Ranar 25 ga watan Afrilun kowace shekara rana ce da hukumar lafiya ta duniya ta kebe domin ta zama ranar yaki da cutar zazzabin cizon sabro a afrika. Ko a bana kamar dai sauran shekaru an gudanar da shagulgullan zagayowar wannan rana a sassa da dama na Afrika cikin su kuwa har da kasar Nijar. (...) >suite
Babbar yekuwa ta kawar da cututtukan fitsarin jini ko ciwon tsagiya da kuma tsutsar ciki a cikin jahohin Maradi da Tawa
jeudi 22 décembre 2005
A game da namjin kokarin da hukumomi a ma’aikatar kiwon lafiya ta kasarnan ke yi domin kawar da ciwon tsagiya ko fitsarin jini da kuma cutar tsusar ciki a Nijar, wannan yasa aka kirkiro da wani bangare a ma’aikatar ta kiwon lafiya mai yaki da irin wadannan cututtuka a wannan kasa Nijar. Wannan dangare dai an kirkiro shi ne a cikin watan Maris na shekara ta 2004, inda kuma yake cigaba da gudanar da ayyukan sa na warakar da jama’a a sassa da dama na kasarnan >suite
A kowace shekara, kimanin yara yan kasa da shekaru biyar a duniya dubu goma sha daya ne dake fama da cutar tamowa, ke samun kulawar wata kungiya mai zaman kanta a yankin Maradi. >suite