Alternative Espaces Citoyens Niger
Accueil du site > Hausa > Taron Al’Umma

Taron Al’Umma

Articles de cette rubrique


YAKI DA TSADAR RAYUWA : INA AKA KWANA ? (Sharhi)

mardi 18 avril 2006 par Mamane Sani Adamou
Ranar 15 ga watan Maris na 2005 ta kasance mai matukar mahimmanci cikin tarihin gwagwarmayar kungiyoyin farar fula na jamhuriyar Nijar. Hakika, tun zanga-zangar da ta biyo kisan gillar dalibai na jami’ar Yamai a shekarar 1990, ba a taba samun yunkurin al’umma da ya yi tasiri da (...) > suite


Al’ummar Yamai ku da wadataccen ruwan sha, watakila sai badi warhaka (Sharhi)

vendredi 23 décembre 2005
Ruwa su ne rayuwa ! Alhaji Baba Ba’abba, magatakardan gwamnatin jahar Yobe a tarrayar Najeriya, kuma tsohon magatakarda mai zartarwa na hukumar ABN da ke kulla da raya kogin Nijar, ya jadadda cewa, dan adam na iya rayuwa har tsawon kwana 40 ba tare da ya ci kallaci ba, amma ba zai iya rayuwa kwana 40 ba tare da ya sha ruwa ba, wannan magana nuna mana muhimmancin ruwa ga rayuwar dan adam a duniya. > suite


Rashin hadin kan kungiyoyin kwadago abin farin ciki ne ga gwamnati ! (Labarai)

vendredi 23 décembre 2005
Daya ga watan mayu 1886, 1 ga watan mayu 2005 shekaru 119 kenan cur da aka yi wa ma’aikatan kwadago dake zanga zangar neman hakkin su kisan gilla a birnin Chikago na kasar Amuruka. Kamar sauran ma’aikatan kwadago na kasashen duniya nan ma a kasar Nijar ma’aikatan sun gudanar shagulgullan tunawa da wanan bakar rana ta alhini da takaici. > suite


Kiran kungiyoyin farar

Kira, daga kungiyoyin kwadago, da masu zaman kansu, da na Mata da Matasa, tare da na mazauna karkar da su ka halarci babban zaman taron al’ummar Nijar (Taron Al’Umma)

vendredi 23 décembre 2005
Kamar sauran kasashen Afrika, kasar Nijar ta rungumi tsarin mulkin Democradiya tare da samar da jam’iyun siyasa barkatai ne, a 1991, a lokacin da ta gudanar da babban zaman taron kasa mai cikakken iko.Wannan cigaba da aka samu ya haifar da kafa jam’iyun siyasa da dama tare da shirya babbab zabe, da kuma samar da kundin tsarin mulki da ya tabbatar da yancin dan adam da na Democradiya, kana an samu kafuwar kungiyoyin fararen hula da dama, tare da sakin mara ga kafofin yada labarai.Duk kuwa wannan muhimmin cigaba da aka samu ta fuskar siyasa, ya faru ne sanadiyar sadaukar da kan da al’ummar Nijar maza da mata su ka yi ne, tare da kaucewa dak wani yanayi da zai sa a koma gidan jiya ,ma’ana inda aka fito. > suite


Tsadar Haya a birnin Yamai (Sharhi)

vendredi 23 décembre 2005
Tsadar hayar gidaje a birnin Yamai da kuma sauran manyan birane na kasar Nijar, ta zama daya daga cikin abubuwan da ke ci wa ma’aikatan bariki da sauran jama’a musamman masu dan karamin karfi tuwo a kwarya,inda a cikin yan shekarun baya-bayan nan matsalar ke cigaba da yin kamari. > suite


Malamai magoya bayan kungiyar SNEN a Damagaram, sun gudanar da azumi da adu’o’i domin neman sakayyar Ubangiji akan gwamnati (Labarai)

vendredi 23 décembre 2005
Bayan sun sha yin yajin aiki sau da dama kamar yadda uwar kungiyar su ta bukace su, domin ganin cewa gwamnati ta shafe masu hawaye, a halin yanzu malaman makaranta magoya bayan kungiyar SNEN a birnin Damagaram sun canza salon gwagwarmaya domin kwato hakkokin su da suka ce gwamnati tayi rib da ciki akan su yau shekaru da dama kenan. A ranar Alhamis da ta gabata, daruruwan malamai ne magoya bayan kungiyar ta SNEN suka fito akn titunan birnin na Damagaram inda suka yi wata zanga-zangar lumana, domin ko wata kila hukumomi za su saurare su a wannan karo har ma su shafe masu da hawayen na su. > suite


Ana wata ga wata, bayan karin kudin harajin TVA, shi ma kampanin SEEN yayi kari ga kudin ruwan sha (Labarai)

vendredi 23 décembre 2005
Kaungiyoyin kare hakkin dan Adam da kuma na ma’aikatan kwadago a kasar Nijar, sun kudiri aniyar cigaba da gwagwarmaya har sai lokacin da shugaban kasar Tanja Mamadu, ya soke dokar nan mai kara kudin haraji akan kayayakin abunci, ruwan sha da kuma makamashin lantarki . > suite


Bakin tika tika bakin tik !!! (Labarai)

vendredi 23 décembre 2005
Daga Karshe dai an cimma daidaito tsakanin gwamnati da kungiyar nan mai fafukar yaki da tsadar rayuwa a kasar Nijar. > suite


Shin wai Nijar ce tafi duk sauran kasashen duniya tsadar Man Petur ? (Sharhi)

vendredi 23 décembre 2005
A ranar Lahadi 1 ga watan mayu ne al’ummar Nijar suka wayi gari da karin farashin kudin man petur da ba a taba ganin irinsa ba a tarihin kasar, wanda yasa lita daya na man ya kai dala 106 sabanin dala 98 da yake tunda farko, al’amarin da ke nuna karin ya kai na dala 8. Wannan tashin gwabran zabo da farashin man ya yi, ya kara jefa al’umma cikin maywuyacin halin matsi da wahalar da suke fuskanta tunda farko. > suite


A garin bakin tone-tonen sa zakara ya tono wukar yankansa, domin kuwa dan Nijar ya zabo yan majalisar dokoki daidai da shi !!! (Labarai)

vendredi 23 décembre 2005
A daidai lokacin da al’ummar Nijar ke fama da kangin talauci, fatara, kai har ma da karamcin abinci sai gashi kwatsam sabuwar majalisar dakoki kasar ta amince da wadansu sababbin hanyoyin karbar haraji ga talakawa kota halin kaka wanda gwamnati ta gabatar mata. > suite


Accueil du site | Contact | Plan du site | Espace privé | Statistiques | visites : 107489

Suivre la vie du site ha  Suivre la vie du site Hausa  Suivre la vie du site Taron Al’Umma   ?

Site réalisé avec SPIP 1.9.2c + ALTERNATIVES

Creative Commons License