Alternative Espaces Citoyens Niger
Accueil du site > Hausa > Yancinku

Yancinku

Articles de cette rubrique


lHukumar kare yancin dan adam ta kasa CNDHLF ta nemi gwamnati da ta soke tare da kwace kaddarorin da kungiyar Timidria ta mallaka (Yancinku)

jeudi 22 décembre 2005
Shugaban kungiyar nan mai yaki bautar da jama’a a kasar Nijar mai suna Timidria Ilguelas Weila na ci gaba da kasancewa a gidan kurkukun birnin Yamai , bayan da jami’an tsaro suka yi awon gaba da shi tun ranar 28 ga watan Maris da ya gabata. Ilguelas Weila wanda aka cabke tare da wadansu manyan jami’ai na kungiyarsa , sun ci gaba da kasancewa a hannun jami’an tsaron ne har na tsawon mako daya, kafin daga bisani a saki wasu daga cikinsu kana aka ci gaba da tsare shugaban kungiyar na kasa baki daya da kuma mataimakin magatakarda na kungiyar mai kula da shiyar Tillaberi mai suna Alasan Biga. > suite


Al’amarin tsaro a mayan biranen jamhuriyar Nijar (Yancinku)

sai cigaba da tabarbarewa yake
jeudi 22 décembre 2005
Aya ta 11 da ke kumshe a cikin Kundin tsarin mulkin kasar Nijar, ta yi furuci a game da tsaron rayuwa, lafiya da kuma dukiyoyin yan kasa. > suite


Kisan Jinjirai a Nijar (Yancinku)

jeudi 22 décembre 2005
Kisa a wannan zamani wani abu ne mai sauki, da ya zama ruwan dare gama duniya. kisan gilla wata kalma ce da bahaushe ke anfani da ita domin bayyana cewa an fitar da rayuwar wani ko wata da gangan ba tare da aikata wani laifi ba, abin dake cigaba da faruwa a kowace safiya ta Allah a cikin (...) > suite


Ranar yancin aikin jarida ta duniya (Yancinku)

a kasar Nijar ma an gudanar da shagulgula daban daban domin murnar zagayowar wannan rana
jeudi 22 décembre 2005
Ranar 3 ga kowane watan Mayu na shekarar meladiyya ; ta kasance ranar yanci da walwala ga aikin jarida na duniya baki daya kamar yadda majalisar dinkin duniya ta yi ammana tun cikin shekara ta 1990 ;yau shekaru goma sha biyar(15) kenan da su ka gabata. Kamar ko wace shekara ; tun soma raya wannan rana ta yan jarida a bana ma gungun kungiyoyin yan jaridu na kasar Nijar tare da hadin gyuwar da tallafin ofishin jakadancin kasar Amurka na birnin yamai ;sun gudanar da dimbin shagulgulla albarkacin wannan rana. An fara bikin ne da wasar kwallon kafa a hilin kwallon kafa na janar Seini Kountche dake nan birnin yamai. Wasar kwallon ta hada kungiyar yan jarida da ta jami’an tsaro na yan sanda ; inda kuma jami’an tsaron suka yi nasara bisa kan yan jarida da ci daya da babu .Ita dai wannan wasa ta bada shawa kwarai da gaske. Kamar dai yadda ku ka sani yan jarida da jami’an tsaron sun kasance tamkar dan jumma ne da dan jummai ;abun da ma ya kara kayatar da wasar ta yi armashi irin na gaske. > suite


Sarkin Damagaram ya sanya wani dan jarida zaman kaso a gidan tururuwa (Yancinku)

Sarkin Damagaram (Zinder) ya sanya wani dan jarida zaman kaso a gidan tururuwa
jeudi 22 décembre 2005
A na maganin bakin abu dumya na hittowa. Gabe da lokacin da ministan maaikatar sadarwa ke cema gungun kungiyoyin yan jarida, tura keyar yan jarida a gidan wakafi ya kusa zama tarihi a kasar Nijar ko ma ya zama, albishir na cewa za a kadamar da kundin nan mai kumshe da ayoyin dokar da ke kare (...) > suite


Harshe da al’adu... (Yancinku)

HARSHE DA AL’ADU...
jeudi 22 décembre 2005
Ko wa ya bar gida, gida ya barshi. Shi ne yanayin da mu ka tsinci kan mu ciki a halin yanzu. A yau kasar Nijar na da shekaru 45 da samun yancin kai daga turawan mulkin mallakar kasar Faransa. Shekaru 45 ba kwana 45 ba ne,amma kusan gidan jiya noman Goje. kasar Nijar dai kasa ce mai kumshi da (...) > suite


Muhimmin Jawabin da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana game da Hakkokin Yan-adam a shekarar 1948 (Yancinku)

jeudi 22 décembre 2005
Gabatarwa Ganin cewa yanci da adalci da zaman lafiya ba za su girku a duniya ba, sai in an amince da cewa: dukkan yan-adam suna da mutunci, kuma suna da hakkoki na kowa daidai da na kowa, wadanda ba za a iya kwace musu ba, Ganin cewa ba abin da ya sa aka aikata abubuwa irin na lokacin (...) > suite


A garin Inates na jahar Tillaberi, an rufe kare da sanho (Yancinku)

jeudi 22 décembre 2005
Bauta wata kalma ce da bahaushe ke amfani da ita domin bayyana rayuwar wani mutun ko mutanen da suka kasance ba tare da sun mallaki ikon kansu ba. Tarihi ya nuna cewa bautarda jama’a abu ne wanda ya samu tushe tun shekaru aru-aru a cikin kasashen duniya da dama, wadanda suka hada har da kasar Nijar. > suite


Accueil du site | Contact | Plan du site | Espace privé | Statistiques | visites : 107652

Suivre la vie du site ha  Suivre la vie du site Hausa  Suivre la vie du site Yancinku   ?

Site réalisé avec SPIP 1.9.2c + ALTERNATIVES

Creative Commons License