Alternative Espaces Citoyens Niger http://www.alternativeniger.org/ ha SPIP - www.spip.net Fira da Musa Cangari Babban Magatakardan Kungiyar Alternative Espace Citoyen (AEC) Yamai http://www.alternativeniger.org/spip.php?article508 http://www.alternativeniger.org/spip.php?article508 2010-11-08T13:23:47Z text/html ha Labarun Nijar Shugaban kasar Cana Hu Jintao ya kai wata ziyar aikin kwana uku a kasar Faransa, daga ranar 4 zuwa 7 ga watan Nobamba na shekarar 2010. A karkashin wannan ziyar aiki, shugaban kasar Cana Hu Jintao da takwaransa na kasar Faransa Nikolas Sarkozi sun rattaba hannu a kan wasu yarjejeniyoyi na kwagila tsakanin kasashen biyu, wadanda suka ba Faransa damar samu tsabar kudin Amirka dala miliyan dubu 20 daidai da kudin Faransa (Yuro) miliyan dubu 14 ke nan. A cikin kwangilolin suka shiga tsakanin (...) - Labarun Nijar

Shugaban kasar Cana Hu Jintao ya kai wata ziyar aikin kwana uku a kasar Faransa, daga ranar 4 zuwa 7 ga watan Nobamba na shekarar 2010. A karkashin wannan ziyar aiki, shugaban kasar Cana Hu Jintao da takwaransa na kasar Faransa Nikolas Sarkozi sun rattaba hannu a kan wasu yarjejeniyoyi na kwagila tsakanin kasashen biyu, wadanda suka ba Faransa damar samu tsabar kudin Amirka dala miliyan dubu 20 daidai da kudin Faransa (Yuro) miliyan dubu 14 ke nan. A cikin kwangilolin suka shiga tsakanin kasashen biyu, akwai wadda ta shafi karfen Yuranium wanda kampanin Areva na kasar Faransa ke haka a cikin karkarar Arlit yakin Agadez Jamhuriyar Nijar. Kasar Cana da kasar Faransa, kasashe biyu ne dake huldar tattalen arziki da kasar Nijar musamman a kan abin da ya shafi ma'adannan kasa. To ko wadannan yarjejeniyoyi na iya taba tattalen arzikin kasar Nijar ? Me kuma yan kasar Nijar ke fargaba a ciki ? Ga nazarin da Malam Musa Cangari Babban Magatardan Kungiyar Alternative Espace Citoyen (AEC).

Malam Musa Cangari ya fara da cewa : tabbat duk abubuwan da suka wakana, sun shafi kasashen biyu, kuma sun shafi kasar Nijar. Dalilin da yasa suka shafi Nijar, shi ne, a cikin yarjejeniyoyin da suka sa hannu, akwai wadda ta shafi hakar karfen Yuranium, wanda kampanin AREVA na kasar Faransa ke haka a jamhuriyar Nijar yau fiye da shekaru 40. sanin kowa ne, a da kampanin Areva kadai ne ke hakar wannan karfe a doron kasar Nijar. To amma a cikin yan shekarun nan shuwagabanin kasar Nijar sun bude kasuwar samun kwangilar hakar Yuranium ga kowa, wato kowace kasa ta duniya na iya ta zo a yi yarjejeniya da ita saboda ita ma ta nemi wani abu daga cikin arzikin ma'adannan kasar da Allah ya albarkanci Nijar da su. A cikin kasashen da suka samu wannan kwatara ta hakar Yuranium, akwai kasar Cana wadda ta samu har da ta tonon man petur. Sanin kowane lokacin da wannan yarjejeniya ta shiga tsakanin kasar Nijar da Cana kampanin Areva bai ji dadi ba. Wato banda wurare biyu da kampanin Areva yake da shi, wato na SOMAIR da COMINAK, Areva ta so ta samu wani lasisin buda wani sabon kampanin hakar Yuranium, wannan kuma shi ne na IMURAREN. Shi ma da kyar da walahau la suka same shi, saboda kasar Nijar ta nemi a kara kudin Yuranium. Bayan ja-in-ja tsakanin kasar Nijar da Areva aka samu yarjejeniya wadda ta ba su damar tonon rijiyar ta IMURAREN. A yau ita ma kasar Cana tana nan, ke nan Areva ta samu kishiya, wato ana iya a ce Cana ta shigo gonar Areva. Shigowar Cana da wasu kasashe cikin gonar ta Areva ya ba yan kasar Nijar damar cewa, tun da masoyan Nijar masu yawa ne, irin su Kanada da Indiya da Ostaraliya da dai sauransu, ko ina mana da masoya, wato masu bukatar su ma su shigo su hako wannan karfe na Yuranium da wasu ma'adannan kasa, ke nan wata dama ce gare mu da za mu sayar da kayanmu ga wanda muke so kuma da daraja. Wannan bai yi ma Areva dadi ba. To ita ma karsar Cana ta yi yarjejeniya da kasar Nijar.

