Matsalar kananan yan kasuwa
lundi 8 mai 2006
Lokacin da dubun dubatar yan kasa suka fito a kan titunan birnin Yamai, tsawon wasu makonni, domin su nuna rishin amincewar su ga tsadar rayuwa da suka tsinci kansu a ciki.
A yayin da mahukuntan Nijar sun kai kunnuwan uwar shegiya ga matsalar tsadar cimaka, su kuma manya yan kasuwa sun tankware kanana.
A karshe wasu daga cikin makarabban kungiyoyin fararen fula suka rumtse idon, sunka sa hannu tare da gwamnatin a kan wata yarjejeniyar banza, a yayin da kuma fiye da million 7 na al’ummar kasar ke fama da talauci da fatara, su kuma a na su bangare yan kasuwa suna cikin zullumin rishin abukan cinikayya.
A lokacin nan ne muka tarda wani karamin dan kasuwa mai suna Insa a zaune, fuskar sa a turnike, yayi tagumi, ya na zullumi da tunanin, inda zaya fito da tsabar kudi jika dari 3 da tamanin (80) kirar CFA, da ya kamata ya zubawa Alhaji, nan zuwa sabkowar ruwan damana.
Insa, daya daga cikin yan kasuwar dake saye da sayarwa, a kasuwar Complexe, da aka fi sani da sunan kasuwar hatsi birnin Yamai, kuma yau fiye da wata biyar (5) kenan, da ya dauko bashin buhunan hatsi gurin Alhaji, to amma har sakunan sun fara yoyewa bai sayar ba.
A cewar shi Insa, « A da kasuwancin hatsin da muke yana tafiya kamar yadda ya kamata, to amma a yanzu, harakar ta canza zanne, masaya ba karfin sayen sakuna, ma’ana dai ba su da kudi ». Irin wadannan yan kasuwa, suna da dama a kasuwune daban daban, wadanda suka tsunduma cikin irin wannan hali.
Kasuwar hatsin dake kusan cibiyar yada al’adu da galgajiya ta kasa Umaru Ganda (CCOG), itace babbar kasuwar kasuwanci cimaka iri iri, kamar su hatsi, masara, dawa, wake da dai sauransu.
A cewar Alhaji Sumaila, daya daga cikin yan kasuwar dake sana’a a kasuwar hatsi, (idan kaga shagunan mu makil da cimaka, to wannan lokaci, mu, muna fargaba sosai da shi, ma’ana dai yana nuna muna cewa ba kasuwa). A na iya gane wannan lisafi a cikin sauki, ma’ana hawan farashen cimaka a kasuwar abu ne da ake ganewa, ta bangaren yawan masu zowa sayen cimakar, ga shi kuma a wannan lokaci da muke ciki ba masayan. Kana kuma za’a gano da rishi masayan a duk lokacin da aka gano da cewa, masu sayen tiya tiya ne suka yawaita a kasuwar. Alhaji Sumaila ya kara da cewa, yanzu kai, ta kare a gare mu, sai dai mu koma kauye da zama, tunda kasuwanci ya tsaya.
Kamar yadda hukumar kasa mai bada sanarwar farashen cimaka a kasuwunen kasar ta bayyana (SAP) za’a iya gano da cewa, akwai hawa hawan farashen cimaka a kasuwunen kasar, musamman a kan hatsi da dawa, wadanda kudin su, suka karu da kashi 4 cikin dari (4 %) a watan fabrairu .
Kamar dai yadda Yunusa ya shaida muna da cewa, yau farashen saku hatsi mai nauyin kilo dari, ya kai jika 15 a kasuwar hatsi birnin Yamai. Sanarwar SAP din ta bayyana cewa, farashen saku wake mai nauyin kilo dari ya kai jika 19 a kasuwa, farasjen ya karu da kashi 8 cikin dari (8%) tun a watan janairu.
Wannan hawa- hawan farashen sauran cimaka yake iya zayo karuwar farashen wasu daga cikin cimakokin da ake samu da rahusa. Hakan kuma yake zakulu fusantar masu amfani da ire iren wannan cimaka, kamar dai yadda, Afisa wata mata, mai tuyar kosai, take mamaki da kuma cewa, « Mu fa ba mugane komai ba a cikin wannan haraka, a bara anyi zangazangar yaki da tsadar rayuwa a kasa, saidai har yanzu komai bai canza ba, cimakar sai kara kudi take ».
