Alternative Espaces Citoyens Niger

Zanga-zangar ranar 15 ga watan maris na shekara ta 2005

jeudi 4 mai 2006

Babbar zanga-zangar ranar 15 ga watan maris na shekarata 2005 ta kasance mai cike da guri da kuma fata nagari ga dubban al’ummar wannan kasa, wadanda suka fito domin yin tir da wani tsari da gwamnati ta nemi aiwatarwa, wanda kuma yake da matukar illa ga tattalen arziki da haddasa tsadar rayuwa. Shekara daya bayan shirya zanga-zangar, kowa ne darasi aka koya?

A dai dai lokacin da kamfanonin samarda ruwan sha da na makamashin wutar lantarki da yan kasuwa suke ci gaba cin karensu babu babbaka ta hanyar tsadada hajojinsu, su kuwa masu karamin karfi sun tsinci kansu ne a cikin wani halin rayuwa na wahala, yayin da su kuma yan majalisar dokoki na kasar suka tsarawa kansu doka mai kyautata makomarsu, firaminista ma haka-zalika illa kawai talaka da zai ci gaba da dandana kudarsa. A game da haka za’a iya cewa an shimfida wadansu munanan halaye guda uku dake cutar da jama’a; na daya kuwa shi ne nunawa jama’a cewa dole a darajjanta duk wadansu abubuwa da gmwamnatin kasar ta bullo da su, na biyu shi ne kowa ya kauda kaigame da irin siyasar da ake amfani da ita a kasar ko da kuwa tana cutarwa, na uku shi ne a yaki wannan doka mai neman kara tsunduma talaka cikin mawuyacin hali, abin da kuma shi ne al’umma ta zaba har ma ta shirya zanga-zangar ta ranar 15 ga watan na maris 2005.

Wani fata da bai kai ga samun galaba ba

Kamar dai mutum daya, haka al’umma ta fito a wannan rana domin yin watsi da wannan doka. Wannan kokowar ta ci nasara ne ba wai domin wadanda suka shirya ta sun kasance wasu gwarzaye ba, a’a domin kawai jama’a ta fito ne da guri da kuma manufa daya : Na daya kuma akwai zancen kasawar gwamnatin wa’adin farko na shugaba Tanja, wadda ta kasa cikawa yan kasa irin alkawullan da ta dauka masu lokacin yakin neman zabe. Na biyu kuma akwai zancen kin darajjanta dokokin kasa ta fannin bayar da kasuwa a cikin ma’aikatun gwamnati ba akan ka’ida ba ; wani abun kuwa da ya sa gwagwarmayar ta kai ga samun galaba ya hada har da fahimtar da manyan kungiyoyin kwadago na kasar suka yi kan cewa lokaci ya yi da za’a yi yaki da wannan doka ta kasafin kudin kasa na shekarar 2005 Dubban mutane sun karba kiran da aka yi masu a cikin titunan birnin Niamey domin nuna rashin amincewarsu kan wannan doka ta gwamnati.
Yau shekara daya bayan shirya zanga-zangar ko ana iya cewa tsadar rayuwa ta ragu a kasar nan ? A zahirin gaskiya amsar ita ce a’a, domin kuwa kowa ya tabbatar da cewa kayan masarufi frashinsu ya hau zuwa sama ne kawai. Amma watakila abin da ya fi daurewa jama’a kai anan shi ne ; yadda ake ganin cewa tamkar dai wasu daga cikin wadanda suka shiga gaba domin shirya zanga-zangar ta bara suna da alamar gazawa ko kuma sam sun shige cikin gungun wadanda ke tsara dokokin masu cutawa jama’a.

Sabin dabi’u da suka biyo bayan wannan zanga-zangar

A zahiri take cewa wasu daga cikin shuwagabannin da suka shirya bijirewa dokar a shekarar bara, a yau an wayi gari tare da ganin su cikin sha’anin tafiyarda mulkin kasar, tamkar dai manufofin wannan kokowar su ne samarmasu da wata malaba a cikin madafan iko. Har ila yau ana iya cewa wannan kokowar ta haifar da wasu sabbin jagora da suke da ra’yi irin na tsohon soja wanda a koda yaushe ake yaki yake daukar sojojin dake yakin a matsayin wadanda ba su da wata gwaninta ko bajinta a fagen fama tamkar irin wadda yake da ita lokacin da yake sanye da kaki. Wata hujjar fadin wannan magana kuwa shi ne yadda wasu daga cikin irin wadannan mutane suke shiga kafofin watsa labarai suna yin irin na magori wanda hausawa ke cewa wasa kanka da kanka, suna masu nuni da cewa duk wata gwagwarmaya da za’a yi matukar dai ba su ne suka tsara ta ba, to lalle ba za ta samu nasara ba.
Wannan dabi’a da suka runguma ta mayar da su tamkar su ne kawai shuwagabannin na kungiyoyin farar hula a wannan kasa, kuma duk wanda ya yi magana da sunan kungiyoyin farar hula idan har ba su ba ne to lalle kuwa ya kaucewa ka’ida.
Wannan dai wata shaida ce kan yadda suke neman kare martabarsu a idanuwan al’ummar kasar da suka yaudara, sakamakon yadda suka karkata manufofin wannan zanga-zanga a dai dai lokacin da take gaf da smun nasara, kana a yanzu sun zama neman kare manufofin gwamnatin ne ta hanyar yiwa duk wata gwagwarmaya da za’a shirya nan gaba zagon kasa.
Karkashin wata yarjejeniyar sulhu da wannan reshe na kungiyoyin farar hula na kasar dake kumshe da makwadaita ya sanyawa hannu domin dakatar da kokowar, an ga sabbin ma’aikata da suka kutsa kai domin kaddamar da wani gagarumin aiki na karbo harajin kasa da karfi tamkar dai su ne cikakkin ma’aikatan hukumar karbar haraji ta kasa. Ba shi kenan ba domin an samu wasu daga cikinsu sun kasance a cikin kwamitoci daban daban har ma da na rabon taimako abinci a lokacin yunwa.