A yarjejeniyar da ta shiga tsakanin Cana da Faransa, ita Areva ta bada shawarar kasashen biyu su hada gwiwa. Su hada gwiwa tsakaninsu su biyu, don saboda harakar nukileya gabadaya. Wato tun daga hako karfen Yuranium har zuwa sarrafa shi zuwa ga wani makamashi ko wani makami mai lizzami, duk dai abin da ake iya yi da Yuranium. Takamaimai dai shi ne suna son su yi aikin tare da Cana. Tuni dai a cikin yarjejeniyar sun yi dahir da cewa, kampanin Areva za ya ba kasar Cana ton dubu 20 na karfen Yuranium kowace shekara, har tsawon shekaru 10 a nan gaba. Banda wannan kuma, za su kafa wani kafani na sarafa nukileya tsakaninsu. Haka kuma suka yarda a kan za su aikin tare da kasar Cana a kamfanin hakar karfen Yuranium na Imuraren, wato kasar Cana zata daukar wani hannun jari a cikin kamfanin na Imuraren. Idan suka cimma haka, ke nan kasar Cana da Faransa bakinsu daya, babu gasa tsakaninsu. Idan kuma tabbat ta kasance haka, kasar Nijar ba zata ji dadi ba. Saboda idan babu gasa tsakaninsu, wato idan ba su kasance kishiyoyin juna ba, to abin ba ya gyra kasar Nijar. Amma in akwai gasa tsakaninsu, to a duk lokacin da kasar Nijar ta gano da ba ta jin dadi aiki da wani daga cikinsu, sai ta je wajen wacan ta ce masa kai me ka ce? Wato abin kamar ka je kasuwa ne, idan ya kasance dan kasuwa daya ne ke sayar da wani abu, to yadda ya gadama zai sayar. To amma idan yana da abokan gasa, to sai ka kewaya wajen wanda za ku jituwa. Yau Nijar, ita ce ke da karfen Yuranium na saidawa, ke nan in akwai masu bukata da dama, irinsu Cana da Indiya da Ostaraliya da Faransa da Kanada da dai sauransu, sai ta tsayar da kudin karfen Yuranium yadda ta gadama, mai bukata ya saya, wanda kuma bay a iyawa sai ya bar wuri. Hakan kuma zai sa kasashen su yi kokowa domin kowa ya samu shiga. Amma in har ya zamanto bakinsu daya, to kamar mutum daya ne ke gaban kasar Nijar, bata iya buga teburi ta ce ga yadda take so a yi. Wannan yarjejeniya da ta shiga tsakanin Cana da Faransa ta nuna cewa, ba wai masu gasar juna ba ne. Lokacin da shugaban kasar Nijar ya nemi a kara darajar farashen karfen Yuranium, da bay a kasance akwai wasu kampanonin kasashen duniya dake bukatar ba, wadanda suka bayyana, da Areva da kasar Faransa ba za su yarda a kara wani abu ba ga yadda ake a da. To amma da yake akwai su, Areva da Faransa sun yarda, saboda sanin cewa, kasar Nijar na iya ce masu, ba su kadai ke bukatar ba, za a bada kwangilar ga wasu mabukata. Yanzu kuma sun kewaye kasar Nijar, sun je, sun hada baki da kasar da take takama da ita, wato Cana, ke nan yanzu tamkar kasa daya ce ke hakar karfen na Yuranium. A cikin yarjejeniyar da suka yi, akwai wadda ta hada kampanin nukileya na kasar Faransa da Cana, haka kuma akwai ta wani kampanin hakar man petur na kasar Faransa da na Cana. A nan ma kasar Nijar na iya fargaban cewa, watakila, a nan gaba suna iya suyi wani hadin gwiwa a kan hako man petur ma. Sanin kowane, kasar Cana ce ta samu lasisin hakar man petur din kasar Nijar, har ma da na matatar man petur din. Ke nan suna iya cewa, yadda muka bude maku shiga hakar Yuranium ta Imuraren, kuma ku bude mana hakar man petur. Ta nan suna iya samun gamin baki. Wannan kuma ya kamata ya ja hankalin yan kasa, saboda kasar Nijar ce ke da Yuranium da man petur dinta, amma wasu kasashen ketare can ke wani hadin gwiwa a kan hakarsu. Rishin tsoma kasar Nijar cikin wannan yarjejeniya, Wato kafata ba tare da shawartar Nijar ba, nada alaka da yadda muka yi yarjejeniya da kasashen masu hakar ma'adannan kasa. Da ya kasance a cikin yarjejeniyar mun ce, kamar kowane kampani zai alaka ko kafa wata yarjejeniya da wata kasa, sai an yi shawara da kasar Nijar za a yi haka, wato ya shafeta, to da a nan kasar Nijar zata iya fitowa ta ce ma kasar Faransa, kampanin SOMAIR da COMINAK da na IMURAREN da muka ba ku, ba don ku hada da wasu ba ne. Da kasar Nijar ta ce sai a yi shawara da ita da haka ne. A lokcin da ake zazzafar rigima a kan farashen Yuranium, akwai wani kampani na kasar Kanada, wanda shi ma ya samu lasisin izinin hakar Yuranium din. Shi ma wannan lasisi, Areva ce ta kewaya ta saye shi daga hannun kasar ta Kanada. Wato lasisin da kasar Nijar ta hana mata, ta bayar da shi ga kasar Kanada ya zama nata. Hada baki tsakanin Cana da Faransa, daga baya suna iya saye duk wani lasisi da aka ba wata kasa ko wani kampani, wato komai ya zama a hannunsu. Wato ya zama aikin mutum daya. Ba kuma abin mamaki ba ne Areva ta saye duk wani lasisi na kasar Cana. Ana iya zaton watakila abin ba zai yiyuwa ba, amma kuma ba za a fitar da tsammani ba. Bayan haka, wannan hadin kai tsakanin Faransa da Cana yakan iya taba farshen da aka tsayar tsakanin kasar Nijar da wadanda ta ba lasisin hakar ma'adannan kasar. Saboda da ma ba da son Areva aka basu lasisin ba, ya zama cilas ne. In ma ba su sauke farashen ba, suna iya hana ma kasar Nijar fitowa da wata hujjar nuna wata bukatar kara farashen. Dalili kuwa shi ne, sun yi baki daya, to ga wa Nijar zata dogara ta ce masa, shi tana son ya gyara zamansa da ita. Wannan kuma tabbat wani cikas ne. Bisanin wannan hadin gwiwa suna iya cewa, a je a yi magana da kasar Nijar ta rage farashe.

