'aikatan sa-kai a bariki maimakon amfani da kwararru. Gurin gwamnati a nan shi ne ci-gaba da rage nauyin biyan albashi cikin kasafin kudi wanda ya hada da dakatar da daukar sabbin ma'aikata masu matsayi da kuma gaggauta tura wadansu ritaya. Wannan kuma umurni ne na Bankin duniya da Asusun bada lamani na kasashe.

Lamari mai laurin kai

Hakika wannan yunkuri na shugaban kasa Tandja Mahamadu ya zo a makare, dalili kuwa tun washe garin da ya dare karagar mulkin kasar, wato a shekarar 2000 ne shugaban kasar ya kamata ya yi irin wannan furuci. Ma'ana ya fito a gaban ma'aikatan kasar ya fayyace musu hanyar da yake bukata su bi.
Sai dai yau gashi tsawon shekaru shida (6) kenan da shugaban kasa da mukarubbansa ke cin karen su ba babbaka, suna alfahari da wai nasarorin da suka cimma a fannoni dabam-daban na rayuwa. Bugu da kari idan aka yi la'akari da cewa, akasarin jami'an da ake la'anta ko suka sun hito ne daga rukunin hadin gwiwar jam'iyyun siyasar da ke mulki a halin yanzu, kuma a cikin jam'iyyu da ke mulki ma ba ko wace jam'iyya ba ce ke da sukunin samu wani babban mukami illa kawai yan M N S D, jam'iyar da ta dora shugaban kasa a karagar mulki, ko kuma magoya bayan CDS, jam'iyar shugaban majalisar dokoki ta kasa, sai a yi mamakin kalaman shugaban kasa da paraminista.
Ayoyin tambaya a nan sune: yaya aka yi mutanen da kuka nada wato kuka baiwa mukamai a ce ba zaku iya ladabtar da su ba ? Shin wai mene ne dalilin bayyana wannan la'akari da ya saba ma furofagandar gwamnati? Me ya sa sai wannan lokaci? Dangane da bayanin da Paraminista yayi, cewar kudin da ke shigowa baitulmalin kasa, daga cinikayyar mu da ketare sai ja da baya suke. Abin nufi a nan shine jimillar dukiyar kasa tana raguwa daga shekara zuwa shakara.Kenan tsawon shekaru biyar (5) da suka gabata Nijar ba ta taka rawar gani ba a fannin tattalin arziki. Kuma kowa ya san Paraminisata ne ke da wuka da nama a wannan lokaci. Yau an wayi gari ya futa cewa ai babu nasarar da suka cimma. Lalle al'amrin na da daurin kai da ban kumya ainun.

Muhimman dalilai

Yau duk wanda ya yi la'akari zai gano cewa kasar Nijar na cikin mawuyacin hali. A shekarar bara an fuskanci bala'in yunwa wadda ta addabi fiye da mutum miliyan uku. Karewa da karau wannan shekara cutar murar tsuntsaye ta kunno kai inda take neman raunana cimmin mazauna karkara.
A fannin tattalin arziki har ila yau ba a cimma daidaito da asusun bada lamuni na kasashe ba (FMI). Idan kuma ana tune tun watan Disamba da ya gabata ne majalisar dokokin ta karbi tsarin kasafin kudi na sabuwar shekara. Yayin da yake nuna farin cikinsa dangane da karbar doka, ministan harakokin kudi yayi sharhi inda yake cewa, wannan doka ta kasafin kudi ta nada mahimmanci saboda a shekarar bana kudaden da ake samu bangaren talafin (ko taimako) daga ketare zasu ragu sosai. To, babbar matsalar itace, shekara da shekaru kasar Nijar ba ta taba wadata da taimakon isassun kudaden daga ketare ba. Dalili kenan da ake samun gibi wajen zartar da kasafin kudi. Yau masu bada tallafi sun bukaci gwamnati ta dogara da kanta wato da kokarin yan kasarta don gudanar da ayukkanta.Kenan dole ne Tandja ya karbi jagorancin ayyukan gwamnati. Matsalar dogaro da kai ba al'adar hukumar Nijar ba ce. Ma'ana manuhohin mu na siyasa sun sabawa aikata hakan. Sakamakon handama da awon gaba da dukiyar kasa da masu iko ke aikatawa shine mika akalar mulki a hannun ketare. Kazalika mahakunta kan yi amfani da duk wani tallafi da ya shigo daga ketare dan cin moriyar kansu. To yaya za a cimma gurin dakatar da aikata wadannan laifuka ba tare da an canza akidar siyasa ba?