Rigangantu zuwa kwasar garabasa

Watakila cikin rashin sani ko kuma rudanin da kalaman gwamnatin kasar suka haddasa masu, wadannan shuwagabanni na kungiyoyin farar hula sun rugumi tsari na a tafiyar da sha’anin gwamnati tare da su ba tare da sun yi la’akari da abin da zai biyo baya ba.
A ce yau shugaban gwamnati ya kebewa kansa wani romo amma irin wadannan mutanen ba ruwansu, a ci gaba gudanarda mummunan jagoranci a kasa ba su damu da hakan ba, su abin da ya dame su kawai, shi ne a tafiyar da kasa tare da su ba kumya ba tsoron Allah, domin kuwa su abin diniya kawai ya rufe masu ido.
Dangane da haka kirkiro wani kwamiti ko hukuma da za su shigewa, ko shirya taron karawa juna sani kadai ya damesu . To amma duk da haka ba za’a hadu a zama daya ba, domin kuwa cikakkun kungiyoyin farar hula irin wadanda suke yi domin ci gaban kasa kamar CDSCN, sun dukufa sosai ta fannin gwagwarmayar kwato hakkin jama’ar kasar, wanda dama yake wani gimshiki ne a shigarsu cikin waccan kokowar ta ranar 15 ga watan maris na shekarar 2005. Abinka da tarihi a kwana a tashi ranar 15 ga watan maris na wannan shekara 2006 ta zagayo, wato cikon shekara daya cur kenan, CDSCN da wadansu kungiyoyi da suka hada har da na malaman makaranta suka kira jama’ar kasar da su fito a shirya zanga zanga domin neman gwamnati ta kyautata tsarin bayar da ilimi a kasar, to amma me zai faru, sai aka ji wadancan kungiyoyi na makwadaita tsintsa sun shiga cikin kafofin watsa labarai suna yin kira ga jama’a da kada su fito wannan zanga-zangar.
A yau ba wai kawai kungiyar USTN ba da ta saba kauda kai game da shiga zanga zanga da ake tsarawa a Nijar, hatta ma sauran kungiyoyi guda biyu sun bi sahunta. To amma duk da haka sauran kungiyoyin malamai kamar su SNEN da kuma SNECS da na sauran ma’aikatan jami’a sun bayar da goyon bayansu ga wannan kokowar da ake yi. Su kuwa matasa, dalibai maza da mata sun nuna kishin kasa ta hanyar shiga wannan gwagwarmaya mai yin tir da Allah wadai da irin salon siyasar da ake amfani da shi a wannan kasa mai cutawa talaka. Sauran shuwagabannin kungiyoyi masu zaman kansu, da manyan kungiyoyin ma’aikatan kwadago sun kauda kai game da kokowar, irin wadannan yan amshin Shatar gwamnati, yan tumka da warwara, a yau kowa ya tabbatar ba su da wani ra’ayi na yin gwagwarmayar kare yancin dan Adam. Kenan me suke yi illa kawai wargaza duk wani tsari da zai kawowa talaka amfani a rayuwa da kuma ci gaba da yakar sauran takwarorinsu na kungiyoyin farar hular da suke da ra’ayin kyautata rayuwar al’umma. Irin wadannan mutane yau sun zama masu cutawa jama’a a cikin rigar kungiyoyin kare yancin dan Adam, alhali kuwa ba wannan aiki su ke yi ba a zahirin gaskiya sai dai kawai ci da gumin talaka. Kowa ya shaida cewa zanga-zangar da aka shirya ranar 15 ga watan maris na wannan shekara(2006) duk da yake mutane kalilanne suka fito, to amma ana iya cewa an samu galaba musamman idan aka yi la’akari da cewa akwai dubban dalibai da masana sha’anin ilimi da dai sauran jama’ar da suka fito a wannan rana, kuma abu ne mai wuya wani mutum ya iya takawa kungiyoyin da suka shirya zanga-zangar birki akan manufofinsu na kyautata sha’anin ilimi cikin wannan kasa ta Nijar.

Sule Aji

Accueil du site | Contact | Plan du site | Espace privé | Statistiques | visites : 108267

Suivre la vie du site ha  Suivre la vie du site Hausa  Suivre la vie du site Labarun Nijar   ?

Site réalisé avec SPIP 1.9.2c + ALTERNATIVES

Creative Commons License