Abin lura a nan shi ne me? Kasar Faransa tana jan kokari ne don ta rike matsayinta da darajarta a yankin Sahel gabadaya, musamman ma a kasar Nijar. Wato ta rike makaminta na sahun gaba kuma ita ce kasar da ake aiki da ita. Yanzu ma idan aka dubi harakar ga ta Alka'ida wadda ke gudana a cikin arewacin kasar Nijar, kasar Faransa ta zo da sojojinta a cikin kasar Nijar, wannan kuma wani abu ne da ba a taba gani ba. A da sun zauna da wani karamin sansanin soje a kasar Nijar, amma yau da shekaru da dama da suka bar wuri. Yanzu, kuma watakila suna da niyar kafa ta su barikin soje a kasa. Wato kamar yadda suka yi a kasar Cote D'Ivoir da sauran kasashen Afrika. Sun nemi su kai sojojinsu a kasar Mali amma abin ya ci tur, amma sun je su yi wata yarjejeniya da kasar Moritaniya, wadda zata kawo sojojinta a kasar Mali, don su yi kokowa da alka'ida. Amma kuma ai manazarta da dama sun gano da cewa, bayan kasar Moritaniya, Faransa ce ke labe tana jagorancin dukan abubuwa. Su kuma kawo wasu yan sojoji a kasar Burkina Faso.

A shekarun baya Amirka ce ta kawo wani shiri na yaki da ta'addanci, ta kawo sojojinta da manema labarai da dai sauransu dake aiki da jami'an tsaron kasa. Wani tsari ne da suka so daukar duk yankin na Sahel ta hanyar wani furoje mai sunan PAN SAHEL INITIATIVE. Amirkawa ne ke wannan aiki tare da sojojin kasar Nijar da na Mali da dai sauransu. Yanzu ita ko Faransa na son ta shigo wannan aiki, saboda tana ganin kamar Amirka ta shigo gonarta ne. wato yanzu Faransa ta dawo da karfi tana son ta kula da duk wannan yanki na kasashen da ta mallaka. Dalili kuwa shi ne arzikin ma'adannan kasa da yankin ya kunsa, ke nan ba za su yarda ba wadansu su dauka ko su tona. Dole ita Faransa ta kare matsayinta na wadda ta mallakin kasashen a da. Wannan kuma wani sabon salo ne na mulkin mallaka suke kokarin asassawa. Abin da ya yi masu sauran yanzu shi ne, su samu damar kafa sansanin sojojinsu, watakila ma su shiga cikin harakokin zaben shuwagabaninmu. Saboda hakan zai ba su damar samu wani Karen farautarsu, dan amsar Shatansu, wanda zai kare duk wani alfanu nasu a cikin yankin. A taikaice dai wannan yarjejeniya ta shafi kasar Nijar gadan-gadan, amma da yake ba mu da bakin Magana, ana iya a zalumce mu ta wannan hanya.