A yanzu haka a kan dala dari da ashirin nake sayo tiyar wake daya, butar man kwalanshe a dala dari da sittin, bada wasu kayayyaki hadayya da nike amfani da su ba, dan in toya kosai ».
Hawa- hawan farashen a kan cimakokin da yan kasa suka fi yawan amfani da su da suka hada da hatsi, masara da shinkafa , ya zamanto bako ne ga yan kasa, farashen hatsin ya karu da kashi 4 cikin dari (4%) a yayin da kuma ita shinkafar da ake shigowa da ita, farashen na ta ya karu da kashi 6 cikin dari (6%).
Tsadar cimakar da wasu kayan masarufi, ya sa wasu daga cikin yan kasuwar sun talauce,kamar yadda mu ka samu malam Samuel Subu wani dan kasuwanci shinkafa da kayan masarufi, yayi tagumi, ba ma su saye. Ya kuma bayyana muna da cewa, tunda na kara farashe a kan kayayyaki na, kasuwanci ya tsaya, dalili kuwa shine mutane sun saba da arha.
Hawan TVA a kan sauran kayayyakin masarufi, shine ya kawo hawa-hawan farashen cimakar, wanda hakan ya sa , su kuma manyan yan kasuwa suke cin kajin su ba babbaka a doron kananan yan kasuwa.
Hakan kuma ya sa, yan kasuwar sunyi rishi masaya da dama, kamar yadda Samuel ya jadada muna da cewa, yau, ya rasha kashi 3 daga cikin kashi 4 mutanen dake sayen cimaka da kayayyakin masarufi a gurin sa.
Tun a wannan lokaci, kasuwancin sai ja da baya yake, da kuma ya gano ba ci gaba ga sayarda shinkafa da wasu kayayyakin masarufi sana’ar sa ta yau da kullum, Samuel ya sake sana’a. Yake sayarda kayayyakin marmari , dagin su (coca cola) , nonon campani da yake daukowa bashi a campanonin. To, saidai wannan kasuwanci, ba zai biya ma sa bukatun sa ba, kamar yadda ya saba.
Da ganin sa malam Abubakar wani mai shagon sayarda kayayyakin marmari, shi kai, ya na cikin sukuni fiye da Samuel, ya kuma nuna muna cewa, « A yanzu fa harakokin lafiya lau ne, tunda aka kara farashen kayayyakin masarufi, a da dai ina sayen saku sukari a jika 16, yanzu ko da farashe ya karu muna sayo saku a jika 20, dan haka, ni ma dole ne, ni kara farashen kilo sukari, yanzu kuma kari yakai kashi 70 cikin dari (70%), ba kamar shekarar bara ba.
To, amma duk da haka, mutane na zowa su saya, saidai kananan yan kasuwa, su kai suna kuka da mu.
A cewar wasu kanana yan kasuwa, harakar kasuwanci a jamhuriyar, akwai matsala, yanzu kai saidai suyi murabus,kamar yadda Samuel dan asalin Fada N’gurma cikin kasar Burkina Faso ya jadada muna.
Babbar matsalar, shine wasu daga cikin yan kasuwar, basu da ma kudin shiga motar dawayya a kauyuyukan su, kamar yadda wani daga cikin yan kasuwar ya bayyana muna.
A yanzu haka dai Samuel ya shiga neman aikin kowace ta samu, kofa kofa yana bidar aikin yi, ko boyi, ko tsaron gida, da dai sauransu.
A cewar shi Samuel din, dan shekaru talatin da haihuwa, dakyar da lahaula walakoti yake samu abinda suka kore yawun bakinsu a rana daya, sanin kowane, ciyar da gida a birnin Yamai , ba karamin aiki ba ne, gashi kuma, shi Samuel din bayada karfi , Ya kuma jadada muna da cewa yanzu haka shi da iyalin sa saida suka samu daidaito rage yawan cimakar da suke amfani da ita a rana daya, ya kuma gaskanta cewa, in mutun ba yada komai, to dole ne ya wahala, aiki baya samuwa a birnin ya.

Saidu Jibril
Accueil du site |
Contact |
Plan du site |
Espace privé |
Statistiques |
visites : 107636
Site réalisé avec SPIP 1.9.2c + ALTERNATIVES