Sabon salon mulkin malaka

Idan an nazarci tarihin siyasar Nijar za a yi la'akarin cewa alkibla daya mun ka dogara kanta, tun lokacin da mun ka samu yanci kai. Mun dogara ne da Faransa wace mu damka wa ragamar gina makomarmu. Dalili kenan da muka samu kammu cikin wani hali na kangi da danniya, kuma maimakon ace mu, habaka tattalin arzikin mu abin sai jada baya yake kulum.
A cikin wannan hali ne kuma kasashe masu hannu da shuni tare da bankin duniya da asusun tsara kudade na kasashe suka umurce mu zartar da wannan tsari na tsuke bakin aljihun gwamnati (PAS) wai mai gurin tada komadar tattalin arzikinmu. Wannan shiri tun shekara 1982 ne aka fara ayyana shi inda gwamnati ta dakata bada tallafi don kyautata rayuwar al'umma, musamman ma a kan al'amuran da suka shafi makarantun boko da kiyon lafiya, wadata jama'a da ingantattun ruwan sha da sauransu. Misali, yau iyayen yara su ke daukar nauyin sayen allo karatu, alli,da dai duk wani abu da dalibi (dan makaranta) ke bukata dan daukar darasi.
Kazalika wannan siyasar ita ce makasudin kirkiro rukunin malaman makaranta yan sakai wadanda gwamnati ke son su kai minzanin kashi tamanin cikin dari (80%) na adadin malaman makaranta nan da shekaru goma. A bangaren kiyon lafiya kuma, yau in baka mallaki jika hudu (4000 sefa) ba to zuwa asibiti tamkar yawon gani da ido ne domin babu halin samun magani. Dalili kuwa shine wadanda suke gadin kofar gidan likita, ba ma'aikatan kiyon lafiya ne ba, jandarma ne. Wato in kana da kudi za'a binciki lafiyar jikin ka, in ko ba haka ba to ka san abinda zai biyo baya.
Bugu da kari, tun wannan lokaci ne kuma ta soma zartar da tsarin sayar da kamfanonin malakar gwamnati, wadanda aka yi ma cinakin wulakanci. Akasarin saidaddin kampanonin yau sun mutu. Rashin karfin masana'antu, hakika babbar ila ce ga kasa. A cikin duniya babu kasar da ta yi tasiri wadda ba ta mallaki arzikin masana'antu ba. Yau fiye da shekaru ashirin na ayyana wannan shiri na tada komadar tattalin arziki har yanzu komadar bata tashi ba.
Abin da ya haifar da talauci da rashin aikin yi ga al'ummar kasa da rashin masana'antu kenan. Ashe babu halin shigowa da kudi. Sakamakon wannan shiri ne yau shugaban kasa ya yi la'akari da shi, amma ya na la'akari da shine ta hanyar cewa wai yan Nijar ba su son kasar su, bai yi la'akari da cewa wannan siyasar shi ce umal aba isar haifar da wannan rashin kuzari na yan Nijar.

Ina aka dosa?

Yunkurin shugaba Tandja wani salo ne na nuna ma duniya, musamman ma jami'an bankin duniya kokarin gwamnatinsa wajen gyara dukkan kurakurai da aka gano. A na gudanar da larwai don wai magance matsalar almabazzaranci amma ba za ladabtar da masu laifukka ba. Kazalika a na yin garanbawul na kusoshin bariki amma ba tare da tsige wadanda suka yi ayukkan assha daga mukamansu ba.
Idan kasashe masu hannu da shuni suka matsa lamba to sai a kame wani jami'i a gurfanar da shi gaban kotu. Hakan ta faru dangane da kudin shirya wasannin kasashe masu ma'amala da harshen faransanci « Francophonie ». A wani gefen kuma a kan cilasta masu laifin su biya kudin da suka handama. Misalin cimaka da kasashen ketare suka agaje mu da ita kuma magabata suka handame.
Da karshe a na shakuwa da jigogin jam'iyyun adawa, a kan tattauna da su wai don yin riga-kafin rikicin siyasa amma ba tare da kiyaye ka'idojin dimokaradiyya ba. Hakan ta faru dangane da matsalar soke wariya da banbanci wajen rarraba mukamai na aikin gwamnati inda aka bukaci shuwagabannin adawa ta majalisa su bada sunayen jami'an su da suke son a nada. Watakila ba a ware yan adawa ba amma an kauce ma ka'ida kuma ba a yi adalci ba. Bukatar ma'ikonta ita ce magance duk wata zanga-zanga da adawa za ta hadasa.
Wannan ilimbo zai dore kuwa? Ashe za mu iya cimma gurin ci gaba ba tare da an sake akidar siyasa ba?

A Karkata akalar mulki

Ya kamata yan Nijar su fahimci cewa manufofin mu na siyasa ne ke hadasa talauci, faduwar tattalin arzikin kasa, rishin tarbiya da duk wata matsala da ke addabar al'umma. Kenan idan aka ci gaba da rungumar wannan akida ba yadda za'a yi a shayo kan matsalolin mu na yau da kullum. Zancen rikici tsakanin paraminista da shugaba kasa bai taso ba. Yau, idan kana neman maras kishin kasa, ai cikin jerin shuwagabanin, da kuma kusoshin gwamnati, za ka same su. Su ne yan amsar shata, wato yan koren shanu na kasashen Yamma da mayan kamfanonin su, wadanda suka tsara wannan bakar siyasa ta yaudara, mai halaka talakawan kasa da kuma tabarbare arzikin kasa. Yau babban abin bakin ciki shi ne, rashin akidar ta kishin kasa da adalci ga akasarin jam'iyyun siyasa na Nijar. Galibinsu ma'abuta siyasar wai tada komadar tattalin arzikin ta bankin duniya da asusun bada lamani ne. Ita kau wannan siyasa ba siyasar ci-gaba ba ce.
Idan ana bukatar kubuta daga wannan kangi to dole sai an canja manufa.