"Sai an yi Usula, saboda al'umma ta bukaci in tsaya" http://www.alternativeniger.org/spip.php?article416 http://www.alternativeniger.org/spip.php?article416 2009-05-27T13:01:45Z text/html ha Labarun Nijar Wannan shi ne furucin da shugaban kasa Tanja Mahamadu ya yi a cikin wata fira da ta hada shi da jaridar “Liberation” da kuma talabizon na Faransa 24 na kasar Faransa. Shugaban kasa Tanja Mahamadu ya yi wannan furuci ranar 04 ga watan Afrilu shekarar 2009, albarkacin bukukuwan aza dan faragen farko na ginin kampanin AREVA, kampanin da za ya hakar karfen Uranium na dabagar Imuraren. A yanzu dai ta tabbata Shugaban kasar Nijar Tanja Mahamadu na bukatar Zarcewa ko yana bukatar a (...) - Labarun Nijar

Wannan shi ne furucin da shugaban kasa Tanja Mahamadu ya yi a cikin wata fira da ta hada shi da jaridar “Liberation” da kuma talabizon na Faransa 24 na kasar Faransa. Shugaban kasa Tanja Mahamadu ya yi wannan furuci ranar 04 ga watan Afrilu shekarar 2009, albarkacin bukukuwan aza dan faragen farko na ginin kampanin AREVA, kampanin da za ya hakar karfen Uranium na dabagar Imuraren. A yanzu dai ta tabbata Shugaban kasar Nijar Tanja Mahamadu na bukatar Zarcewa ko yana bukatar a kara masa shekaru uku, kamar yadda wasu yan kasa masoyan tazarce, suka bukata a cikin wata makala tasu da suka mika ga majalisar dokokin kasa ranar 22 ga watan Disamba na shekarar 2008.

"kundin mulkin kasa ya farlanta Usula, gashi kuma al'umma ta bukaci in tsaya, ba za ni kuma sabawa bukatar yan kasa ba".

Haka shugaban kasar ya jadaddawa kafofin labaran biyu na kasar Faransa. Yau dai fiye da watani hudu kenan da wasu yan kasa suka fara tarurukan assassa tazarcen shugaba a cikin kasa, a yayinda kuma a nasu bangaren kungiyoyin fararen hullar kasa suka jajirce kuma suka tsaya a kan bakansu na yan gwagwarmayar tabbatar da adalci tare da nuna cilas a kiyayye kundin tsarin mulkin kasa da shifida demokaradiyya a cikin kasa. A bangaren jam'iyun siyasar kasa, wadanda ake dubi su fitar da sanarwoyin kalubale a kan wannan burin tazarcen shugaban kasa Tanja Mahamadu, musamman jam'iyun adawa sunyi dogon barci, sai a lokacin da abin ya yi tsami, lokacin nan ne jam'iyar PNDS Tarayya ta fitar da wata sanarwa, tare da gabatar da wani taron gangami a unguwar Lazare birnin Yamai, inda ta kalubalanci masoyan tazarcen da tabbatar da cewa, aikata tazarce a cikin kasa, wani juyin mulki ne. Gaskiya ne kundin tsarin mulkin kasa bai haramta shiga usual ba, to amma yana da kyau ayi usular kamar yadda dokokin kasa suka gindaya, wato maganar ta shiga dakin Majalisar dokokin kasa, yan Majalisar su tattauna kana su jefa kuri'ar amincewa da gabatar da usular. Idan aka samu kashi uku cikin huda (3/4) na yan Majalisar dokokin, to a lokacin nan ne yan kasa zasu jefa kuri'ar iya ko a-a.

Babbar matsalar kuma abin fargaba a cikin zukatan yan kasa shi ne, ya ya wakilansu, wato yan Majalisar dokokin kasa zasu karbar wannan maganar shiga zaben usula a Majalisar dokokin kasa? Shin zasu aiki da abin da talakawan kasa ke so ko ko zasu aiki da abin da su yan siyasa suke bukata? Duk dan kasa mai kishin demokaradiyya da kundin tsarin mulkin kasa ba zaya rumtse ido ya rufe kunnuwansa ba yana ji yana gani a kariyar dokokin mulkin kasa don alfanun wasu yan tsirarru. Shugaban kasa Tanja Mahamadu, ya bayyana cewa “al'ummar kasa ta bukaci ya tsaya”, wacce al'umma ce wannan? Ita kuma wadda ta fito ta nuna a kiyaye kundin mulkin kasa me a sunanta? A yau abin bayyane yake karara cewa, yan gwagwarmayar tazarcen, ba ruwansu da wani kundin mulkin kasa, abin da ya dauki hankalinsu, shi ne sahihancin ci gaban mulkin shugaban kasa Tanja Mahamadu ko da kuwa abin ya keta dokokin mulkin kasa ne, ba ruwansu. Ya kamata duk inda dan Nijar yake zaune ya dauki gaban gabarar wannan magana ta tazarce, a matsayin hanyar keta kundin mulkin kasa da gurbata tafarkin mulkin demokaradiyya. Yan kasa su nuwa duniya abin da a ke ciki kowa ya sani. A mayar da wannan batu abin tattaunawa duk fadin kasar da duk inda dan Nijar yake zaune. Wannan zai ja hankalin masu fada a ji na yammacin turai su tsoma baki a cikin harkar. Hakan zai sa abubuwa su daidaita. Amma dai bai kamata a zuba ido ba tare da tunanin cewa, in ba shugaban kasa Tanja Mahamadu ba, ba wani dan Nijar da za ya ci gaba da aiwatar da kuma fitar da hanyoyin gina kasa ba. A yau Nijar ta na cikin kasashen duniya da ake alfahari da su wajen kiyaye kundin mulkin kasa, don haka bai kamata yan kasa su bi son zuciya ba, su bar wannan abu ya afku.

Sharhin Jaridun Mako http://www.alternativeniger.org/spip.php?article398 http://www.alternativeniger.org/spip.php?article398 2008-07-08T15:56:52Z text/html ha Labarun Nijar A wannan mako rinjayen jaridun kasar Nijar masu fitowar mako-mako sun mayar da akalar labaransu ne a kan tsarewar tsohon faraminista kuma shugaban jam'iyar MNSD Nassara Hama Amadu a gidan kason Kutukale, bayanda yan majalisar dokokin kasa suka jefa kuri'ar amincewa da a gurfanar da tsohon faraministan a gaban kotu. Sai kuma labarin k'ik'i-k'ak'ar neman shugabanci jam'iyar MNSD Nassara bayan Hama Amadu.
A fitowarta ta makon jaridar La Griffe ta (...) - Labarun Nijar
A wannan mako rinjayen jaridun kasar Nijar masu fitowar mako-mako sun mayar da akalar labaransu ne a kan tsarewar tsohon faraminista kuma shugaban jam'iyar MNSD Nassara Hama Amadu a gidan kason Kutukale, bayanda yan majalisar dokokin kasa suka jefa kuri'ar amincewa da a gurfanar da tsohon faraministan a gaban kotu. Sai kuma labarin k'ik'i-k'ak'ar neman shugabanci jam'iyar MNSD Nassara bayan Hama Amadu.
Akwai alamun kamuwa daga curutukan hikimar kimiyya dake boye ga al'ummar birnin Arlit http://www.alternativeniger.org/spip.php?article170 http://www.alternativeniger.org/spip.php?article170 2006-05-08T18:40:00Z text/html ha Hassane Boukar Labarun Nijar - Labarun Nijar
Abba Hassan
Matsalar kananan yan kasuwa http://www.alternativeniger.org/spip.php?article169 http://www.alternativeniger.org/spip.php?article169 2006-05-08T18:35:00Z text/html ha Labarun Nijar Lokacin da dubun dubatar yan kasa suka fito a kan titunan birnin Yamai, tsawon wasu makonni, domin su nuna rishin amincewar su ga tsadar rayuwa da suka tsinci kansu a ciki. A yayin da mahukuntan Nijar sun kai kunnuwan uwar shegiya ga matsalar tsadar cimaka, su kuma manya yan kasuwa sun tankware kanana.
A karshe wasu daga cikin makarabban kungiyoyin fararen fula suka rumtse idon, sunka sa hannu tare da gwamnatin a kan wata yarjejeniyar banza, a yayin da kuma fiye da million 7 na al'ummar (...) - Labarun Nijar
Lokacin da dubun dubatar yan kasa suka fito a kan titunan birnin Yamai, tsawon wasu makonni, domin su nuna rishin amincewar su ga tsadar rayuwa da suka tsinci kansu a ciki. A yayin da mahukuntan Nijar sun kai kunnuwan uwar shegiya ga matsalar tsadar cimaka, su kuma manya yan kasuwa sun tankware kanana.

Saidu Jibril
Gwamnatin Nijar ta ba wasu talakawan kasa wa'adin mako 2 su cire dakunan su daga inda suke zaune http://www.alternativeniger.org/spip.php?article168 http://www.alternativeniger.org/spip.php?article168 2006-05-08T18:30:00Z text/html ha Labarun Nijar - Labarun Nijar
Suleiman Maazu
Matsalar karamcin abinci, wani asirin Kasa http://www.alternativeniger.org/spip.php?article165 http://www.alternativeniger.org/spip.php?article165 2006-05-04T09:31:20Z text/html ha Labarun Nijar Hukumomin kasar Nijar sun yanke shawarar haramtawa duk wata kafar yada labarai ta waje dake da niyyar gudanar da rahoto a kan zance karamcin abinci shigowa cikin kasar. Tuni ma tashar gidan talabijin ta BBC ta hadu da fushin hukumomin akan wannan zancen, domin kuwa an tuso keyar Olma Gerin na BBC da kuma wadansu abokannin aikinsa zuwa Niamey, bayan da suka watsa rahotonsu na farko a kan yara kanana masu fama da tamowa, rahoton da suka dauka a cikin wata cibiyar kula da yara masu fama da (...) - Labarun Nijar Zancen samarwa matasa da ayyukan yi http://www.alternativeniger.org/spip.php?article163 http://www.alternativeniger.org/spip.php?article163 2006-05-04T09:28:46Z text/html ha Mamane Sani Adamou Labarun Nijar A lokacin taron koli na kungiyar tarayyar Afrika game da zancen samarar da ayyukan yi wanda ya gudana cikin watan satumbar 2004 a birnin Ouagadougou na kasar Burkina Faso, shuwagabannin na Afrika sun gano cewa tsarin siyasar da ake amfani da shi yau shekaru da dama kamar dai yadda kungiyoyin bayar da lamuna da kuma sauran kasashe masu karfin tattalin arziki na duniya suka shata, ya manta da zancen samarda ayyuka yi ga jama'a. Har ila yau game da irin illar dake tattare da wannan matsala ta (...) - Labarun Nijar
A lokacin taron koli na kungiyar tarayyar Afrika game da zancen samarar da ayyukan yi wanda ya gudana cikin watan satumbar 2004 a birnin Ouagadougou na kasar Burkina Faso, shuwagabannin na Afrika sun gano cewa tsarin siyasar da ake amfani da shi yau shekaru da dama kamar dai yadda kungiyoyin bayar da lamuna da kuma sauran kasashe masu karfin tattalin arziki na duniya suka shata, ya manta da zancen samarda ayyuka yi ga jama'a. Har ila yau game da irin illar dake tattare da wannan matsala ta rashin kyaukyawar siyasar samarda aikin yi ga al'umma da kuma mahimmanci dake ga yin hakan, bai kamata a ce zancen bai damu dukkannin shuwagabannin Afrika ba. A cikin hali na tabarbarewar tattalen arziki da kuma koma-baya ta fannin kyautata jin dadin rayuwar dan Adam, zancen rashin aikin yi ba wanda yafi shafa face matasa. A kasar Nijar alal misali rashin aikin yi ga matasa ya kai intaha, abin dake shafar hatta ma zancen ci gaban dan Adam
Zanga-zangar ranar 15 ga watan maris na shekara ta 2005 http://www.alternativeniger.org/spip.php?article164 http://www.alternativeniger.org/spip.php?article164 2006-05-04T09:28:38Z text/html ha Labarun Nijar Babbar zanga-zangar ranar 15 ga watan maris na shekarata 2005 ta kasance mai cike da guri da kuma fata nagari ga dubban al'ummar wannan kasa, wadanda suka fito domin yin tir da wani tsari da gwamnati ta nemi aiwatarwa, wanda kuma yake da matukar illa ga tattalen arziki da haddasa tsadar rayuwa. Shekara daya bayan shirya zanga-zangar, kowa ne darasi aka koya?
A dai dai lokacin da kamfanonin samarda ruwan sha da na makamashin wutar lantarki da yan kasuwa suke ci gaba cin karensu babu babbaka (...) - Labarun Nijar
Babbar zanga-zangar ranar 15 ga watan maris na shekarata 2005 ta kasance mai cike da guri da kuma fata nagari ga dubban al'ummar wannan kasa, wadanda suka fito domin yin tir da wani tsari da gwamnati ta nemi aiwatarwa, wanda kuma yake da matukar illa ga tattalen arziki da haddasa tsadar rayuwa. Shekara daya bayan shirya zanga-zangar, kowa ne darasi aka koya?

A dai dai lokacin da kamfanonin samarda ruwan sha da na makamashin wutar lantarki da yan kasuwa suke ci gaba cin karensu babu babbaka ta hanyar tsadada hajojinsu, su kuwa masu karamin karfi sun tsinci kansu ne a cikin wani halin rayuwa na wahala, yayin da su kuma yan majalisar dokoki na kasar suka tsarawa kansu doka mai kyautata makomarsu, firaminista ma haka-zalika illa kawai talaka da zai ci gaba da dandana kudarsa. A game da haka za'a iya cewa an shimfida wadansu munanan halaye guda uku dake cutar da jama'a; na daya kuwa shi ne nunawa jama'a cewa dole a darajjanta duk wadansu abubuwa da gmwamnatin kasar ta bullo da su, na biyu shi ne kowa ya kauda kaigame da irin siyasar da ake amfani da ita a kasar ko da kuwa tana cutarwa, na uku shi ne a yaki wannan doka mai neman kara tsunduma talaka cikin mawuyacin hali, abin da kuma shi ne al'umma ta zaba har ma ta shirya zanga-zangar ta ranar 15 ga watan na maris 2005.

Wani fata da bai kai ga samun galaba ba

Kamar dai mutum daya, haka al'umma ta fito a wannan rana domin yin watsi da wannan doka. Wannan kokowar ta ci nasara ne ba wai domin wadanda suka shirya ta sun kasance wasu gwarzaye ba, a'a domin kawai jama'a ta fito ne da guri da kuma manufa daya : Na daya kuma akwai zancen kasawar gwamnatin wa'adin farko na shugaba Tanja, wadda ta kasa cikawa yan kasa irin alkawullan da ta dauka masu lokacin yakin neman zabe. Na biyu kuma akwai zancen kin darajjanta dokokin kasa ta fannin bayar da kasuwa a cikin ma'aikatun gwamnati ba akan ka'ida ba ; wani abun kuwa da ya sa gwagwarmayar ta kai ga samun galaba ya hada har da fahimtar da manyan kungiyoyin kwadago na kasar suka yi kan cewa lokaci ya yi da za'a yi yaki da wannan doka ta kasafin kudin kasa na shekarar 2005 Dubban mutane sun karba kiran da aka yi masu a cikin titunan birnin Niamey domin nuna rashin amincewarsu kan wannan doka ta gwamnati.
Yau shekara daya bayan shirya zanga-zangar ko ana iya cewa tsadar rayuwa ta ragu a kasar nan ? A zahirin gaskiya amsar ita ce a'a, domin kuwa kowa ya tabbatar da cewa kayan masarufi frashinsu ya hau zuwa sama ne kawai. Amma watakila abin da ya fi daurewa jama'a kai anan shi ne ; yadda ake ganin cewa tamkar dai wasu daga cikin wadanda suka shiga gaba domin shirya zanga-zangar ta bara suna da alamar gazawa ko kuma sam sun shige cikin gungun wadanda ke tsara dokokin masu cutawa jama'a.

Sabin dabi'u da suka biyo bayan wannan zanga-zangar

A zahiri take cewa wasu daga cikin shuwagabannin da suka shirya bijirewa dokar a shekarar bara, a yau an wayi gari tare da ganin su cikin sha'anin tafiyarda mulkin kasar, tamkar dai manufofin wannan kokowar su ne samarmasu da wata malaba a cikin madafan iko. Har ila yau ana iya cewa wannan kokowar ta haifar da wasu sabbin jagora da suke da ra'yi irin na tsohon soja wanda a koda yaushe ake yaki yake daukar sojojin dake yakin a matsayin wadanda ba su da wata gwaninta ko bajinta a fagen fama tamkar irin wadda yake da ita lokacin da yake sanye da kaki. Wata hujjar fadin wannan magana kuwa shi ne yadda wasu daga cikin irin wadannan mutane suke shiga kafofin watsa labarai suna yin irin na magori wanda hausawa ke cewa wasa kanka da kanka, suna masu nuni da cewa duk wata gwagwarmaya da za'a yi matukar dai ba su ne suka tsara ta ba, to lalle ba za ta samu nasara ba.
Wannan dabi'a da suka runguma ta mayar da su tamkar su ne kawai shuwagabannin na kungiyoyin farar hula a wannan kasa, kuma duk wanda ya yi magana da sunan kungiyoyin farar hula idan har ba su ba ne to lalle kuwa ya kaucewa ka'ida.
Wannan dai wata shaida ce kan yadda suke neman kare martabarsu a idanuwan al'ummar kasar da suka yaudara, sakamakon yadda suka karkata manufofin wannan zanga-zanga a dai dai lokacin da take gaf da smun nasara, kana a yanzu sun zama neman kare manufofin gwamnatin ne ta hanyar yiwa duk wata gwagwarmaya da za'a shirya nan gaba zagon kasa.
Karkashin wata yarjejeniyar sulhu da wannan reshe na kungiyoyin farar hula na kasar dake kumshe da makwadaita ya sanyawa hannu domin dakatar da kokowar, an ga sabbin ma'aikata da suka kutsa kai domin kaddamar da wani gagarumin aiki na karbo harajin kasa da karfi tamkar dai su ne cikakkin ma'aikatan hukumar karbar haraji ta kasa. Ba shi kenan ba domin an samu wasu daga cikinsu sun kasance a cikin kwamitoci daban daban har ma da na rabon taimako abinci a lokacin yunwa.

Rigangantu zuwa kwasar garabasa

Watakila cikin rashin sani ko kuma rudanin da kalaman gwamnatin kasar suka haddasa masu, wadannan shuwagabanni na kungiyoyin farar hula sun rugumi tsari na a tafiyar da sha'anin gwamnati tare da su ba tare da sun yi la'akari da abin da zai biyo baya ba.
A ce yau shugaban gwamnati ya kebewa kansa wani romo amma irin wadannan mutanen ba ruwansu, a ci gaba gudanarda mummunan jagoranci a kasa ba su damu da hakan ba, su abin da ya dame su kawai, shi ne a tafiyar da kasa tare da su ba kumya ba tsoron Allah, domin kuwa su abin diniya kawai ya rufe masu ido.
Dangane da haka kirkiro wani kwamiti ko hukuma da za su shigewa, ko shirya taron karawa juna sani kadai ya damesu . To amma duk da haka ba za'a hadu a zama daya ba, domin kuwa cikakkun kungiyoyin farar hula irin wadanda suke yi domin ci gaban kasa kamar CDSCN, sun dukufa sosai ta fannin gwagwarmayar kwato hakkin jama'ar kasar, wanda dama yake wani gimshiki ne a shigarsu cikin waccan kokowar ta ranar 15 ga watan maris na shekarar 2005. Abinka da tarihi a kwana a tashi ranar 15 ga watan maris na wannan shekara 2006 ta zagayo, wato cikon shekara daya cur kenan, CDSCN da wadansu kungiyoyi da suka hada har da na malaman makaranta suka kira jama'ar kasar da su fito a shirya zanga zanga domin neman gwamnati ta kyautata tsarin bayar da ilimi a kasar, to amma me zai faru, sai aka ji wadancan kungiyoyi na makwadaita tsintsa sun shiga cikin kafofin watsa labarai suna yin kira ga jama'a da kada su fito wannan zanga-zangar.
A yau ba wai kawai kungiyar USTN ba da ta saba kauda kai game da shiga zanga zanga da ake tsarawa a Nijar, hatta ma sauran kungiyoyi guda biyu sun bi sahunta. To amma duk da haka sauran kungiyoyin malamai kamar su SNEN da kuma SNECS da na sauran ma'aikatan jami'a sun bayar da goyon bayansu ga wannan kokowar da ake yi. Su kuwa matasa, dalibai maza da mata sun nuna kishin kasa ta hanyar shiga wannan gwagwarmaya mai yin tir da Allah wadai da irin salon siyasar da ake amfani da shi a wannan kasa mai cutawa talaka. Sauran shuwagabannin kungiyoyi masu zaman kansu, da manyan kungiyoyin ma'aikatan kwadago sun kauda kai game da kokowar, irin wadannan yan amshin Shatar gwamnati, yan tumka da warwara, a yau kowa ya tabbatar ba su da wani ra'ayi na yin gwagwarmayar kare yancin dan Adam. Kenan me suke yi illa kawai wargaza duk wani tsari da zai kawowa talaka amfani a rayuwa da kuma ci gaba da yakar sauran takwarorinsu na kungiyoyin farar hular da suke da ra'ayin kyautata rayuwar al'umma. Irin wadannan mutane yau sun zama masu cutawa jama'a a cikin rigar kungiyoyin kare yancin dan Adam, alhali kuwa ba wannan aiki su ke yi ba a zahirin gaskiya sai dai kawai ci da gumin talaka. Kowa ya shaida cewa zanga-zangar da aka shirya ranar 15 ga watan maris na wannan shekara(2006) duk da yake mutane kalilanne suka fito, to amma ana iya cewa an samu galaba musamman idan aka yi la'akari da cewa akwai dubban dalibai da masana sha'anin ilimi da dai sauran jama'ar da suka fito a wannan rana, kuma abu ne mai wuya wani mutum ya iya takawa kungiyoyin da suka shirya zanga-zangar birki akan manufofinsu na kyautata sha'anin ilimi cikin wannan kasa ta Nijar.

Sule Aji
Ma'anar sabon yunkurin shugaban kasar Nijar http://www.alternativeniger.org/spip.php?article161 http://www.alternativeniger.org/spip.php?article161 2006-04-29T10:05:04Z text/html ha Mamane Sani Adamou Siyasa Duk masu lura da al'amurran siyasa na yau da kullum sun yi la'akari da canje-canjen da aka samu a dangataka tsakanin shugaban jamhuriya da mataimakinsa paraminista Hama Amadu. Ganin yanda tsawon shekaru biyar shugaba Tandja ya damka wa paraminista akalar gudanar da harakokin mulki, abin mamaki ne yau a ce shugaban gwamnati ya jahilci manufofin abokinsa. Har ma yan kallo na daukan cewa ai ba da bata lokaci za a kori Hama daga matsayinsa. A cikin wannan takarda za mu bincikin gaskiyar wannan (...) - Siyasa
Duk masu lura da al'amurran siyasa na yau da kullum sun yi la'akari da canje-canjen da aka samu a dangataka tsakanin shugaban jamhuriya da mataimakinsa paraminista Hama Amadu. Ganin yanda tsawon shekaru biyar shugaba Tandja ya damka wa paraminista akalar gudanar da harakokin mulki, abin mamaki ne yau a ce shugaban gwamnati ya jahilci manufofin abokinsa. Har ma yan kallo na daukan cewa ai ba da bata lokaci za a kori Hama daga matsayinsa. A cikin wannan takarda za mu bincikin gaskiyar wannan hasashe kana mu dubi halin cimin kasa da sauran dalilai da suka cilasta shugaban kasa canza salon jagorancinsa.